UKUBAR KISHIYATA 1-END

UKUBAR KISHIYATA Page 11 to 20

Jawota jikinshi yayi ya rugume tare da manna mata peck sannan ya rad’a mata kunne ” haka ake gaisuwa my prety nd thank u so much for d gift Allah ya mii albarka”.

Shiru tayi ta manne a kirjinshi dan bata so ta d’ago da kanta su had’a ido.

D’agata yayi suka koma kan gado ya ja musu bargo,ya shiga wasa da ita.

Gaba d’aya Ameera ta gama tsurewa dan bata manta wahalan da tasha jiya ba,saidai baiyi abinda take tsoro ba yaja musu bargo suka koma bacci.

11:20am suka farka,rad’a mata yayi a kunne ” tashi muje muyi wanka”.da sauri ta girgiza kai tana k’ara shigewa bargo.

Bata ankara ba taji ta a sama,wutsil-wutsil ta fara da k’afa tare da magiyan ya sauketa amma bai direta ba sai cikin bathtube.

Gaba d’aya kunya ya hanata motsi yayin dashi kuma ko ajikinshi saima fitina da ya isheta shi.

Haka suka gama wanka suka fito suka shirya,batayi wani make up ba just powder ta shafa sai wet lips da tasa amma tayi k’yau cikin riga da skirt da tasa na atamfa blue nd white.

Riko hannunta yayi suka fito palourn ta suka tarar an cika musu kan table da kayan breakfast.

Kujera yaja ya zauna,itama taja na kusa dashi zata zauna yayi saurin riketa yace ” me zakiyi?”

“Zama zanyi” ta bashi amsa a takaice.

“A ina ” ya kara tambaya,kujeran ta nuna mishi da hannu.

Jawota yayi ta fad’a jikinshi,ya sunkuya ya bata peck a goshi sannan ya gyara mata zama akan cinyanshi yace ” as frm today ga wajan zamanki nan”.

Batayi magana ba sai murmushi da tayi

Bud’e warmers d’in yayi d’aya bayan d’aya yana lek’en fuskanta yace ” me zan zuba miki”.

” kowanne ma ka zuba zanci”.

Shi ya zuba musu abincin a plate 1,yana bata a baki shima yana ci har suka kammala sannan suka dawo kan cushions d’in palourn suka zauna ya kunna musu kayan kallo.

D’ora kanshi yayi akan cinyanta suna kallon arewa 24,wata masifaffiya aka nuno tana ta bala’i a cikin shirin da suke haskawa.

Ganin matan yasa ya tuna da Lateefa koya ta k’wana oho mata.

Rungumo cikinta yayi daga k’wancen yace ” prety bari inje mu gaisa da yayarki”.

” inka je kace nima ina gaishe ta “tace tana kallon gefe dan da gaske taji wani iri a zuciyarta.

Saida yayi pecking d’in goshinta sannan yayi hanyan fita.

Kallon shi take tana murmushi bata san tayi nisa a sonshi haka ba sai yau, har ya kai k’ofa kaman yasan tana kallonshi ya juyo suka had’a ido da sauri ta d’auke idonta tana kallon gefe tare da murmushi.

Kamshin turaren shi taji a kusa da ita, ta juyo da sauri ta ganshi a gefenta yana murmushi yace ” na dawo dan naga baki yarda da tafiyata ba”.

Da gudu ta tashi tayi bedroom ta kulle tana dariya,shima dariyan gayi ya fice daga part d’inta cike da nishad’i.

Yana zuwa part d’in Lateefa ya nemi wannan farincikin ya rasa saima fargban ya zasu k’washe da ita, abu d’aya yasa a ranshi ba zaiyi tolarating rashin hankalinta ba.

Sallama yayi ya shigo palourn ya tarar suna hira da k’annenta,sai dai suna ganin shi suka mik’e bayan sun gaishe shi suka fita zuwa nasu part d’in.

Cikin fara’a ta tare shi tana ango kasha kamshi.

Kallon mamaki ya bita dashi na yanda ta rikid’e one time kaman ba ita bace jiya suka rabu b’aram- b’aram ba.

” mesa ka fito da sassafen nan ka bar min k’anwata ita kad’ai”tace tana murmushi.

Kallon aggon d’akinta yayi yaga 12:30pm take cewa safe?koda yake ya gane magana ta fad’a mishi a fakaice.

Bai kula da magan ba dan yaji dad’in canzawarta dan haka zama yayi a d’akin suna hira sama-sama har aka kira sallahn azahar yayi alwala acikin bathroom d’inta sannan ya fita zuwa masallaci dan gabatar da sallah azahar.

