UKUBAR KISHIYATA Page 11 to 20

Bayan tafiyan shi Fateema da sauran frnds d’inta suka zo suka taya ta yini suna mata tsiya,sai kusan 4 suka koma gida.
Suna tafiya ta shiga bathroom tayi wanka ta fito daga ita sai bath robe wanda kpo cinyarta bai gama rufewa ba.
Da yake tasan gidan bakowa yasa ta saki ranta ta fara shirinta cikin k’wanciyar hankali.
Zama tayi a gaban mirrow tayi shafe-shafenta sannan taje gaban sip d’inta ta ciro inner wears ta fara sawa.
Zame bathrobe d’in ta fara kokuwan saka brezia amma ta kasa, kaman zatayi kuka take ta trying saboda ko a gida Fateema ce mai taimakata kullum.
Kaman daga sama taji hannun mutum ta bayanta ya had’a mata mata abinda ta kasa.
A razane ta juyo sai ganin shi tayi a tsaye yana mata dariya.
Tsaban rikicewa rasa abinyi tayi,durkushewa tayi a wajan ta takure waje guda.
Dariya Al’ameen yake harda rik’e ciki yace…” dama ganina ne yasa kike shiga wanka da hijab? Tohyau Allah yau ya kamaki cos akan idona kikayi komai nd dis kunya zanyi maganinta”yace tare da zuwa gaban sip d’inta ya ciro mata wani gown na material maroon mai adon black flowers a jiki ya ajiye mata akan gado ya fita zuwa palour ya barta dan taji dad’in shiryawa.
Yana fita ta sauk’e wani ajiyan zuciya sannan tacigaba da shiryawanta,perfumes masu sanyin kamshi tayi amfani dasu wajan feshe jikinta dasu.bata saka d’an k’walin kayan ba sai wani black veil da tayi rolling kanta dashi sannan ta nufo palourn tana taku a hankali cikin natsuwa.
Zuba mata ido har ta k’araso gefe shi ta zauna ba tare da tace komai ba,shine yace…” i’m sorry my baby na tafi na barki ke kad’ai ko?”
Murmushi tayi tace” a’a su Fateema sunzo bayan fitanka,tare muka yini dasu dan basu dade da tafiya ba”.
K’wantar da ita yayi akan cinyan shi ya zame mata veil d’in yana wasa da gashin kanta yace” ni ina can na wuni da tunanin na barki ke d’aya ashe ke wunin dad’i ma kikayi”.
Dariya tayi tare da gyara k’wanciyarta a jikin shi suka cigaba da hiran su na masoya har aka k’ira sallahn magrib sannan suka mik’e dan gabatar da farali.
Bai shigo cikin gida ba saida yayi sallahn isha’i sannan ya shigo ya sameta ta canza k’walliyarta,doguwar rigar shadda dark blue yasha aiki har kasa ga d’an k’walin tayi mishi irin d’aurin nan mai steps ya matukar yi mata k’yau.
Tana zaune a kan kujera ya shigo ya karaso gabanta ya tsuguna tare da rik’o hannayenta yayi kissing sannan yace ” irin wannan make up haka ai sai kisa in manta kaina,kin ganki kuwa kaman mai zuwa beauty contents “.
Waro ido tayi tace ” haba mana zaka fara ko?”
“Fad’an gaskiya ba”yace yana dariya.
Hannunta ya kama zuwa kan dinning table dan cin abinci,kaman yanda sukayi breakfast yanzu ma haka akan cinyanshi ya d’aurata ta zaunasuka rink’a ciyar da juna a baki har suka gama.
” zoki rakani inyi wanka “yace yana mik’a
Mak’e kafad’a tayi tare da yin kasa da kai.
Lek’o fuskanta yayi yace ” zaki rakani ne ko kuma…..?”
“Ehh….ehh zzzzan raka ka”ta amsa muryanta yana cracking
Dariyan mugunta yayi cos ya san ya gama tsorata ta,sannan ya shige ya barta a tsaye.
Kaman bazata je ba amma tasan in bata je bama zai iya zuwa ya tafi da ita yasa ta fara jan k’afa a hankali har zuwa bakin k’ofan bathroom d’in ta tsaya.
Shahada tayi da ta gaji da tsayuwa ta bud’e ta shiga ciki,jikin k’ofan ta jingina ta tsaya kanta a kasa.
Tana d’agowa sukayi 4eyes dashi yana k’wance cikin bathtube,da hannu ya mata alaman ta karaso.
