UKUBAR KISHIYATA Page 21 to 30

” wuce ki gyara kan table d’in sannan ki gyara min bedroom kuma ki wanke min toilet tas ” tace mata a gadarance.
“Toh Aunty ” tace tana yunkurin mik’ewa domin taje ta aiwatar da abinda aka sakata.
Yauma bata samu zama ba sai kusan tara na dare dan haka wanka kawai tayi tabi lafiyar gado,cikin minti 2 bacci mai nauyi yayi gaba da ita.
Al’ameen yana k’wance amma duk a takure yake saboda yau k’wata-k’wata baisa Ameera a idonshi ba saboda Lateefa ta kara tsanta doka kan cewa in Al’ameen yana gida kar ta yarda ta fito ko tabi inda yake.
Abinda Lateefa bata sani ba shine boka yayi nasaran dasa tsoronta a zukatansu amma soyayyar da suke ma juna yana nan daram.
Bai saba k’wanciya tare da ita yasa yake jinsa a matse.
Motsinta daya ji shiya shi saurin rufe ido kaman mai bacci,yana jinta tana sauk’owa a hankali har ta iso bakin k’ofa ba tayi wani babban motsi ba gudun kar ya farka.
Yana ji ta bud’e k’ofan ta fita tare da maida k’ofan ta rufe duk a hankali tayi su.
Bayan ta fita kaman da 5mins ya bud’e idonshi yaga tabbas bata d’akin,zama yayi a bakin gadon ya kai minti 10 zaune amma baiji motsinta ba.
Tashi shima yayi cikin tsand’a kaman wani b’arawo ya iso main palourn yaga bata nan,rab’ewa ya dinga yi tsakanin cushins d’in palourn har ya isa hanyan part d’in Ameera cikin sa’a ya samu k’ofan a bud’e,ba wata wata ya bud’e k’ofan ya shiga.
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
????♀????♀????♀????♀????♀????♀
*~UKUBAR KISHIYATA~*
????????????????????????
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman yusuf)
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*
*~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*
*part twenty six*
Sakamakon gajiya da take fama dashi kuma ya hadu da kasala tana k’wanciya bacci mai dad’i yayi awon gaba da ita.
Baccinta take harda mafarkin su Umma da Fateema tana musu korafin sunk’i zuwa dubata daga nan suka bige da wasa da dariya ita da fateema wanda har yake fitowa a zahiri.
Ruwa mai bala’in sanyi da aka shek’a mata shi sanadin katse mata baccinta mai dad’i.
A gigice ta farka tana neman hanyan guduwa.
Ficikota akayi taji tare da kifa mata wani wawan mari da ya k’ara gigita ta tare da k’ara mata ciwon kai.
Muryan Lateefa da Shamsiyya suna zazzaga mata k’wandon rashin mutunci akan meyasa tayi bacci har lokaci ya k’ure gashi 5 ta gota batayi girkin rana ba har time d’in d’ora na dare yayi.
Shamsiyya itace a gaba wajan neman nad’a mata na jaki ,Fa’iza ta shigo da k’yar ta k’waceta tana basu hak’uri.
Hankad’a keyarta sukayi zuwa har cikin kitchen d’in sannan suka k’yaleta.
Tana kici-kicin d’ora girki Fa’iza ta shigo ta same ta.
Rik’ota Fa’iza tayi tana kallon yanda fuskanta ya kumbura yayi jah sai hawaye da take sharewa.
Zaunar da ita tayi ta fita sai gata sun shigo da rabi,tacewa rabi ta cigaba da aikin ita kuma Ameera taje ta k’wanta ta huta.
Har k’asa Ameera ta duka zatayi mata godiya tayi saurin rik’eta tana ” bana son haka Ameera ni sonki nake shiyasa bana juran inganki cikin wahala yanzu jeki k’wanta ki huta sun fita ba zasu dawo da wuri ba.
Fita tayi zuwa part d’inta zuciyarta cike da farinciki tare da bawa Fa’iza daraja na musamman a cikin zuciyarta.
Rabi sai jinjina abin take a ranta saboda tana da shakku akan Fa’iza meye dalilinta na yin haka alhalin tasan Shamsyya rashin mutunci,koma menene tana mata addu’an neman tsari daga masifar Lateefa da k’annenta.
Allah ya taimake ta har dare ba wanda yabi ta kanta,amma zazzabi da ciwon kai sun hanata bacci sai juyi take akan gado tana hawaye.
12:30 am Al’ameen ya lallab’o ya shigo part d’inta ya same ta a haka.
