UKUBAR KISHIYATA 1-END

UKUBAR KISHIYATA Page 21 to 30

A wulakance ta d’aga mata hannu tace…” Keep quite idiot, me kika min da zaki ban hak’uri?ki wuce muje part d’in my Ameen Ku gaisa da yayan shi”

Kamin Ameera ta samu bakin bata amsa taji an murd’e mata kunne da karfin tsiya sannan tace mata..” Saura kiyi misbehaving da zaki nuna halinki na jakuna a wajan,hmmmm kema kinsan sauran ba saina bata bakina ba”.

Tana fad’an haka ta dugure mata kai tayi gaba abinta.

Da sauri ta mik’e tana gyara zaman hijabinta tabi bayanta tare da shafa kunnenta daya sha murd’a.

Sun same su suna tsakiyar hira da dariya shida d’an uwan shi,Ameera tayi sallama ta durkusa daga bakin k’ofa tana gaishe shi.yayin da Lateefa ta wuce ba tare da sallama ba ta zauna a bakin gado tayi crossing legs d’in tana kad’asu.

Ya Sa’ad Yana amsa gaisuwan tare observing d’in yanayinta a matsayin shi na doctor.

Al’ameen yana daga k’wance yana kallonta ba bakin magana amma ji yake kaman yaje ya rungumeta ya tambaye ya jikinta.

Suna gama gaisawa bata wani tsaya b’ata lokaci ba ta mik’e dan komawa part d’inta saboda ta kiyaye gargad’in da akayi mata.

Tana tashi jiri ya kwashe ta sakamakon zafin zazzab’in dake dake jikinta ga cikinta tun jiya baiga k’wayar hatsi ba,saurin dafa bango da tayi shi ya hanata fad’uwa.

“Subhanallah ba dai kema baki da lafiyan ba ya barki a gida?”ya Sa’ad ya tambsya Yana aikawa Al’ameen mugun kallo.

Sadda kai k’asa yayi ganin Lateefa nayi mishi kallon warning ta k’asan ido.

Ameera batace komai ba saima kokarin barin d’akin da tacigaba dayi.

Dakatar da ita yayi da sauri ganin da gaske fitan zatayi.yace…” Wai meyasa kake Al’ameen? In kai Baka son hospital meyasa zaka bar iyalinka cikin irin wannan hali”.

Tsaki yaja yana mai mik’ewa yacewa Ameera da take tsaye waje 1 ta kasa gaba 

ta kasa baya ” muje hospital in duba ki i can’t tolarate dis”.

Yana fita Ameera bata tsaya bata lokaci ba ta mara masa saboda itama tana bukatar ganin doctorn.

Yana zuwa bakin motan shi ya bud’e mata back seat ta shiga ta zauna ya rufe sannan ya zagayo ya bud’e driver seat ya zauna ya juya ya kalli k’ofan palourn yaga da gaske Al’ameen bashida niyan biyosu dan haka ya ciro wayarshi ya danna mishi k’ira a lokacin Lateefa tana zaune agefen shi tana mitan halin Ya Sa’ad kiran ya shigo wayarshi.

Bai kulata ba ya d’aga wayan yasa a kunnen shi,kamin yayi magana yaji muryan yayanshi yana cewa..”fito muu tafi tare dan kaima ban gama da kaiba” yana gama fad’an haka ya katse k’iran tare da maida hankalin shi hanyan fitowa daga palourn.

Ajiye wayan Al’ameen yayi tare da mik’ewa daga kan gadon,da ido Lateefa tabi shi har zuwa bakin closet d’inshi ya cire rigan baccin shi ya zura jallabiya milk colour akan wandon rigan baccin shi.

Dawowa yayi bakin gado ya k’washe phones d’in shi yayi hanyar fita ba tare da yace mata cikanki ba.

Da gudu Lateefa ta tari gabanshi tana aika mishi mugun kallo tace…” ina zuwa haka mallam?”

” Ya Sa’ad ne yake k’irana” ya bata amsa yana murmushi saboda yasan ba yanda ta iya dashi.

Wucewa yayi abinshi ya barta nan tsaye cike da tashin hankalin me zai faru in suka fita tare.

Cike da farinciki Al’ameen ya fito kasancewar zuciyarshi ta k’wad’aitu da zuwa amma tsoro ya hana shi Allah ya kawo mishi hanya cikin sauki.

Front seat ya bud’e ya shiga,Ya Sa’ad yaja mota suka bar gidan.

Lateefa tana jin tashin motansu tayi bedroom d’inta cikin matukar tashin hankali ta k’ira Aina’u.

