UKUBAR KISHIYATA 1-END

UKUBAR KISHIYATA Page 21 to 30

“Keee” ta daka mata tsawa,a razane Ameera ta juyo tare da durkusawa k’asa tace…” Aunty ina k’wana”.

A wulakance take dubanta tace” ke rik’e gaisuwarki kuma ki tattara ki wuce part d’inki nd kada ki kuskura ki fito sai na neme ki”.

Amsawa tayi da “toh” ta tashi ta wuce part d’inta tana godewa Allah cos atleast zata samu hutu koda kad’an ne kamin su nemetan.

Wasu masu aiki ta kira suka cigaba da hidimomin gidan.

Cikin 20mins Ya Sa’ad ya k’araso gidan hankali tashe.

Sai da ya duba shi hankalin shi ya d’an k’wanta ganin cewa stress ne ya mishi yawa.

Sama- sama suka gaisa da Lateefa,ya kama hanyan fita Lateefa har ajiyan zuciya ta saki na samun relief.

Har ya kai bakin k’ofan fita ya dakata tare da juyowa yace…” bros ina amaryarka ne ban ganta ba? Ina ganin sau 1 na ganta lokacin da muka had’u da ku a gidan Hajiya har kamin alkawari zaku je mana yini muka ji shiru da alama rowanta kake” ya k’arasa cikin zolaya yana dariya.

Lateefa ji tayi kaman ta shak’e shi ya mutu.

Bata gama kulewa bama saida ta tsinci muryan shi yana ce mata ” uwar gida kirawo min kanwar taki pls”.

Bata da bakin musu haka ta fita tana tsine mishi albarka.

[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀

*~UKUBAR KISHIYATA~*

????????????????????????

(Its all about love and betrayal)

Story by *~UMMEE YUSUF~*

        (Maman yusuf)

*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*

*~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*

*part twenty eight*

A main palour suka yada zango anata hira da raha,Hajiya tasa ‘yar aikinta ta gyarawa Ameera d’akin da zata zauna,cikin k’ank’anin lokaci ta gyara yayi fes.

Nan Hajiya ta umarce ta shiga ta k’wanta ta huta.

Bayan ta shiga Hajiya ta dube su tace…” ina son maganan nan a rufe shi anan ya zama tsakaninmu kad’ai zai tsaya,kaima Al’ameen ban yarda ka fad’awa matarka ba ka bari in lokaci yayi ta gani ina fatan kun fahimta ?” 

Duk amsawa sukayi da “eh sun fahimta kuma zasu kiyaye,a haka taro ya watse duk suka tafi gidajen su amma banda Al’ameen da ya mak’ale yaki tafiya.

Yana ganin Hajiya ta shiga bedroom d’inta ya sulale yabi Ameera d’akinta.

Yana shiga ya maida k’ofan ya rufe,a tsaye ya sameta fitowanta kenan daga wanka.

Zuwa wajanta ya farayi idonshi akanta yana murmushi,yana k’arasowa ya jawota jikinshi ya rungume yana mata godiya.

Had’e bakinsu yayi ya fara kissing d’inta har suka fad’a kan gado,sun dad’e a haka sannan ya sake ta ya d’ora kanta akan kirginshi yana shafata a hankali yace…”,Babyna ranan da kika haifa min abinda yake cikinki bansan yanda zanyi ba dan farinciki da zanyi ba zai misaltu ba”.

Ita dai murmushi kawai take ta rasa bakin magana,saboda yanda taga duk sun rikice gaba d’aya saboda cikin dake jikinta toh ranan da d’an ya fito kuma fa?

K’ara narkewa tayi a jikinshi cikin shagwab’a tace…” yayana yunwa nake ji amma fresh milk nake so mai sanyi”

Kwatar da ita yayi akan gadon ya tashi yana ” bari in dubo miki yanzu amma ya kamata kici wani abu saboda Ya Sa’ad yace kar a barki da yunwa”.

” ni dai koma menene ka had’o da fresh milk”tace tana gyara k’wanciyarta.

Yana fita direct bedroom d’in Hajiya ya nufa lokacin tana shirin shiga wanka,ganin d’an autan nata yasa ta dakata tana dubansa.

Yana shafa k’eya yace…”Hajiya me za’a samu ne a gidan?Ameera ce take jin yunwa”.

Fasa shiga wankan tayi ta dawo da baya tace…” yanzu nake shirin insa Altine ta kai mata abinci,ko akwai abinda tace tana son ci?”

