UKUBAR KISHIYATA Page 11 to 20

” ki k’wantar da hankalinki kar wannan abinda ya faru ya dame ki bcos tana da matsalan jinnu yanzu haka na bata magani tayi bacci,dan duk lokacin da ya tashi haka muke fama da ita”yace yana zama kusa da ita.
Batace komai ba amma har cikin zuciyarta ta tausayawa Lateefa kuma at d same time ta samu relief na cewa ashe ba haka halinta yake ba,da har ta fara tunanin ya zamansu zai kasance.
Tashi yayi ya shiga bathroom d’inta yayi alwala ya fito yace itama taje tayi ta fito suyi sallah nafila.
Batayi musu ba itama ta shiga ta d’auro alwalan ta fito.
Shi yaja su sukayi raka’a 2 sannan ya sallame,ya dad’e yana k’wararo musu addu’an zaman lafiya tana amsawa da ameen sannan suka shafa.
Tashi yayi ya fita palour sai gashi ya shigo da ledodi har 2 ya ajiye a tsakiyan rug carpet da yake shimfid’e a tsakiyan d’akin.
Fita ya k’arayi ya shigo dasu plates cups nd knife akan wani k’aramin tray ya ajiye tare da jawo ledodin ya juye musu gasassun kajin da suke ciki ya yanyanka sannan ya d’ago kai ya kalleta ta wani ta wani takure waje d’aya ko kallon inda yake ma batayi.
“Bismillah sauko muci nasan yunwa kike ji” yace still idosa akanta.
Girgiza kai tayi a hankali tace ” um-um na koshi”
Cike da tsokana yace
” kin isa ma kice kin koshi,bayan tundazu naga kina ta bin late din da kallo ta kasan ido kina had’iyan yawu.zo kici yarinya ki bar yin fulako”.
Waro ido tayi tana kallonshi kaman zatayi kuka,fisabillilahi in banda sharrin Al’ameen yaushe ta kallima inda yake bare ta had’iyi yawu?ita dai kam ta kasa sabawa da halin nan na Al’ameen komai tayi sai ya fassara shi nagaetive.
Sunkuyar da kai k’asa tayi tare da yin rau-rau da ido kaman zatayi kuka.
Jawota jikinsa yayi yana dariya yace ” noo my baby don’t cry nine ko?sorry na daina”.
Gutsuro naman yayi ya sa mata a baki yana rarrashi tare da lallab’ata,tun tana nonnokewa har ta sake taci d’an dsyawa bcos ba laifi tana jin yunwan .cup ya cika fresh milk ya bata ta sha sannan ya k’yaleta.
Zagewa yayi shima ya cika cikinsa dan rabon shi da abinci tun safe,hidimomi basu barshi ya samu zama ba balle ya tuna da abinci.saida ya gama sannan ya tattara wajan ya fad’a bathroom yayi wanka ya fito daga shi sai 3quater da singlet farare tas.
Tana zaune a inda ya barta ta takure cikin hijabin da tayi sallah,zuwa yayi ta bayanta ya rugume ta tare da bata wani hot kiss a wuyanta sannan yace ” tashi kije kiyi wanka kema zaki fi jin dad’in bacci”.
Murya na cracking tace ” a’a ba sai nayi wanka ba zan iya k’wanciya a haka……”bai jira ta karasa ba ya shure ta sai cikin bathroom ya dire ta.
” zakiyi ko inyi miki da kaina?”
Ba shiri tace ” ba sai kamin ba wallahi zanyi da kaina “.
Fita yayi yana mata dariya ” yace matsoraciya kawai”.
Bata dad’e ba ta fito cikin wani zurmumemen hijab da tayi sallah dashi,
Shi kuma yana ta aikin feshe wata arniyan red night gown da performes masu d’an karan kamshi.
Juyowa yayi suka had’a ido tayi saurin sauke nata k’asa tasiwa yayi da rigan a hannun shi yazo gabanta yace ” meye haka Ameera da hijabin zaki k’wanta?”
Gyad’a kai kawai tayi ba tare da ta d’ago ba ” ga riga nan kije ki canza ko kuma inzo in canza miki da kaina”.
Ba musu ta karb’a tayi bathroom a ranta kuma tana jin ba dad’i dan gani take ya takura mata dayawa shi ko kunya baya ji.
Kallon gown d’in take baki sake ganinta ‘yar k’arama da ita dan da k’yar ya rufe mata cinya kuma ba shi da maraba da net cos ba abinda zai rufe mata yana show sosai.
