UKUBAR KISHIYATA 1-END

UKUBAR KISHIYATA Page 21 to 30

Alwalan magrib ta d’auro bayan ta gama wankan sannan ta fito tayi sallah,tana addu’an Allah yasa lafiya ganin har anyi sallah Al’ameen bai dawo ba.

Al’ameen driving yake a mota ya taso daga gidansu sakamakon amsa k’iran Alhajin shi da yayi bayan ya tashi a office, murmushi yake shi kad’ai saboda yana cike da farincikin zaiga sanyin idaniyan shi wato Ameera cos yayi missing d’inta sosai.dan haka duk ya k’osa yaga ya isa gida.

Yana zuwa mai gadi ya bud’e mishi gate ya shigo cikin gidan.

Ya dade a cikin motan sannan ya samu courage d’in fitwowa a ciki sakamakon yana shigowa haraban gidan yaji haka kawai gaban shi yana fad’uwa ga wata fargaba da mutuwar jiki da suka sauko mishi lokaci 1 wanda baisan dalili ba.

Da k’yar da jan k’afa yayayi sallama ya shigo palourn farko, bakowa nan ya k’arasa main palour anan ya tarar da Lateefa zaune tana sanar da rabi cewa ta dakatar dasu daga aikin.

A razane rabi ta d’ago da kai tana kallonta saboda tashin hankali ta rasa bakin magana cos tun Lateefa tana amarya suke tare har ya zamanto ta kasance leader. 

Dariya Lateefa tayi tana ” k’wantar da hankalinki ba na sallame ku bane hutu na baku saboda nasamu sabuwar ‘yar aiki,ina son ku bar mata aikin tayi ita kad’ai na d’sn wani lokaci saboda ta saba”.

Rabi zatayi magana taga shigowar Al’amee,ba shiri ta had’iye maganarta jiki na rawa tayi mishi sannu da zuwa ta fita ta basu waje.

Kallon inda yake Lateefa tayi dan bata san da shigowar shi ba,suna had’a ido yaji duk duniya ba wanda yake tsoro da shakka sama da ita.

Cike da dauriya yayi yak’e yace…” my Lateefa kina hutawa ne?”

Harara ta galla mishi tace…” kai meye haka daga zuwa zaka wani cika ni da sututu,haba Ameeenu” ta k’arasa da jan gajeran tsaki.

Sassauta murya yayi yace…”Allah huci zuciyarki my queen “.

Tashi tayi tana murmushin nasara ta k’araso gabanshi tare da kama hannun shi tace…” muje kayi wanka sannan kaci abinci ko?”

Bashida bakin magana bare musu,haka yabi bayanta kaman rak’umi da akala har cikin bedroom d’in shi.

Fitowa tayi bayan shigarshi wanka ta shiga k’wakawa Ameera k’ira, wacce zamanta kenan a gaban dreesing mirrow danyiwa angonta k’walliya amma jin muryan Lateefa yasa ta tashi jiki na b’ari ta zumbula hijabi ta fito palour.

Zubewa tayi a gaban Lateefa kai a k’asa tace…” gani Aunty”.

Al’ameen yana sauk’owa daga stairs idonshi ya sauka kan Ameera da take durkushe gaban Lateefa tana masifance ta nan yaji zuciyar shi tana bugawa da sauri-sauri har ya k’araso wajansu.

[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀

*~UKUBAR KISHIYATA~*

????????????????????????

(Its all about love and betrayal)

Story by *~UMMEE YUSUF~*

        (Maman yusuf)

*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*

*~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*

*part twenty five*

Rufe k’ofan yayi da key ta ciki sanna cikin hanzari ya wuce bedroom d’inta.

Tana k’wance daga ita sai kayan bacci a jikinta wanda gaba d’aya ya tattare yayi sama ga gashin kanta duk sun baje kan pillown da ta d’ora kanta tana ta baccin gajiya.

Ya dad’e a tsaye a kanta yana kallonta dan ba k’aramin k’yau tayi mishi ba duk da ta rame tayi duhu cikin ‘yan k’wanakin nan.

A hankali ya lallab’a ya hau gadon ya k’wanta a gefenta yana gyara mata gashinta yana shafa ta a hankali.

Motsi tayi ta juyo kaman zata bud’e ido amma baccin yafi karfinta.

Matsota sosai yayi jikinshi ya rungumeta tsam yana mata rad’a a kunne yace…” wake up my sleepin beauty”.