Yana fita ta k’washe da dariya tace ” zaka gane kurenkane yaro dan sai na gana muku bak’ar *UKUBA*a gidan nan daga kai har k’aramar karuwar da kawo cikin gidan nan”.

[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀

*~UKUBAR KISHIYATA~*

????????????????????????

(Its all about love and betrayal)

Story by *~UMMEE YUSUF~*

        (Maman yusuf)

*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*

*~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*

*part eighteen*

Part d’in k’annenta ta nufa dan fad’a musu abinda yake faruwa cos basu san da maganan auren ba.

Knocking ta fara jin k’ofan nasu a rufe.

Su kuma a wannan lokacin suna kan gado a tub’e suke tsirara suna aikata masha’ansu da suka saba.

Buggun k’ofan ne ya dawo dau cikin haiyacinsu,da k’yar suka suka rabu Shamsiya ta fad’a bathroom dan kar Lateefa ta fahimci wani abu.

Fa’iza kuma kayanta ta mayar sannan tazo ta bud’e k’ofan tana kikiro murmushin dole tace…” Aunyty kece da kanki?ai kin k’ira waya zamu zo mu same ki”.

Bata bata amsa ba tabi ta gefenta ta shiga ciki ta nemi kujera ta zauna sannan ta kai dubanta ga Fa’iza da ta kasa zama tace…” ina Shamsiyya?”

“Ta shiga wanka”.

” and u wat happen to ur eyes?naga sunyi ja”.Lateefa ta tambaya tare da kafe ta da ido.

Cikin in-ina ta amsa da cewa…” ammmm b…bacci na fara Aunty bugun k’fan ne ya tashe ni”.

“Ok ko kunsan cewa Al’ameen yayi amarya?”

A zabure Fa’iza ta kunduma ashar sannan tace…”amarya fa kika ce Aunty,ya akayi haka ta faru bamu sani ba?wallahi ubanta zamuci a gidan nan,wai Mama ta sani kuwa?”

” hmmm ban gaya mata ba dan nima bai gaya min ba,jiya ina zaune naji an shigo da ita”.ta bata amsa.

Shamsiyya ta fito daga bathroom d’aure da towel tace…”dama na gaya miki tun lokacin da ake gyara wancan part d’in”.

Murmushi Lateefa tayi ganiñ yanda k’annenta suka tada hankalinsu tace…”ku kwantar da hankalinku dan na gama shiri na,inaso ku zuba ido ku sha kallo kuma kar kuna wani tashin hankali ko canza fuska just kuyi abinda nace hope kun gane?”

” shikenan Aunty tunda haka kike buk’ata amma da kin k’yale mu dasu sai sun gane shayi ruwa ne”tace tana huci.

” don’t worry komai zai tafi tafi yanda ya kamata,yanzu zan k’ira Mama mu tattauna b4 inje gida in same ta”nan suka cigaba da kulla makircin akan Al’ameen da Ameera.

Al’ameen yana fita daga masallaci direct gidan iyayen shi ya nufa.

Alhaji da Hajiya suna zaune a palour suna hiran yanda biki ya kasance,sallamar Al’ameen ne ya katse su.

Shigowa yayi ciki bayan sun amsa mishi, neman guri yayi a kasa kusa da k’afan Hajiya ya zauna sanna ya gaishe su.

Cike da farinciki suka amsa ganin wata natsuwa da farinciki da suka gani kan fuskan d’an autan nasu.

“Ya naga gidan ba kowane?”ya tambaya yana k’arewa gidan kallo.

” tun 11am ‘yan katsina suka koma,munso su k’ara k’wana amma suka k’i saboda auren ‘yar kawunka baffa da za’ayi next week” Hajiya ta bashi amsa.

B’ata fuska yayi yace…”wai harda tsohuwan nan suka tafi itama bata tsaya taga amarya ba?”

Alhaji yayu dariya yace…” ai itace ta hura wutan tafiya sauran ma suka bi bayanta”.

K’ara shagwab’e fuska yayi zaiyi magana,Hajiya ta katse shi ta hanyan cewa…” Kai dai baka girma, ina amarya?”

Nan da nan fara’a ya cika fuskar shi yace…” tanan nan lafiya”

Nan hira ta b’arke tsakáninsu kan yanda bikin ya kasance har zuwa la’asar sannan suka fito zuwa masallaci shida Alhaji dan gabatar da farali.

Suna idar da sallah gida ya nufa yana tunanin ya barta ita kad’ai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button