UKUBAR KISHIYATA Page 21 to 30

Shamsiya ta ajiye remote d’in hannunta sannan tace…”dats great Aunty dama ni kullum mamaki kike bani da kika k’yaleta ta samu k’wanciyar hankali a gidan nan,yanzu kuwa zakiga aiki da cikawa,taso muje Fa’iza”.
Shamsiya tayi gaba Fa’iza tana binta a baya har bak’in k’ofan palourn Ameera,knocking sukayi har su biyu sannan suka ji ta amsa da” da waye ne ? ina zuwa”.
Sanye take cikin wata black abaya tayi rolling da veil d’in kayan,sosai yayi mata k’yau kuma ya kara fito mata da haskenta. tana tunanin waye haka by dis time? tasan dai ba mijin ta bane dan shi yana da key a wajen shi ko yazo sai dai ya bud’e ya shigo.
Har ta k’araso k’ofan bata daina zancen zucin ba.
Bakin fuska ta gani bayan ta bud’e k’ofan.
Fa’iza da Shamsiya baki da hanci suka sake suna kallonta dan basuyi especting zasu ganta haka ba.
“Sanun ku da zuwa, tace ganin basu da niyan maga saina mujiya da suka zuba mata.
Shamsiya ce tayi karfin halin cewa…” uhummm amarya dama mun zone dan mu gaishiki”.
Fara’anta fuskantata ne ya fad’ad’a, ta d’an matsa ta basu hanya, sannan tace ” ku shigo mana ya kuka tsaya a waje”.
Shigowa sukayi suna k’arewa palourn ta kallo cos ba karya ya burge su.
Saida suka zauna sanna Fa’iza tace..” nasan baki samu ba ko?”
Murmushi tayi tana wasa da yatsin hannunta tace..” eh gaskiya ban gane ku ba”.
Tab’e baki Fa’iza tayi tana gyara zama sannan tace..” muna cikin gida 1 amma bamu san juna ba,toh mu k’annen Aunty Lateefa ne ganin har kinfi wata a gidan bamu sanki ba shiyasa muka zo dan mu gaisa”.
Shamsiyya ta karb’e da ” ina zamu ganta kullum tana cikin part d’inta a kulle”.
Dariya Ameera tayi tana ” wallahi ba haka bane,kinsan in kana bak’o sai a hankali”.
” eh hakane kam amma tunda mun biyo ki yanzu kin wuce bak’uwa,sai ki saki jiki damu mu saba ayi zaman tare kema zaki fi jin dad’in gidan”.
Cikin jin dad’i Ameera tace…hakane kuma nagoda da zumuncin,let me get u something to drink”.
Rik’eta Fa’iza tayi tana ” noo da kin barshi kawai “.
B’ata fuska Ameera tayi tace..” haba mana ya haka kuma,ku da kuka ce in saki jiki daku mun zama d’aya shine za kuce ba zaku ci abincina ba?”ta karasa cikin shagwab’a.
Kallon sha’awa Fa’iza take binta dashi,can ta daure tace…” is ok ba sai kinyi mana kuka ba je ki kawo mana koma menene zamu ci kinji”.
Tana dariya tayi hanyan kitchen still idon Fa’iza na kanta.
Mari Shamsiyya ta zuba mata a cinya sannan ta dawo hayyacinta,ta juyo tana kallon yayarta spechless.
” come back to ur sence Fa’iza nd stop stairing at dat bitch”Shamsiyya tace tana hararnta cike da kishi.
Yawu ta had’iye tana kallon Shamsiyya still bakinta ya kasa furta komai.
” karki soma nagetive tinking akan yarinyan nan saboda dalili 2,first ina son ki tuna wacece ita nd 2 kuma zaki iya samu a wani hali bcos u re not sure she will accept u or not.pls Baby think twice b4 doing something” Shamsiyya tace mata tana shafa mata gefen fuska.
Ajiyan zuciya ta sauke tare da kamo hannun Shamsiyya ta rike tace ” tnx da kika tunatar dani if not i have done something rubbish” ta k’arasa da dariya but deep down her bata hak’ura ba kuma ta tabbatarwa kanta she will surely have her one day.
Suna cikin dariyan Ameera ta iso d’auke da katon tray ta cika shi da kayan ciye-ciye da drinks kala-kala ta ajiye a gabansu.
Sunfi 30 mins suna hira sannan suka ce mata zasu tafi.
B’ata fuska Ameera tayi tana ” har zaku tafi,pls ku zauna mana muyi hira”.