Haka ta daure ta saka gudun kar yazo yasa mata da kanshi kaman yanda yace.
Gaban dogon mirrow da yake cikin bathroom d’in ta tsaya kallon kanta,ganin she’s half naked yasa ta nemi wuri ta zauna dan bazata iya fita gaban shi haka ba.
Al’ameen yana zaune zama jiranta shiru har zuwa 15mins,hakan yasa ya tashi ya bita,cikin sa’a ya samu k’ofan a bud’e bata saka key ta ciki ba.
Tura k’ofan yayi ya shiga ciki,tana ganin shigowar shi ta fara kokarin rufe jikinta da hijabin da ta cire.
Zuwa yayi kusa da ita ya k’wace hijabin yayi wurgi dashi.
Wani wahalallen yawu ya had’iye saboda ganin had’add’en surarta a waje dan bai tab’a sanin haka take da sura mai d’aukan hankali ba sai yau saboda kullum cikin hijab take.
Cikin sassarfa yazo ya rungumeta tare da bin jikinta da hot kisses gaba daya a juye ya zama wani mutum.daban kaman ba Al’ameen da ta sani ba.
Ameera duk ta rud’e ta fara hawaye dama daurewa take.
Cak ya d’agata yayi kan bed da ita ya k’wantar shima ya k’wanta a gefenta tare da jawota jikinshi ya ruungume, sak’onni masu wuyar fassara ya shuga aika mata da zafi da zafi.
Daga nan nima nayi waje sai dai muce asha amarci lafiya *AMEERA*.
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
????♀????♀????♀????♀????♀????♀
*~UKUBAR KISHIYATA~*
????????????????????????
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman yusuf)
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*
*~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*
*part seventeen*
Har kusan asuba Al’ameen bai samu bacci ba sai kallon fuskan Ameera da yayi kaca-kaca da hawaye yake yi cike da zallan nishad’i dan sai yau yasan cewa mata suna suka tara,saboda bai tab’a samun natsuwa haka ba tare da Lateefa kuma sai yau ya k’ara tabbatar da zargin shi na cewa Lateefa bata kawo mishi budurci gidan shi ba.yayi shiru ne dai kawai dan yana sonta yayin da ita kuma ta d’auka tushe-tushen da ta kashe mak’ud’an kud’i a kaine sukayi tasiri.
Dak’yar ya samu bacci mai dad’i ya d’auke shi.
6:30am ya farka daga bacci mai nauyi daya d’auke shi,a gurgije ya fad’a bathroom yayi wanka tare da d’auro alwala ya fito ya zura farar jallabiya.
Komawa yayi kan gadon inda Ameera take baccin wahala,gefen fuskanta yake shafa a hankali.ture hannun tayi tare da turo baki gaba tacigaba da baccinta.
Murmushi yayi ya kawo bakinshi saitin kunnenta ya hura mata iska,magana ta fara cikin bacci tana ” Fateema meye haka,Umma kin ganta ko?”
Kamo bakin da ta turo gaba cike da shagwab’a yayi ya d’an ciza.
Bud’e ido tayi da sauri ta sauke shi a kanshi da ya tsura mata ido yana murmushi.
Waro idon tayi sosai tana kallonshi tare da mamakin me ya kawo shi gidansu,can ta tuna ashe fa jiya ba gidansu ta k’wana ba. tana tuna abinda ya faru tsakaninsu ba shiri ta rintse ido dan wani irin kunyanshi taji yana shigarta.
” tashi kiyi sallah prety ” yace yana kokarin d’agata.
‘Yar k’ara ta saki jin wani rad’ad’i a kasanta ga cinyoyinta kaman wacce tayi tsallen k’wad’o.
A rud’e yake mata sannu,tare da kamata har zuwa cikin bathroom ya had’a mata ruwan dumi sannan ya barta ya fito sannan ya tada sallah.
Yana fita ta shiga cikin ruwan ta k’wanta lamo tana jin dad’in yanda yake gasa mata jiki,
Saida taji ruwan ya fara sanyi sannan ta had’a sabo tayi wanka tare da alwala ta fito.
Yana zaune yana azkar d’inshi ta fito,murmushi ya sakar mata mai d’auke da sakonni kala-kala
Saurin kawar da kanta tayi,da sauri ta nufi kan sallayan da ya shimfid’a mata ta tayar da sallah.
Tana idarwa ta matso kusa dashi kanta a kasa tace ” ina k’wana “.