UKUBAR KISHIYATA Page 21 to 30

Sallama tayi mishi cikin muryan jan hankali bayan tayi recieving.
Wani sanyi yaji yana ratsa zuciyar shi har ya nemi bacin ran da Lateefa ta sa mishi ya rasa.
Tana jin shi ta cikin wayan ya sauke ajiyan zuciya sannan yace…” sorry Babyna kina bacci na tashe kiko?”
” bakayi bacci ba har yanzu”ta tambaye shi cikin mamakin ya akayi Lateefa ta bar shi har ya kirata a waya a wannan lokaci?
” tunaninki ne ya hana ni bacci,I’m really missing u Babyna wanda har nake jin ba zan iya controling d’in kaina ba.i’m coming to ur room right now”.yace mata in a serious tone.
Duk da taji dad’in kalaman shi amma hakan bai hana ta
Saurin katse ba tace… ” no Yayana kayi hak’uri kada kazo ka manta d’azu kai kake gaya min cewa inyi hak’uri zamu rink’a kasancewa bayan ko wani k’wana 2,kuma in kazo yanzu ita kuma kaga ai bamu k’yauta mata ba” a zuciyar shi yake cewa da kinsan wacece Lateefa da baki bakin kiba……
Muryarta ne ya sake katse shi a karo na 2 tace…” kuma bana son ka kasance cikin masu shanyayen jiki ranar gobe k’iyama”.
Jikin shine yayi mugun sanyi jin kalamanta kuma ya godewa Allah da ya bashi mace mai natsuwa kamarta cos he know Ameera is a blessing frm Allah.dan haka yace…” hakane Babyna nagode da kika tunatar dani gaskiya i will try my best wajan k’watanta adalci a tsakaninku insha Allah,nan suka kama hira kaman ba dare ba sun dad’e kamin suka hak’ura suka k’wanta bacci.
Da washe gari ya kasance monday ne dan haka Al’ameen tun 8 na safe ya shirya fita zai office,ko kallon kayan breakfast dake jere akan table baiyi ba ya wuce part d’in Ameera a lokacin kuma Lateefa tana can tana baccin asara da ta saba.
Yana shiga part d’int Ameera ya same ta fes taci k’walliya da wani material peach clour riga da skirt sun zauna das a jikinta saboda dinkin yabi jikinta tayi matuk’ar k’yau duk da ba wani k’waliya tayi ba.
Tana ganin shi ta tashi ta tare shi da murnanta dan ba k’arya tayi missing d’in mijinta.
Ajiye brief case d’in hannunshi yayi tare da bud’a mata bud’e hannayen shi,da gudu tazo ta fad’a kirjinshi suka rungume juna suna dariya.d’ago hab’anta yayi suna kallon juna yace..” i missed u so much Babyna…”
K’wantar da kanta tayi akan kirjin tana shakan daddad’an kamshinsa tace…”ina k’wana my one”.
D’agota yayi tare da bata peck a goshi sannan yace…” kin tashi lafiya Babyna?”
” lafiya lau,ya na ganka da jaka ko yau zaka fara fita aiki ne?”
” yes yau zan fara kuma in na tafi sai 6:00pm” yace mata cikin tsokana.
Shagwab’e fuska tayi kaman zatayi kuka tace…” wai gasikya yayi yawa ni dai ka rage time d’in ko in bika office d’in”tace cikin shagwab’a har da dire-diren k’afa.
Shiko kallonta ya tsayayi cike da sha’awa dan yana matukar son mace mai shagwab’a.kasa jurewa yayi saida yayi kissing d’inta sosai sannan ya saketa ya juya zai fita ta tsayar dashi ta hanyan tambayan shi ” kayi breakfast kuwa?”
Tsayawa yayi ya dawo da baya yace….”dont worry in naje office zan sha tea acan”.
Bata bashi amsa ba ta kama hannun shi har zuwa kan table ta zaunar dashi,nan da nan ta zuba mishi chips da fried egg a plate sannan ta had’a mishi tea mai kauri tace ..” bismilla”.
Tunda ta fara mishi hidima yake binta da wani irin kallo mai cike da zallan so,yaushe rabon da ya samu kulawa a wajan Lateefa haka ita da kullum tana bacci yake fita office ba ruwanta da yaci ko bai ci ba.