Hankalin shi inyayi dubu to ya tashi jin zafin jikinta har yayi over ga fuskanta da ya kumbura suntum saboda maruka da tasha a wajan Lateefa.
A rud’e ya d’agota yana jero mata tambayoyi…” Babyna meke damunki?,tun yaushe kike k’wance haka?”
Da k’yar ta iya d’aga hannunta na dama ta nuna mishi kanta.
K’wantar da ita yayi ya shiga cikin bathroom d’inta ya d’ebo ruwa a bowl da towel ya dawo kan gadon.
Rage mata kayan jikinta yayi sannan ya fara goge mata jiki da ruwan sanyi,daga nan ya fita parlour zuwa inda suke ajiye first aid box ya had’o mata drugs harda na zazzab’i.
K’ara d’agata yayi ya bata drugs d’in sannan ya k’wantar da ita yana ta mata sannu.
Zuwa 30 mins bacci yayi awon gaba da ita,yana zaune ya zuba mata ido yana jin wani abu a zuciyarshi wanda baisan dame zai fassarata ba.
Shi bai bar d’akin ba sai wajan karfe uku na asuba a lokacin jikin yayi sanyin sosai,haka ya wuce ba dan ranshi ya so ba.
Koda ya dawo d’akin shi kaman yanda ya zata Lateefa bata nan,rannan dai bai wani samu baccin kirki ba.
Kiran sallahn farko a kunnen Ameera,wanka ta farayi da ruwan zafi ko zataji dad’in jikinta .kuma ba laifi ta d’an ji dama-dama.
Sallah tayi sannan ta zura doguwar riganta na atamfa ta zumbula hijab ta fito aiki.
Haka kawai taji yau ranta ba abinda yake so kaman fresh milk,bata tsaya b’ata lokacinta wajan duba fridge d’in palourn ta ba saboda ya dade da zama empty rabonta dasu tun kamin Lateefa tayi nasara akansu.
Tana zuwa main palourn ta bud’e fridge Allah ya taimake akwaisu aciki,guda 2 ta k’wasa ta wuce kitchen gudun kar wani ya ganta duk da tasan cewa yanzu ko sallah basuyi ba.
Tana shiga kitchen kuwa ta kafa kai ta shanye k’wali d’aya sannannta fara aikinta cikin karfi hali dan har yanzu tana jin zazzab’in.
Al’ameen shima da saboda rashin baccin da baiyi ba last night ya tashi da ciwon kai har da zazzab’i.
Yana k’wance bayan yayi sallahn asuba basida niyan tashi bare yayi shirin office.
D’ayan wayarshi da yake kusa dashi ya fara ringing d k’yar ya mik’a hannu ya jawo wayan.
Sunan yayanshi Sa’ad ya gani yana yawo akan screen d’in dan haka ba b’ata lokaci yayi recieving call d’in yayi sallama.
Amsa sallaman yaya Sa’ad yayi bayan yana ce masa ya biyo hospital d’inshi yana da magana dashi.
” bros yau bazan fita office ba” ya bashi amsa.
” why wat happend”ya buk’ata.
Numfashi yaja yake cewa fever ce kawai yake d’an ji amma yanzu zai sha paracetamol.
” don’t u try dis kasan self madication ne nd u know i dont like it,just hold on gani nan zuwa” yana fad’an haka ya kashe wayan ba tare da ya jira amsan Al’ameen d’in ba.
Duk da abinda yake ji a jikin shi amma bai hana shi murmusawa ba saboda yanda yayunshi suke ji dashi.
Yana ajiye waya Lateefa ta shigo cikin k’walliyarta kaman mdi zuwa dinner sai baza kamshi take.
Turus tayiganin Al’ameen still cikin bargo,k’arasowa tayi gaban gadon tana ” my Ameen lafiya kuwa har yanzu baka tashi ba ?”
” fever ce take son kamani “yace mata lokacin da take zama kusa dashi.
Tashi tayi da sauri dan d’auko mishi magani ya dakatar da ita ta hanyan cewa “ya Sa’ad is on d way”.
Gaba d’aya ranta taji ya b’aci jin cewa Sa’ad zai shigo mata gida dan ita tun kamin auren su da taji ya kushe ta take jin haushin shi amma kuma koda wasa bata iya nunawa a gaban shi sabida duk rashin mututuncinta shakkan shi take.
“Okay ” kawai tace ta fice zuwa kasa ta sami Ameera tana goge-goge tana layi kaman zata fad’i.