Da sauri Fa’iza ta d’auke kai cos in taga tana wannan shagwab’ar da ya zama al’adarta ji take kaman taje ta rungumeta.
” a’a in kina so ki fito muje main palour muyhiran acan,kinga sai mu k’ara sabawa “.
” ku bari zuwa gobe sai in fito muyi hiran acan” Ameera tace musu tana murmushi.
Fizgo hannun Fa’iza Shamsiyya tayi sukayi hanyan fita tana mita ” muyi tafiyar mu Fa’iza dama ba wani bak’unta dama kawai bata son alaka damune take wani fakewa da bakunta” Fa’iza dai binta kawai take dan sosai take nadaman shigowanta part d’in nan.
Har sun kai bakin k’ofa tayi saurin dakatar dasu ta hanyan cewa ” pls ku tsaya mu muje,dan Allah karkuyi fushi dani ba nufi na ba kenan”.
Tsayawa sukayi suna murmushi tare da cewa ” ko kefa”.
Jerawa sukayi tare suka fito palourn suka zauna tare da cigaba da hiransu.
Shamsiyya ce rike da phone d’inta tana rubatawa Auntynta short msg kan cewa gasu nan a palourn sun fito da ita.
Cikin minti 1 reply d’in Lateefa ya shigo mata.
Mikewa tayi bayan ta karanta massage d’in tace…” ammm ina zuwa pls” sannan tayi hanyan part d’in Auntynsu.
A tsakiyan palournta ta same ta sai kaiwa da komowa take ” gani Aunty” tace lokacin da iso gabanta ta tsaya.
” take dis ku tabbata kunsa mata shi a drink ta sha,pls try ur best my lovely sisters”.tace mata pleadlly.
“Don’t worry Aunty consider it done “.tace mata tana zuba maganin cikin wani drink dake cikin glass cup,ta zuba wasu glass 2 suka zama uku sai dai ta banbant zaman cups d’in sannan ta d’auki katon trayn ta fita zuwa palourn da ta barsu.
Ameera da Fa’iza sunan zaune a inda ta barsu suna ta kwasan dariya.
Dire trayn tayi akan center table na glass dake tsakiyan palourn sannan ta jawo shi gaban su.
” wai hiran me kuke ne?naga kuna ta kwasar dariya haka?”tace lokacin da take zama.
“Labarin k’wawarki Aisha nake bata,yanda tasha k’asa a gaban saurayinta”Fa’za tace tana dariya.
Dariya Shamsiyya tayi sannan ta d’auko drink mai ta mikawa Ameeera tace ” toh ya isa ga drink nan kowa ya ya sha dan muji dad’in hira”.
Ba tare da tunanin komai ba Ameera ta karba,suma suka d’auka suka fara sha suna hira.
Sun gama sha kaman da minti 10 Ameera ta fara jin dizzness ko bud’e ido dak’yar take yi can kuma ta yanki jiki ta fad’i kan kujeran da take Zaune ta kama bacci kaman matatciya.
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
????♀????♀????♀????♀????♀????♀
*~UKUBAR KISHIYATA~*
????????????????????????
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman yusuf)
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*
*~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*
*part twenty two*
Zuba mata ido sukayi dukan su 2 kowacce da abinda take tsak’awa a ranta.
Dawo da dubanta Fa’iza tayi kan yayarta fuska d’auke da damuwa tace…” sis me kika bata ne a cikin drink d’in nan tasha har ya jefata cikin wannan halin?”
Fuska cike da fara’a Shamsiyya ta amsa mata da cewa…” ni ba abinda na saka mata,hasalima Aunty ce ta bani tace mu bata tasha.i don’t know her mission amma let me call her”ta k’arasa zancen tare da dannawa Lateefa k’ira nan da nan ta fad’a mata halin da Ameera take ciki,cike da zumud’i tace gata nan fitowa.
Cinkin abinda baifi minti 2 ba sai gata ta fad’o cikin palourn kaman an jefota.
Sauri- sauri gudu-gudu ta k’araso hannunta na dama rik’e da tsurkullen da boka ya bata hannunta na hagu kuma rik’e da rigan Al’ameen ta k’araso wajansu tana” ke Shamsiyya zo ki raka ni ke kuma Fa’iza ki zauna da ita kamin mu fito”
Ta nufi part d’in Ameera ba tare da ta jira amsarsu ba Shamsiyya ta mara mata baya suka bar Fa’iza da taradaddin kar Allah ya basu sa’an cutar da ita dan yanzu ita tausayi take bata.