UKUBAR KISHIYATA Page 11 to 20

Murmushi yake cikin jin dad’i dan wani irin nishad’i yake ji cos baiyi zaton haka daga Lateefa ba,kallon gefen da Ameera take yayi sannan yace” kina da magana ne babyna?”
Girgiza kai tayi da sauri ba tare da ta d’ago kai ba.
“Alhamdullilah naji dad’in haka wannan ya nuna min tun yanzu zaman lafiya ya samu a cikin gidan nan,now sai kuyi shawara k’wana nawa-nawa zaku yanke?”
” ni a ganina k’wana 2 yayi koya kika ce Babyn angonta”Lateefa tace tana hararan Ameera cos tunda Al’ameen yace mata babyna ta kasa controling kanta.
Ameera ko tunda ta shigo kanta a k’asa yake dan haka bata san ma tanayi ba.
Yanzu ma da Al’ameen ya nemi ta fad’i ra’ayinta cewa tayi duk abinda sukayi dai-daine.
” toh ni zan shiga in k’wanta sai da safenku “tashi tayi ta nufi part d’inta ba tare da ta tsaya taji amsan su ba.
Da ido ya rakata har ta shige sannan ya dawo da duban shi kan Ameera da har yanzu kanta yana k’asa.
Zuwa yayi ya tsugunawa a gabanta yace…”ya dai babyna?”
Ajiyan zuciya ta sauk’e tana dubansa tare da k’ak’alo murmushi.
Cike da damuwa yace…”bana son in ganki cikin damuwa pls idan ba ki saki ranki ba bazan iya tafiya in barki ba”.
Gefen fuskan shi ta shafa tace ” ba damuwace a raina ba just ina tunanin yanda zanyi 2days without u,but dont worry ya wuce na daina”tace tana murmushi.
“Tashi muje in rakaki d’aki”.
Tashi tayi suna tafiya kaman basa so har suka shigo palourn ta,rungumeta yayi tsam kaman Zai maida ta ciki yana shinshina wuyanta,daga nan kuma maganan ya sauya dan kissing d’inta yake tare da romancin d’inta da zafi-zafi.
Ture shi tayi da taga yana shirin zarcewa.sake ta yayi suna maida numfashi dak’yar.
Juyawa yayi da sauri ya fita ko sai da safe bai tsayayi mata ba dan yasan in ya cigaba da tsayuwa ba zai iya controling kanshi ba
Yana fita ta zube a wajan tana kuka zuciyarta a cunkuse da kishi a ranta tana dole Lateefa ta musu hauka ranan da a kawota dan duk macen data d’and’ani zama da miji irin Al’ameen dole ta guji duk wani abinda zai rabasu koda na minti1 ne.
Mikewa tayi ta hau kan gado ta k’wanta taji duk pillown da ta d’aura kanta akai baya mata dad’i dan rabonta da k’wanciya akan pillow tun tana gida,juyi ta rink’a yi akan gadon dak’yar ta samu bacci ya d’auketa.
Al’ameen part d’inshi ya nufa yana tsammanin zai samu Lateefa a can amma yaga wayam bata nan dan haka bathroom ya fad’a da niyan wanka amma sai yaji ba dad’i saboda cikin k’wanaki da sukayi tare da Ameera ya saba da abubuwa dayawa wanda da bai san dasu ba a auren su da Lateefa.
A daddafe yayi wankan ya fito still bata zo ba har ya shirya cikin white pyjames d’inshi ya fito ya nufi part d’in Lateefa amma ga mamakin shi yaji k’*ofan ta a bud’e .
Bud’ewa yayi ya shiga sannan ya mayar da k’ofan ya rufe.
Tana k’wance suna waya ita da Salees d’inta taji motsi a palourn ta dan haka cikin sauri ta katse wayan ta tura shi karkashin pillow ta runtse ido kaman me bacci.
Ya dad’e tsaye a kanta yaga alama baccin take da gaske.
Hawa gadon tare da shigewa cikin duvet da ta rufu dashi,rungumeta yace ” har kinyi bacci?”
Mik’a tayi (irin ita mai baccin nan).
Bud’e ido tayi a hankali tace “my Ameen ka shigone,ina amarya?”
“Kema kinsan yau Ameen nakine meye na pretending”yace yan k’ara rugumeta.
” no ba pretending bane just kaima kasan yanda ciwon kaina yake in ya tashi but na sha magani,let me sleep for while i wiil b alright”tace tan yamutsa fuska tare da lumshe ido.
Wani kululun bakinciki ne ya tokare mishi mak’ok’ora dan ya fara gajiya da wannan wanda halinta wanda bata tashi rashin lafiyanta sai taga yazo gare ta.ba dan ya kasance mai yaki da zuciyarshi ba da tuni ya fad’a halaka.
Cike da jin haushin kanshi ya fice daga part d’inta yayi nashi tare da alkawarin ba zai k’ara waiwayanta ba tunda Allah ya mishi canji.
Yana k’wance a kan lallausar gadon shi sai juyi yake ya kasa bacci Ameera kawai yake bukata a wannan lokacin.
Kasa daurewa yayi ya jawo wayanshi dage side drower yayi dialing no Ameera.
Share this
[ad_2]