UKUBAR KISHIYATA 1-END

UKUBAR KISHIYATA Page 11 to 20

Koda Al’ameen ya dawo suka kama hanya,ba k’aramin dauriya ya nemo yasawa zuciyarshi ba na ganin bai bata mata k’walliya ba.

Hall ya cika tam su kad’ai ake jira,dan haka ana cewa sun iso d.j ya saki wakan aurensu.

Ameera ji tayi kaman ta zura da gudu ta koma bcos bata saba shiga cikin jama’a haka ba ga kuma idon mutane duka a kansu bama kamar ita dan ‘yan uwanshi da frnds d’inshi sai yabonta suke suna cewa sai yanzu Al’ameen ya samu mata.

Shagali akayi sosai a wurin,anci ansha sannan aka tashi kowa ya tafi cike da farinciki.

Lateefa tana k’wance a cikin bedroom d’inta tana wondering me ya hana Al’ameen dawowa har yanzu,sama-sama kunnenta yake jiwo mata gud’a.

Firgita tayi ta tashi zaune bcos kaman a mafarki take ji dan haka ta k’ara kasa kunne.aiko wata mai murya cikin ‘yan uwan Umma ta rangad’a gud’an dai-dai sun shigo main palour dan haka har tsakiyan kanta taji shi.

Zumbur ta mik’e tsaye tare da dafe kirji tana ” na shiga uku dama yaune auren nashi?shikenan na kad’e na lalace “.

Goge hawayenta tayi tace ” wallahi Al’ameen ya d’ebo ruwan dafa kanshi dan wallahi sai auren nan ya zama fitina a rayuwanshi sai yayi nadama dan zan goge sauran son da nake maka nayi maganinka “haka ta cigaba da sumbatu kaman zararriya,sai kaiwa da komowa take a tsakiyan d’akinta.

Su kuwa ‘yan kawo amarya sai mamaki da jinjina suke sunga gida kaman aljannan duniya,suna zaune sunata hira da bark’wanci anata dariya da shewa harda gud’a wanda Lateefa take ji kaman mashi suke dab’a mata a zuciya.

Basu wani jima ba aka maida su,aka bar amarya ita kad’ai sai kamshi take.

Jin gidan ya zama shiru ya tabbatarwa Lateefa ‘yan kawo amarya sun tafi nan taji wani b’angare na zuciyarta na ingizata taje taci ubanta d’ayan kuma na cewa k’yaleta tukun.

Tana zaune a bakin gadonta sai tsaka da warwara take.sallaman Al’ameen ne ya katse mata tunani.

Juyowa tayi cike da tsiwa da masifa tana mishi kallon wulakance.

Bai kulata ba ya zauna kusa da ita a bakin gadon tare da ajiye mata ledan hannunshi.kamin ya bud’i baki yayi magan ta wawuro ledan ta jefa mishi a jiki,kaji da drinks da suke ciki suka zube a k’asa.

” wallah Al’ameen baka isa ka wulakanta ni ba a gidan nan daga kai har wannan ‘yar iskan nan da ka kawo gidan”.

” karki k’ara yunkurin kiran mata ta da makamacin suna irin wannan dan wallahi zan iya miki abinda baki tab’a tsammani ba”yace yana kokarin danne fushinshi.

Cike da mamaki take kallon shi tace ” Al’ameen ni kake zarewa ido ? wallahi bari kaji kamin kamin abinda kake…..”

Wucewa yayi ba tare da ya tsaya jin sauran maganganun ta ba dan a yanda yake ji zai iya karyata ne in ya cigaba da sa insa da ita.

Part d’in amaryan shi ya bud’e ya shiga tare da sallama,ba kowa a palourn dan haka bedroom d’in ya wuce.

Sallama ya k’arayi ko motsi batayi ba balle ta amsa.wani sanyayan ajiyan zuciya ya sauke daya hango ta can karshen gado cikin lulub’i,d’akin yana fitar da wani ni’imantaccen kamshi

Murmushi yayi tare da maida k’ofan zai rufe yaji an banko k’ofan da karfin tsiya.

A razane ya juya sai ganin Lateefa yayi ta shigo tana dube-dube a d’akin.

Ameera itama duk ta rikice ta rasa inda zata sa kanta dan a rayuwa ba abinda ta tsana irin tashin hankali.

A guje Lateefa tayi kan Ameera da ta hango can ta mak’ale a karshen gado.

Cikin zafin nama Al”ameen ya cafkota yana ” meye haka baki da hankali ko Lateefa,me kike shirin aikatawa?”