Ameera bata barshi ba saida ya cika tumbinsa sannan ta rako shi har bakin k’ofan palourn ta tace…”Allah ya bada sa’a ya kare ka daga dukan abin k’i”.
Hancinta yaja yana murmushi yace” ameen Babyna Allah yayi miki albarka”zuciyar shi fari sol kuma cike da jin dad’in addu’ointa ya fita zuwa office,zai iya cewa tunda yake da Lateefa bata tab’a yi mishi irin wannan addu’an ba shiyasa yake jinta daban a cikin zuciyar shi gata dai yarinya ce k’arama amma abinda take wajan kula da miji tafi manyan mata dayawa.
Lateefa duk ta fita hayyacinta saboda yanda taga Al’amern ya susuce akan Ameera,duk ta rame ji take kaman ta k’ona su kowa ya huta amma in ta tuna da maganan bokanta sai hankalinta ya d’an k’wanta saboda ta yarda da aikin shi.
A daddafe tayi wata 1da boka ya basu,lokaci yanayi suka hanya ita da Aina’u sai gidan boka.
” boka gamu nan mun dawo dai-dai lokacin da ka bamu”Aina’u ce takewa boka bayani yayin da Lateefa kuma tana zaune ta k’osa taji mai boka zaice.
Boka saida yayi wasu tsurkullen shi sannan ya d’ago kai yana kallonsu yace…”aikinki na yau ba mai sauki ne bane kaman da saboda yariyan tana da ibada sosai ba wani aljani da zai iya tunkarar ta a halin yanzu”.
Gumi Lateefa ta goge zuciyarta na bugawa da karfi jin abinda boka yace,cikin matuk’ar tashin hankali tace….” na shiga uku boka da kai kad’ai na dogara yanzu ya zanyi?” (waiyazubillah)
Dariya boka ya kece dashi sannan yace…” bukarar ki zata biya amma wannan karpn saida taimakon ki”
Cikin sauri ta katse shi tare da cewa…” ka gaya min komenene zanyi boka”.
Wani bakin kulli ya mik’o mata yace…” ga wannan ki sa mata a abin sha tana sha bacci mai nauyi zai d’auketa,ke kuma a lokacin da take baccin sai kije d’akinta ki samo rigarta dana mijinku zan baki wasu layu da guraye saiki nannad’e su da kayan ki tura su a k’arkashin gadonta.in kikayi haka toh kin gama kama gidan dan ba abinda zasu iya aiwatarwa saida umarninki,zasu kasance cikin matuk’ar tsoronki da shakkarki yanda ba k’ya zato.kece zaki mulke su son ranki dafatan hakan yayi miki”.
Wani irin dariyan farinciki ta fashe dashi cikin tsananin murna tace…” yayi boka zan aiwatar da komai yanda kac,wallahi sai na sa sun bauta min dukkan su 2 sai sun gane basu da wayo”
Makud’an kud’ad’e ta ajiye mushi wanda yafi na kullum sannan suka fito.
A hanyarsu ta dawowa gida Aina’u ta dubi lateefa tace…” besty yanzu ya zakiyi ki bata wannan maganin tasha?”
Harar Lateefa ta wurga mata tare da tab’e baki sannan tace…” sai kace baki san dawa kike magana ba?”
“Toh ai gani nayi ko fitowa batayi kikace”.
“Ke dai zuba ido kisha kallo”tace cikin isa.
” nasan zaki iya ba abinda zai baki wuya mata a gidan Ameenu”Aina’u tace tana k’ara zugata.
Cike da k’warin guiwa ta iso gida.
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
????♀????♀????♀????♀????♀????♀
*~UKUBAR KISHIYATA~*
????????????????????????
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman yusuf)
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*
*~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
*part twenty one*
Bayan dawowarsu daga gidan boka Lateefa duk ta tashi hankalinta kullum cikin tunanin ya za’ayi ta zubawa Ameera magani take,k’watsam rannan suna zaune da kannen ta a palour suna kallo wata dabara ta fad’o mata.
Cikin sauri ta juyo wajansu tace….
“ke fa’iza ina son kuje kifito min da ‘yar iskan can da my Ameen ya ajiye a can part d’in yanzu amma fa cikin dabara “. ta k’arasa maganan tana duba lek’en part d’in Ameera.