UKUBAR KISHIYATA 1-END

UKUBAR KISHIYATA Page 21 to 30

Cikin tsanin farincikin zata ga Ummarta ta tashi ta fito parlour wajan Hajiya kuma har tana aiyanawa a ranta matsalarta ya kusa karewa dan tasan Abba yana ji zaiyi wani abu akai.

[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: ????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀

*~UKUBAR KISHIYATA~*

????????????????????????

(Its all about love and betrayal)

Story by ~UMMEE YUSUF~

(Maman Yusuf)

*~GOLDEN PEN WRITER’S ASSOCIATION~*✨✨✨

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*

*~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*

*part twenty nine*

Hajiya fita tayi ta barsu ganin Al’ameen ya tsaya nuku-nuku yaki fita.

Tana fita ya kamo hannayenta duka 2 ya matse acikin nashi yana kallon cikin idonta yace…”Baby zan tafi sai kuma gobe in na dawo,ina son ki kula da kanki da kuma babyn mu”.

Gyad’a mishi kai tana murmushi ba tare da tace komai,kissing d’in goshinta yayi sannan yasa hannu ya shafa shafaffen cikinta a hankali ya mik’e ya fito parlour yayiwa iyayen shi sallama ya kama hanyan gida shida drivern Alhajin shi.

Shida saura driver yayi parking a compound d’in gidan,Al’ameen cike da fargaban me zai cewa Latifa ya sauka ya nufi cikin gida.

A main parlour ya tadda ta zaune tayi crossing legs d’inta tana kad’asu,cikin rawan murya yayi mata sallama wanda bakinshi ne kad’ai ya motsa amma babu sautin da ya fito balle mutum yaji,amma ga mamakinsa yaga ta taso da murnanta ta tare shi tanayi mishi ya jiki?

Har cikin bedroom d’inshi ta raka shi ta had’a mishi ruwan wanka sannan tace ya shiga yayi wanka.

Ba musu ya shiga wankan kuma sai a lokacin ya tuna ashe through out yau baiyi wanka ba farincikin cikin dake jiikin Ameera ya mantar dashi komai.

Ita kuma Lateefa fitowa tayi ta barshi fuskarta d’auke da murmushin mugunta dan tunda rana Aina’u ta kirata ta fad’a mata sak’on boka,ya tabbatar mata da kulle bakinsu da yayi kuma yace ta kwantar da hankalinta kaman yanda suka zo suka tafi da ita haka zasu dawo da ita da kansu.

Bayan sallah isha’i suka zauna yin dinner amma sai yaji abuncin ba dad’i Sam saboda yanzu ya saba da girkin Ameerarsa amma gudun masifar Lateefa yasa ya tuttura harda santin karya.

Koda suka dawo parlour suka zauna hira nan ma Al’ameen sam hankalin shi baya jikinshi yana wajan Ameera har ta kai Lateefa ta fara tsarguwa tace…” My ameen lafiya kuwa na ganka yau wani iri ko dai jikin ne har yanzu?”

Yak’e yayi mata wanda dashi g’wara babu yace…”eh jikin ne kuma gobe da sassafe muna important meeting shiyasa nake son k’wanciya da wuri “.

” ya kamata kaje ka k’wanta tun yanzu Dan karka makara”.

Tun kamin ya mik’e ta riga shi dama kaman jira take tana Hamma tace…”nima dama baccin nake ji kuma ina son yin nafilan cikin dare,”tana fad’an haka tayi hanyan part d’inta.

Da kallon takaici ya bita,baisan ranan da zata canza ba.gashi dai bashi da lafiya maimakon ta tsaya ta kula fashi shine tayi tafiyarta ta barshi.

Bedroom d’inshi ya shiga shima ya hau makeken gadon shi ya k’wanta,wayarshi ya jawo ya dannawa Ameera k’ira,a lokacin ta fara bacci taji ringing d’in wayar shi da ya bar mata kafin ya tafi.

Bata bukatan duba screen d’in wayan saboda tasan mai k’iran nata.

A kasalance ta d’aga wayan tasa a kunnenta a shagwab’ance tace…” Assalamu alaikum”.

“Sorry Babyna kin fara bacci na tashe ki ko?”

K’ara narkar da murya tace…”eh yayana kasan drugs da aka bani harda na bacci a ciki”.

Cikin muryan rarrashi yace…” Koma kiyi baccinki dama na k’ira ne inji lafiyarku keda Babynmu”.

Cikin jin dad’in yanda yake nuna kulawar shi a gare ta tace…” Lafiya lau muke tunda muna da kamar kai dole mu kasance natsuwa da k’wanciyar hankali”.

