UKUBAR KISHIYATA Page 21 to 30

Suna shiga part d’in direct bedroom d’inta suka wuce,wani riganta na atanfm Lateefa ta binciko a cikin sip d’inta ta had’a da rigan Al’ameen ta nannad’e kaya tsafin boka dasu, Shamsiyya ta taya ta suka d’aga gadon suka tura kayan karkashin gadon sannan suka gyara komai kaman ba abinda ya faru suka fito palour.
Ameera saida ta k’washi gud 4 hrs tana bacci sannan ta farka.cikin baccin da tayi boka yayi nasaran yin aikin shi a kanta sannan ya turo wata aljana da zata zauna a jikinta ta hana ta addu’oin da take saboda kar aikinsu ya lalace.
Da ido kawai take binsu d’aya bayan d’aya ta kasa tantance wani hali take ciki har idonta ya sauka kan Lateefa da itama idon ta zuba mata dan taga reaciton d’inta.
Wani irin bugawa taji zuciyarta yayi kaman ya fad’o k’asa.
A take taji wani irin tsoron Lateefa na ratsa duk jinin jikinta,a yanda take ji a yanzu komai ta saka ta źata iyayi.
Tsawa Lateefa ta daka mata tana ” wace irin mayya ce ke da zaki zo ki tsare mutane da ido kaman na mujiya?”
Murya na rawa tace” Aunty kiyi hak’uri ba kallon ku nake ba”.
Wani malalacin murmushi tayi ganin tarkonta ya kama tsuntsu duk da dama ta yarda da aikin bokanta,yanzu saura Al’ameen take jira shima yazo taga yanda zaiyi.
Hada rai tayi tace ” oya tashi kije ki d’aura mana dinner”
Sunkuyar da kai tayi k’asa zuciyarta na k’ara speed tace…” me zan dafa Aunty?”
Tsawa ta k’ara daka mata cike da masifa tace…” ke dak’ik’iyar inace ina baki comand kina min tambayoyi…?
Shamsiyya ce tayi caraf tace…” ai dole ta tambaya Aunty ba’a saba cin mai maik’o ba a gida,so gwara ki bata order kar aje ayi mana k’wamacala”.
Gyara zama tayi tana wani huhhura hanci a garance tace…” je kiyi mana tuwon shinkafa miyan taushe sannan kiyi peppe soup d’in d’anyan kifi da fruit salad…kuma saura ayi sallahn magrib baki gama ba kiga yanda zanci ubanki a gidan nan”.
Jiki na b’ari ta mik’e cikin sauri kaman zata kifa ta fara laluben babban kitchen d’in gidan kasancewar tunda aka kawota gidan bata tab’a fita daga part d’inta ba.
Dariya Shamsiyya ta kwashe dashi tana ” shikenan mun samu sabuwar ‘yar aiki”.
“K’yale ni dasu sai sun gane shayi ruwane,dole ta bauta min daga yau zan dakatar da masu aikin cikin gidan nan”.
Fa’iza dai shiru tayi tana jin ba dad’i cikin zuciyarta saboda tausayinta.
Murmushine ya k’wace mata da ta tuna cewa itama zata iya amfani da wannan daman ta cimma burinta akanta.cikin jin dad’i itama ta shiga cikin hiran da suke.
Kujeran da ta gani guda d’aya a kitchen d’in Ameera ta zauna dafe da kirjinta da har yanzu bai bar bugawa ba,tana mamakin sudden change daya same ta.
Tasan tabbas tun farko tana tsoron Lateefa amma na yanzu na musamman ne tunda ko ido bata iya had’awa da ita balle tayi mata musu, gata harda sakata girki.
Cikin zuciyarta take cewa tasan Al’ameen yana zuwa zaiyi maganin abin yayi musu iyaka saboda ba zai yarda da wannan zaluncin ba.
Pls kuyi mange da wannan dan yau sau 3 ina typing yana gogewa.
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
????♀????♀????♀????♀????♀????♀
*~UKUBAR KISHIYATA~*
????????????????????????
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman yusuf)
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*
*~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*
*part twenty three*
Tashi tayi ta fara girkin da aka sata,saboda kar lokaci da aka bata ya kure gashi kuma tayi warning d’inta.
Bata dad’e ba ta kammala girkin gaba d’aya gidan ya karad’e da kamshin girkinta.
Wani had’dd’en set d’in warmers ta d’auka ta zuzzuba abincin a ciki sannan ta k’washe su ta kai kan dinning ta jera su.
