UKUBAR KISHIYATA 1-END

UKUBAR KISHIYATA Page 21 to 30

“Ina ruwana da rashin lafiyarta kai ta mutuma mana ni meya dame ni?”tace tana wani tab’e baki.

K’ara k’wantar da kai Fa’iza tayi tace..” ai shiyasa nake ganin ya kamata ta samu kulawa daga wajanki ko dan kiji dad’in bautar da ita”.

Murmushi Lateefa tayi tace…”ke Fa’iza in kin fara wannan nacin naki nasan ba bari zakiyi ba saboda haka kije ki d’auki paracetamol 2 cikin first aid box ki bata ta sha nd na bata hutun 10 mins kawai ta dawo kan aikinta”.

A kitchen Fa’iza ta taddata zaune rik’e da kanta da yake barazan fashewa.

Dafa shouldernta Fa’iza tayi,a firgice ta mik’e tana ” kiyi hak’uri Aunty yanzu zanyi wallahi”.

Rik’ota Fa’iza tayi da sauri tana mata murmushi tace..” k’wantar da hankalinki ba Aunty bace nice “.

Hankalinta ya d’an k’wanta da ganin Fa’izan dan ba laifi ita tana k’yautata mata ba kaman sauran sisters d’inta ba.

Da kanta ta bud’e fridge ta ta d’ebo mata ruwa tare da b’allo mata paracetamol 2 ta bata.

Ba musu tasa hannu ta kab’a ta watsa a bakinta tare da kora ruwan.

” kije d’aki ki k’wanta ki huta inji Aunty”.

Murmushi tayi tace ” nagode Aunty Fa’iza Allah ya saka da alkhairi”.

[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀

*~UKUBAR KISHIYATA~*

????????????????????????

(Its all about love and betrayal)

Story by *~UMMEE YUSUF~*

        (Maman yusuf)

*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*

*~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*

*part twenty four*

Gadan-gadan ya nufo su zuciyar shi na bugawa,rai a matuk’ar b’ace ya iso gaban Lateefa ya tsaya da niyyan yi mata magana.amma suna had’a ido ya manta me ya kawo shi wajan saima wani murmushi da ya sake mata yace…” my Lateefa yunwa nake ji”.

Murmushin itama ta mayar mishi tare da kama hannun shi sukayi hanyan dinning tana” dont worry ur food is ready my Ameen”.

Ameera ta dade a durkushe a inda suka barta saboda ta rasa kuzarin tashi daga wajan,dama a tunaninta Al’ameen yana dawowa komai zai daidaita komai,sai gashi ko kallon inda take baiyi ba bare tasa ran zai kulata ko d’aukan mataki.

Muryan Lateefa taji tana k’wala mata k’ira kaman tana wata duniyar.

Amsawa tayi ta mik’e cikin sauri ta isa dinning d’in ta durkusa nesa dasu kanta a k’asa tace…” gani Aunty”.

” k’washe kayan nan kije ki wanke su tas kamin ki k’wanta dan bana sin k’azanta”.

Wani abu ya rink’a ji a k’asan zuciyarshi lokacin da yaga tana k’washe kayan,yana son kallon fuskanta amma ya kasa yana tsoron kar Lateefa ta ganshi.

Ameera tana barin wajan Lateefa ta jashi zuwa parlour dan suyi hira amma shi ya kasa maida hankali kan hiran saboda rabin hankalin shi yana kan Ameera.

Dube-dube take a kitchen d’in inda ta bar abincinta amma cikin ikon Allah ta neme shi sama da k’asa ta rasa,gata sosai take jin yunwa cos yau ko lunch batayi ba.

Abinda bata sani ba Lateefa ce ta d’auke abincin nata ta bayar dashi dan mugunta.ganin yunwa na neman halakata yasa ta jawo sauran abincin dasu Lateefa suka rage ta cinye sannan tayi wanke-wankenta tare da gyara kitchen d’in tsab ta fito.

Ba kowa a palourn ta wuce part d’inta zuciyarta a cunkushe kan sabon rayuwa da ta tsinci kanta a ciki,bata dad’e da kwanciya ba bacci mai nauyin gaske yayi gaba da ita sakamakon gajiya da take tattare da ita.

Al’ameen zubawa Lateefa ido yayi wacce take bacinta cikin k’wanciyar hankali,yana son zuwa d’akin Ameera saboda yau k’wananta ne amma tsoron Lateefa ya hana shi koda yunkurin tashi ne bare yayi gigin fita a d’akin.