Hayayyak’o mishi tayi ” a tsammaninka zaka Iya shigowa da wata karuwa ku k’wana a cikin gidan nan?wallahi sai……”.

Tagwayen maruka da tasmu a fu

Kanta shi ya katse mata masifan da take .

Dafe da kuncinta take kallon shi tace ” Al’ameen ni ka mara?”

“Abinda yafi mari ma zaki gani in dai akan mata tace,ke har kina da bakin kiran wani da mugayrn suna?”

Zatayi magana ya fizgota da karfin tsiya duk kokarinta na ganin ta k’wace hannunTa kasawa tayi dan ba k’aramin rik’o ya mata ba.

Bai tsaya a ko ina ba sai a main palour,jefata yayi kan kujera ta bugu da karfin gaske sannan ya nunata da yatsa yace ” wallahi in kin cika mahaukaciya ki koma d’akin nan ki ga abinda zan miki,banza dabba mara hankali”.ya juya ya koma d’akin amaryanshi cikin tsanan halayyarta.

Lateefa kasa motsi tayi saboda ta tsorata da yanayin shi gaba d’aya ya canza lokaci 1 kuma tunda take bata tab’a ganin shi cikin irin wannan yanayin ba dan haka tashi tayi ta koma part d’inta da gudu tana kuka.

[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀

*~UKUBAR KISHIYATA~*

????????????????????????

(Its all about love and betrayal)

Story by *~UMMEE YUSUF~*

        (Maman yusuf)

*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*

*~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*

*part sixteen*

Wani irin suya take ji zuciyarta nayi mata yau ita Al’ameen ya wulakanta akan wata?

Dialling no Aina’u tayi cikin kuka da tashin hankali take magana ” Aina’u kin ganshi can da ita har sun rufe d’aki,ni daman nasan na shiga uku.i’m finished Aina’u pls help me”.

” Lateefa wats going on,pls ki daina kuka ki gaya min me yake faruwa,waye a d’aki da yarinya kuma wacce yarinyan?Aina’u take jera mata tambayoyin nan a rude sabida yanda take jin k’warta na kuka.

Da k’yar ta saita muryanta da ya fara dishewa sannan ta zaiyane mata abinda yake faruwa,tun daga farko har karshe.

Ajiyar hrt Aina’u tayi tace ” haba Lateefa kiyi hak’uri mana ko kin manta dama boka yace mana ba makawa sai anyi auren,yanzu fa dole ne ki daure ki danne zuciyarki har lokacin da boka ya d’iba mana yayi,nd if u continiou like dis zamu sha wahalan aiwatar da aikin mu in lokacin yazo.nuna musu zakiyi ba ruwanki sannan kija ta ajiki by then komai zai zo mana da sauki hope kin gane”.

” nagane Aina’u but bazai gane bane abin akwai ciwo”.tace tana danna saitin zuciyarta inda take jin zafi kaman ana hura mata wuta.

” Lateefa kenan nasani mana tunda nima wanda nake so kullum yana tare da wata amma na daure saboda abinda nake hangowa gaba yafi na yanzu,shiyasa nake so kema ki daure yanda duk abinda zai faru ba wanda zai zarge ki”.

” i will try my best but waye kike so baki tab’a gaya min ba?”

D’an dariya Aina’u tayi tace ” zan gaya miki but for now k’wanta ki huta,sai da safe”.hanging d’in call d’in tayi ba tare da ta bawa Lateefa daman magana ba.

K’wanciyar tayi zuciyarta kaman ya fito take ji wai yau Ameen d’inta ne zai k’wana d’aki 1 da wata kuma a cikin gidanta.

Al’ameen yana komawa part d’in Ameera,a tsaye ya same ta a tsakitan palourn sai rarraba ido take.

Murmushi ya sakar mata lokacin da yake kulle k’ofan da key.

Tana tsaye ya gama ya shigo yazo dab da ita ya kama hannunta suka shiga cikin bedroom ya zaunar da ita a bakin gado,shi kuma ya durk’usa a gabanta yana lek’en fuskanta.

K’ara jan mayafin tayi ta rufe fuskanta.

Murmushi yayi yasa hannu ya bud’e mayafin tayi saurin rintse idonta,matsowa yayi yayi kissing d’in saman idonta.

Waro su tayi ta sauke su a kanshi suna had’a ido tasa hannayenta ta rufe fuskanta tana murmushi.

” *AMEERA*”ya k’ira sunanta kaman mai rad’a,bata amsa ba kuma bata bud’e fuskanta ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button