Kaman a mafarki take jin kamshin turaren shi ga kuma d’umin jikin shi da taji yasa ta k’ara gyara k’wanciyarta a jikin shi tana shakan kamshim da tayi missing.amma jin muryan yasa ta bud’e ido a firgice.

A rud’e ta fara k’okarin zare jikinta daga nashi tana ” yayana dan Allah ka tafi kar Aunty tazo ta same wallahi zan shiga matsla babba”.

Rik’ota yayi da sauri yana shafa bayanta a hankali yace…” cool down mana ki k’wantar da hankalinki ba wanda zai shigo nan dan tana can tana bacci kinji..”

Fashewa tayi da matsanacin kuka mai tsuma zuciya tare da k’ank’ame shi ta fara magana.

“Yayana wai me yake faruwane?,ka taimake ni ka sanar dani me yake faruwa…?

Bai samu bakin magana ba sai shafa bayanta da yake har yanzu alamun rarrashi,toh shi mema zaice mata saboda shi kanshi baisan me yake faruwan ba.

Had’e bakin su yayi ya fara bata hot kiss yana aika mata da sak’onni cikin zafi-zafi saboda ba k’aramin missing d’inta yayi ba.

Bai barta ba saida suka faranta ran juna sannan ya shiga lallashinta da kalamai masu dad’i da taushi sai gata nan tana k’yalkalan dariya kaman ba ita ba,nan suka shiga hiransu ta masoya kaman basu da wata matsala har zuwa 3am sannan yayi mata saida safe ya fita da k’yar dan ji suke kaman kada su rabu.

Da fargaba ko zsi tarar Lateefa ta dawo d’akinshi,zuciyarshi sai bugawa yake kaman wanda yayiwa sarki babban laifi amma ga mamakinsa yana shiga d’akin yaga ba kowa kaman yanda ya tafi ya bari.

Zuciyar shi fari kal ya haye gadonshi ya k’wanta cike da nishad’i.

Ameera haka tacigaba da rayuwa a gidan Lateefa tana gana mata *UKUBA* iri-iri duk tayi bak’i ta rame ta fita hayyacinta,duk wanda ya ganta sai ya tausaya mata hatta masu aikin gidan suna tausaya mata dan ba yanda suka iyane amma wani lokaci suna fakan ido su tayata aiki bama kaman Rabi duk tafisu taimakonta.

Al’ameen shima duk ranan da Lateefa ta koma d’akinta sai ya lallab’a yaje d’akin Ameera su sha love abinsu.har yau baisan dalilin da take guduwa cikin dare ta barshi ba,yafi alakanta hakan da kin bashi hakkin shi da take baisan cewa raba dare suke da Salees d’inta suna waya ba.

Yau monday Ameera da k’yar ta fito daga part d’inta saboda k’wata-k’wata bata jin dad’in jikinta,kasala ce zallah yake damunta ga wani azababben ciwon kai da take ji tun cikin dare dan haka a daddafe ta gama aikinta na safe ta koma part d’inta tana neman magani bata samu ba dole ta hak’ura ta dawo ta cigaba da aikin saboda lokacin d’aura abincin rana yayi.

Faten doya da yaji ice fish da kayan lambu tayi musu,ta jera musubakan table kaman yanda ta saba sannan ta k’arasa palour inda ta samu Lateefa sun baje itada k’annenta sun cika palourn suna kallo.

Can nesa dasu ta durkusa dak’yar tace…Aunty na gama”.

Zuba mata ido sukayi a wulakance banda Fa’iza da take binta da murmushi.

Cikin basarwa da gadara Lateefa tace…” naji ina sauran aikin kinyisu?”

“Kainane yake ciwo Aunty banyi ba amma yanzu zanje….”a tsawace tace..” wat?,lallema yarinyan nan wuyanki yayi k’wari ya isa yanka har insaki aiki ki tsaya kina kawo min k’abli da ba’adi?,ba ciwon kai ba uban ciwon kai kike ba abinda ya dameni dan haka ki bace min da gani kamin in b’allaki banza kawai” ta k’arasa maganan tare da jan digon tsaki.

Daurewa ta k’ara yi ta yunkura ta tashita koma aikinta.

Shamsiyya tayi dariya tana jinjinawa Auntynta tace “Aunty kina wuta muna binki da fetir”.

Cike da ji da kai tace…” kad’an ma suka gani dan yanzu na fara bautar da ita”.

Ajiyan zuciya Fa’iza dake sauraransu tayi kana tace…” ni dai Aunty ina ganin da gaske take fa bata da lafiyat”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button