Yanzu da yana wajan Ameera ne suna can suna tattalin juna amma ita saidai ma ta kara mishi damuwa

Yasan kuma da gayya tazo ta k’wanta mishi a d’aki dan kar ya samu daman keb’ewa da Ameera.tunda sai suyi kusan sati 2 bai isheta kallo ba dama a wajan Ameeran shi yake samun kulawa.

Juyi yake yana ta sak’e-sak’e a zuciyar shi da k’yar bacci yayi nasaran d’auke shi.

Ameera data farka da asuba bayi mamakin rashin ganin Al’ameen ba saboda yanda taga jiya ya wofintar da ita.

Tana idar da sallah asuba bata tsaya yin addu’a ko azkar ba tayi hanyar kitchen,hasalima mantawa tayi anayi saboda wannan shine amfanin aljanin da aka turo mata.

Ruwan zafi daya sha kayan kamshi ta fara d’aurawa sannan ta d’ebo irish da take ganin zai ishi gidan ta fara aikin ferewa.

Kamin tagama firan har ruwan tean ya tafasa yanata kamshi,juyewa tayi a wani babban tea flask sannan ta fara soya irish d’in.

Tana gama soyawa ta samu wani babban bowl ta fasa eggs a ciki ta yayyanka mishi wadatattacen albasa ta soya shima,ta k’ara musu da kunun k’wak’wa sannan ta fito dasu kan dinning ta jerasu.

Komawa kitchen d’in tayi ta gyara ko ina sannan ta fito palourn ta share tare da yin mopping,b4 8am harta gama aikinta tayi wanka taci k’walliyarta da wani less peach colour da white stones a jiki tayi bala’in k’yau.

Zama tayi a bakin gadonta tana jira taji k’ira dan tasan basu tashi ba.

Ba tafi 10mins da zama ba taji ana zabga mata k’ira,cikin azama ta fito.

Kamshin turaren ta yasu d’ago kai suna kallonta.

Al’ameen kam kasa d’auke idonshi daga kanta yayi saboda gaba d’aya ta rikita shi.

Tsawan da Lateefa tayi yasa shi dawowa cikin hayyacin shi kuma ya nemo natsuwa cikin d’an k’ankanin lokaci ya sunkuyar da kai tare da wayancewa.

Ameera itama tuni tasha jinin jikinta ta fara karkarwa.

Lafiyayen marin da tajine ya sata mik’ewa ba shiri tare da dafe fuskanta inda Lateefa ta mara dan ga yatsunta nan tsab sun fito abinka da farar fata.

Nunata take da yatsa cike da masifa take magana…” ke k’aramar ‘yar iska wallahi zanyi maganin kine a gidan nan wato tsabar kinyi degree a karuwanci shine kikayi wannan k’waliyan harda saka ture kika zo gaban mijina ?”

Kama 1 kunnenta tayi ta murd’e iya karfinta sannan tace…” zanyi miki last warning a gidan nan,duk ranan da naga kinyi k’walliya ko kika saka turare a gidan nan hmmmm…..” murmushin mugunta tayi sannan ta cigaba” wallah sai na lahira ya fiki jin dad’i.dallah b’ace min daga nan bak’ar munafuka..”

Da gudu ta koma part d’inta tana kuka kaman ranta ya fita.

Lateefa ta juyo tana kallon Al’ameen daya sunkuyar da kai k’asa ba zaka tab’a tantance yanayin da yake ciki ba tace…” sorry my Ameen wannan munafukar tana son b’ata min rai da sassafen nan”.

Ajiyar zuciya yayi ya dago kai tare da kirkiro murmushin dole yace…” sorry my Lateefa kema kinsan bana son b’acin ranki”.

Jawo warmers d’in gabansu tayi ta fara serving d’insu cikin jin dad’i tace…” shikenan my Ameen na hak’ura”.

Abincin yayi mishi dad’i sosai tsakanin jiya da yau yasan an samu canji wajan girki a gidan dan ya lura Ameerarsa ce take girkin amma hakan baisa yaci ba sai jujjuya fork d’in hannun shi yake.

Ganin irin kallon tuhuma da Lateefa take aika mishi yasa ya zage ya fara tutturawa.

Suna gamawa ta rako shi har waitin palour abinda bata tab’a yiba wai dan kar ya samu daman branching a wajan Ameera.

Tun kamin ta karaso cikin palourn ta fara k’iran Ameera.

Fitowa tayi cikin wani jallabiya red fuskanta a kumbure babu make up d’in dazu sakamakon kukan da tasha.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button