A ranta take mita ,wai mesa baya ganewa tana kunyan shine?
“Oya come on babyna ke nake jira” ya katse mata zancen zuci da take.
Bata da wani option daya wuce na zuwa.
Da dabara ya rinka janta har tasaki jiki sosai dashi,sun kai 1gud hour suna wankan sannan suka fito.
Shi ya zab’a mata night gown da zata saka,nan sukayi shirin k’wanciya suka k’wanta ya rungumeta sosai kaman wani zai kwace mishi ita sukayi baccinsu mai dad’i.
Haka suka yi ta zuba love kaman su lashe juna dan yanda Al’meen yake nuna mata luv yasa itama ta sake sosai dashi suka ci amarcinsu har 7 days da zaiyi a d’akinta suka kare,kuma a yau ne zai koma d’akin Lateefa.
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
????♀????♀????♀????♀????♀????♀
*~UKUBAR KISHIYATA~*
????????????????????????
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman yusuf)
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*
*~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*
*part nineteen*
Ameera tana zaune a palourn ta bayan tayi sallahn isha’i duk ta rasa me yake mata dad’i.
Al’ameen yana dawowa daga masallaci direct part d’in Lateefa ya wuce,ya samu ta baje a palournta tana waya,tana ganinshi ta katse wayan tayi tare da
K’irk’iro murmushi tanayi mishi barka da zuwa.
Bai zauna ba yace ta fito main palour yana son magana dasu,ta amsa da toh sannan ya fita zuwa part d’in Ameera.
Yana shiga parlourn yaganta ta zuba tagumi da hannu 2,tsayawa yayi yana kallonta yana jin ba dad’i a zuciyar shi dan yasan abinda yake ji a zuciyar shi itama shi take ji,gashi kuma ya sabar mata da abubuwa da yawa wanda yasan dole yanzu su dame ta.
Cire mata tagumin yayi lokacin da yake zama kusa da ita.
A d’an firgice ta juyo ganin shine yasa ta d’anyi dariya tace ” yaushe ka shigo ne?”
” tayaya zakiji shigowata while u re lost in ur thought,wai tunanin me kike ne haka?”
” nothing just bana jin dad’ine”.ta amsa mishi cikin dauriya.
Jawota yayi jikinshi yayi huging d’inta sannan ya fara rad’a mata magana cikin kunnenta yace…” am sorry Babyna nasan abinda yake damunki but am asuring u bai kai rabin yanda nake ji ba cos i will miss u badly.sai dai ina so ki k’wantar da hankalinki dan after 2days zamu kasance tare kinji?”
Gyad’a kai kawai take dan kukan da take ba zai barta tayi magana ba.hannu yasa yana share mata fuskanta,sannan ya d’ago fuskanta suka had’a ido,murmushi yayi mata itama ta mayar mishi.
Kissing d’inta ya shiga yi sosai,bai barta ba saida yaga ta samu natsuwa sannan yace ta tashi su fita main palour zaiyi magana dasu.
Yana rik’e da hannunta suka fito zuwa palour,nan suka tarar da Lateefa zaune tana jiransu.
Ameera da Lateefa suna had’a ido kowacce zuciyarta saisa ya buga,bama kaman Lateefa dan k’yaun Ameera shi ya razanata,ashe rannan kallon tsoro tayi mata.
Ita kuma Ameera ganin Lateefa goggayiyar mata kuma wayayyayiya shi ya bata tsoro,tayaya zata iya kishi da ita?
Gyaran murya Al’ameen yayi bayan sun zauna sannan ya fara magana yace…Lateefa dake zan fara tunda kece gaba da ita muna tare dake yau 14years kenen dan haka kinfi kowa sanin gidanki dani kaina kuma wannan…”ya nuna Ameera dake zaune tana wasa da wani zoben gold dake d’an yatsanta yace….
” k’wanwarki ce kuma bak’uwa,ina son kija girmanki ki rik’eta da amana kuma kijata a jiki.ke kuma Ameera ina son ki bata girmanta ku zauna lafiya tunda kinga ni ba zamaunin gida bane,soo in kin bata had’in kai kuka zauna lafiya jin dad’inku ne dukkan ku,nima hankalina zai k’wanta”.
Gyara zamanta Lateefa tayi tana tab’e baki tace…”muna godiya my Ameen kuma ka taya mu da addu’a Allah ya had’a kanmu muma zamuyi iya k’okarinmu na ganin bamu baka kunya ba”.