Murmushi ya sake kaman tana ganinshi kana ya d’ora da cewa” k’wanta kiyi bacci Babyna saina zo da safe” nan sukayi sallama ta koma baccinta mai dad’i cikin k’wanciyar hankali.

Da washe gari da sassafe Al’ameen ya shirya ya fice daga gidan Lateefa ko tashi batayi ba balle tasan ya k’wana.

Direct gidansu ya nufa ganin babban parlourn ba kowa ya tabbatar mishi masu gidan suna bacci.

Bedroom d’in Ameera ya wuce kai tsaye ya murd’a handle d’in ya bud’e ya shiga ya mayar da k’ofan ya rufe a hankali harda murza key.

Baccinta take cikn bargo ta kudundune kaman mai jin sanyi.

” sleeping beauty ” yace yana rage kayan jikinshi.

Hulan kanshi ys fara cirewa sai kuma riganshi ta shadda d’inkin tazarce shima ya cire ya zama daga shi sai vest da dogon wandon shi,hayewa gadon ya k’wanta kusa da ita.

Jawota yayi jikinshi ya gyara mata k’wanciya akan faffad’ar kirjinshi,yasa d’ayan hannunshi kuma ya rungumota sannan yaja musu bargo ya lullub’e su dashi.da yake shima baccin shi na jiya rabi da rabi ne,nan da nan bacci mai dad’i yayi awon gaba dashi.

Tara saura k’wata Ameera ta farka daga bacci sakamakon wata azabbabiyar yunwa da ya addabeta.

Ganinta tayi mak’ale akan kirjin mijinta,cike da so da k’auna take kallonshi kuma lokaci guda ta cika da mamaki da ta tuna cewa ba gida d’aya suka k’wana ba.yaushe yazo kuma? Ta tambayi kanta kuma ta rasa mai bata amsa.

Bata son katse mishi bacci sakamakon ganin yanda yake jin dad’in baccinsa,maida kanta tayi a hankali ta k’wanta tana kallonshi har agogon d’akin ya buga karfe tara cif.

A lokacin ne kuma dauriyarta ya k’are,ya kamata ta nemi wani abu tasa a bakinta dan yanzu a yanda take jin yunwan gani take in ta k’ara minti 5 zata iya halaka.

A hankali ta fara raba jikinta da nashi ta yanda take ganin ba zai farka ba but tun kafin ta gama raba jikinta da nashi taga ya bud’e ido yana kallonta tare da murmushi akan fuskarshi yace…” Kin farka Babyna”.

Gyad’a kai tayi tana maida mishi martanin murmushi tace…”yaushe kazo ne Yayana,kodai anan muka k’wana tare?”

‘Yar dariya ce ta subuce mishi yace…” Da safen nan nazo na tadda gidan duk kuna bacci sai masu aiki kawai Nagani suna aikinsu,nima dama da baccin nazo shiyasa kiga na kwanta.hala bakiyi sallahn asuba ba ko?”

Shafa gefen fuskanshi tayi sanna tace..” Haba wani baccine da zai hani sallah asuba akan lokaci,amma kai me ya hanaka baccin?”

Lakace mata hanci yayi yace…” Tunanin ki da Babyn mu shi ya hana ni bacci”.

Rau-rau tayi da ido kaman me shirin kuka tace…” Haba yayana ka rinka bacci mana bayan kasan muna lafiya karkashin kulawar Hajiya,kuma kaima kasan rashin bacci yana da illah ko?”.

“I know Babyna ayi min afuwa na daina ” ya k’arasa maganan yana rik’e kunnuwansa duka 2.

Fari tayi da ido tana kokarin mik’ewa ya rik’eta yace “ina zaki je?”

” wanka zanyi” ta amsa a takaice.

Mik’ewa yayi shima yana harararta da wasa yace…” Shine bazaki jira muyi tare ba?

“Rabonmu da wanka tare tun yaushe?”tace a cikin zuciyarta amma a zahiri dariya tayi ta juya da niyan shiga bathroom d’in abinta.

Taku 2 tayi kawai sai ji tayi an d’aga ta cak an nufi bathroom d’in da ita.

Sai cikin bathroom ya direta,suka fara wanka tare da wasanni

 Bayan sun fito daga wanka ya tayata shafa mai ya shiryata cikin kaya na alfarma da Hajia tasa aka kawo mata su tun last night sannan suka fito babban parlour suka tafda iyayen nasu akan table sun gama break fast suna hira.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button