” komai ma zata iya ci sai dai wai a had’a mata da fresh milk” ya bata amsa.

Girgiza kai Hajiya tayi tace…” banyi zaton akwai fresh milk a gidan nan ba,kayi maza kaje ka sayo mata ni kuma zan sama mata abinda zataci da kaina”.

“Toh” yace ya fita da saurinshi zuwa wani mall dake kusa da gidansu,caton 6 na fresh milk ya siyo ya dawo gida ya samu Hajiya tayi mata peppe soup na hanta da k’oda yaji kayan kamshi da yaji yanda mai ciki zata ji dad’in ci.

Mai wankinsu Hajiya shi mallam tukur shi ya rink’a shigowa da kayan da Al’ameen ya sayo.

Hajiya baki bud’e ta kallon catons na fresh milk d’in tace…” lalle Al’ameen d’aukin ne haka?ina mutum d’aya zai iya shanye wannan kayan duka?”

Murmushi yayi yana sosa kai yace..”Hajiya aina zata tana bukatarsu dayawa ne”.

Dariya tayi tace…” hmmmm kai dai ka sani,yanzu ka bud’e 1 ka zuba a frdge daga nan kuma ga abincin can ka d’auka ka kai mata d’aki,kasan bata da lafiya kuma tunda cikin baiyi k’wari ba,bai kamata ace tana yawan zirga-zirga ba”.

Amsawa mata yayi sannan ya d’auki trayn abincn ya wuce d’akin ya sameta tana bacci abinta hankali k’wance.

Ajiye kayan yayi a hankali ya fita zuwa masallaci dan gabatar da sallahn la’asar.

Bayan ya idar da sallah ya dawo cikin gida tare da mahaifin shi,wajan frdge ya ya nufa ya bud’e ya d’auko k’wali 2 na fresh milk ya wuce d’akin Ameera dasu a hannu.

Akan sallaya ya sameta ta tana sallah itama.

K’arasawa yayi ya zauna a bakin gado yana jiran ta idar.

Bayan ta sallame ta dube shi tace…” Yayana baka je office ba yau?”

Jawota yayi ta fad’a jikinshi yace…” Babyna yau ba zancen zuwa office,ga babban office anan “.

Murmushi tayi kawai ba tare da tace komai ba l.

Saukowa yayi ya zuba mata peppe soup d’in a plate sannan yace…” Bismillah ga abinci harda fresh milk da kika bukata”.

Zamowa tayi itama ta zauna kusa dashi,sosai taci peppe soup d’in tana ta santi shi kuma yana zaune yana kallonta har saida ya tabbatar ta k’oshi sannan shima ya ci kad’an.

Dariyarta yake yanda take shan fresh milk d’in har tana lumshe ido saboda santi.

Tana k’wance a cinyanshi suna ta hira abinsu har 5pm.

Knocking suka ji daga bakin k’ofa Ameera tayi saurin tashi daga jikin shi Al’ameen ya bada izinin shigowa.

Hajiyace ta shigo ta dubi Al’ameen tace…” ka manta ne da tafiya gida yau?”

“ban manta ba Hajiya” yace yana sosa kai.

” tunda baka manta ba tashi ka tafi gida gashi har 5 ta gota”.

Agogon azurfa dake d’aure hannunshi yayi saurin dubawa yana cewa…” dama haka lokaci ya tafi ban sani ba?”

” mu da bama son matarka ta gane in har kana zuwa ka dad’e haka zata iya sa zargin wani abu a ranta kuma bana so kazo ka takura min ita dan ta huta na dawo da ita gidan nan dan haka tashi ka wuce”.

[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀

*~UKUBAR KISHIYATA~*

????????????????????????

(Its all about love and betrayal)

Story by *~UMMEE YUSUF~*

        (Maman yusuf)

*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*

*~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*

*part twenty seven*

A parlour ta Tatar da Ameera a baje a k’asa har ta fara bacci wai dad’in sanyin tiles d’in take ji.

K’afa tasa ta haure ta maimakon ta tashe ta,a firgice ta farka tana raba ido.

K’ara rud’ewa tayi ganin Lateefa akanta tana aika mata da muguwar harara.

Jiki na rawa ta durkusa ta fara bata hak’uri a zatonta tayi bacci mai nisa ne sosai har tayi laifi Dan bata manta maruka da tasha ba jiya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button