Dawowa tayi cikin kitchen ta zauna tana tunanin fita,ba dan komai take gudun fitan ba sai dan kar su had’u da Lateefa.
Gajiya tsyi da zama a kitchen d’in kuma tana son yin wanka kamim Al’ameen ya dawo daga wurin aiki,dole ta mik’e ta fita tana jan k’afa.
Suna nan zaune a inda ta barsu ga kayan ciye-ciye a gabansu suna ci suna hira,yawancin hiran akan samun nasararta akan Ameera ne.
Daga can nesa dasu ta tsaya kanta a kasa tace…” Aunty na gama “.
Juyowa sukayi suka zuba mata ido suna mamakin wai har ta gama girkin bayan har kala 2 ta bata dan kar ta gama da wuri ta samu abin ci mata mutunci,sai gashi harta gama.daga ita har k’annenta ba abinda suka iya a fannin kitchen kasancewar mamarsu ba ruwanta da sasu aiki in dai zasu fita su kawo mata kud’i toh bata da case da su.
Kallon up nd down Lateefa take mata,cikin tsawa ta fara matq magana…” waye sa’an ki anan da zaki zo ki tsaya a kan mu kina magana without any respect ,daga yau in har zaki min magana ki tabbatar kin rage tsawonki “.
A hankali ta kai guwowinta k’asa idonta tab da hawaye amma bata bari sun zubo ba.
Murna fal cikin zuciyarta tace..” je ki gyara min bedroom da toilet d’ina yanzun nan kuma as from today kece mai gyaran duk bedrooms da toilets na gidan nan”.
Bata ce komai ba ta mik’e tayi hanyan part d’in Lateefa.
Tana b’ace musu Fa’iza ta mik’e itama tana d’an soshe-soshen rashin gaskiya tace…” ummm Aunty na bari in d’auko system na a bedroom d’inki “.
” ok kuma ki duba min ko wancan banzan tana min gyaran yanda ya kamata”.
Cike da murnan samun nasara tayi hanyan part d’in da saurinta,Shamsiyya ta bita da ido saboda tadan karya take komai na bukatansu yana part d’insu.
Ameera tana tsakiya gyaran palour Fa’iza ta shigo da sauri ta kama hannun Ameera suka koma kan kujera suka zauna,ita dai Ameera zuciyarta sai dakan 3 yake dan bata san da wacce muguntar tazo mata ba.
Cikin k’wantar da murya tace…” kiyi hak’uri Ameera ban san me yake damun Aunty ba take miki haka amma nayi miki alkawari duk lokacin da kike neman taimako kizo wajena zan miki koma menene….kinji?”tace tana shafa gefen fuskanta .
Mik’ewa tayi tsaye kanta a k’asa tace ” nagode da kulawarki Aunty bari in k’arasa sauran aikina”.
Bedroom d’in Lateefa ta shiga tana mamakin Fa’iza duk da kalamanta sunyi mata dad’i amma tana da kokonto a kai ga wani shafa mata jiki da take shiyasa ma ta shi ta bar mata palourn dan banbarak’wai abin yazo mata.
Tsab ta gyara mata ko ina sannan ta fito palour zuciyarta na bugawa
Tana shigowa da tsawa Lateefa wai me ya fito da ita bayan tasa ta aiki.
” na gama Aunty shiyasa na fito”tace kanta a k’asa.
” sauran toilets d’in gidan wa zai wanke miki ?” ta tambaya tana banko mata harara.
Juyawa tayi ta koma ta hau sama zuwa part d’in Al’meen ta hau gyaran parlourn duk da dama ko ina a kintse yake,ta kama handle d’in kofan bedroom taji muryan Lateefa ta hayyako mata…..
“Ubanwa ya baki izinn shigowa part d’in mijina?”
Ameera duk ta rud’e murya na rawa tace….” kiyi hak’uri Aunty ke kika ce in wanke toilets na gidan man duka shiyasa na shigo amma dan Allah ki yafe min”.
” tashi ki bani guri munfuka,sai ana magana ta rink’a wani sunne kai k’asa kaman mutuniyar k’warai”.
Tsimi-tsimi ta fice zuwa nata part d’in ,direct bathroom ta wuce ta had’a ruwan zafi ta shiga ciki ta kwanta dan yanda take jin bayanta kaman zai balle saboda tunda tazo duniya bata tab’a aikatuwa irin na yau ba.