Ringing 2 yayi ta d’aga tana ” Hajiya a gidan Al’ameen ya akayine da sassafen nan?”

“Aina’u ba lafiya wannan yayanshi mara mutuncin yana son rusa min aikina”.

Wani yayan shi kuma?” Aina’u ta tambaya.

Nan Lateefa ta k’washe abinda ya faru ta fad’a mata sannan ta d’ora da cewa..” pls besty ina son yanzu kije gun boka ya rufe musu baki kar su iya furtawa kowa abinda yake faruwa,yanzu zan miki transfer ta acc d’inki”.

“Toh ” tace tare da tabbatar mata da samun nasara sannan sukayi hanging.

A hospital kuwa suna zuwa ya Sa’ad ya bata gado tare da jona mata drip wanda ya had’ata da alluran bacci a private room da yake duba familynsu kawai sannan ya fara dubata.

Jininta ya d’eba ya bayar aje lab a g’wada yanzu-yanzu sannan ya fita a d’akin ya barsu.

Al’ameen jawo kujeran roba dake gefe yayi zuwa gaban gadon ya zauna ya kallon yanda fuskarta tayi fayau ya k’ara haske tana bacci.

Jikinshi yayi sanyi sosai ganin yanda Ya Sa’ad ya share shi tun a mota har zuwa yanzu,yasan fushi da yayi ba karami bane kasancewar shi baya fushi da wuri.

Toh shi ya zaiyi ya fahimtar dashi ba laifinshi bane?

Tsam ya mik’e da niyan zuwa office d’inshi dan ya gaya mishi halin da suka tsincin kansu shida Ameerar shi a ciki ko zasu samu mafita.a bakin k’ofa suka had’u dashi yana shigowa da wata peper a hannunshi fuskarshi kuwa kaman gonan auduga babu sauran fushin nan da ya fita dashi.

Kallon mamaki Al’ameen ya bishi dashi har ya manta abinda yayi niyan gaya mishi.

Hannunshi Ya Sa’ad ya rik’o suka dawo cikin d’akin har bakin gadon da Ameera take bacci,shi dai Al’ameen da ido yabishi yana neman karin bayani.

Huggin d’inshi yayi yana furta ” alhamdullilah!!!.”

Mik’awa Al’ameen papern yayi yana dariya wanda rabon Al’ameen da yaga yayi irinta har ya manta,kasancewar shi ba ma’abocin yin dariya bane sai dai murmushi.

Karanta result d’in yayi amma kwata-kwata bai fahinci me yake nufi ba,idon shi inba gizo yake ba pregnany test ya gani kuma da sunan Ameera akai.

D’agowa yayi yana kallon yayan nashi tare da neman karin bayani.

“Yes bro ur wife is 2 months pregnant”ya kara tabbatar mishi.

Wani yanayin da bai tab’a tsintan kanshi a ciki ba ba yau yake ji.

Hawaye ne yake zuba a idonshi bakin shi yana motsi alamun yaña son yin magana amma ya kasa fidda sauti ko kad’an.

Rungume Ya Sa’ad yayi yana hawayen farinciki,ashe shima yana da rabon ganin k’wanshi a duniya.

Da k’yar Ya Sa’ad ya fitar dashi daga d’akin dan yana kokarin katsewa Ameera bacci wajan murna.

Office d’inshi ya kaishi ya zaunar dashi sannan ya k’ira iyayensu yayi musu albishir na samun jika daga d’an autansu,daga nan kuma ya cigaba da kiran sauran ‘yan uwansu suma ya sanar dasu duk cike farinciki suka ce gasu nan zuwa.

Cikin k’ankanin lokaci suka cika hospital d’in anata taya juna murna kaman riga da anyi haihuwar.

Ameera bata san wainar da ake toyawa tana ta baccinta,sai bayan sallahn azahar ta farka daga baccin.

Har rige-rigen yi mata sannu suke duk sai taji kunya ya rufe ta ganin harda Hajiyar Al’ameen a ciki.

Bayan tayi wanka tayi sallah,tea mai kauri Hajiya ta had’a mata tare da peppe soup na naman rago zallah sannan ta zo ta zauna a gefenta ta fara bata amma Ameera ta kasa sakewa taci abin kirki.

Ganin haka yasa Hajiya tace duk su fita a barta ta samu taci abinci,ba musu duk suka fice tare da ja musu k’ofa.

Al’ameen kaman jira yake suna fita ya taso da sassarfa ya rungumeta yana sauke ajiyan zuciya,ture shi Ameera ta fara tana cewa…” haba yayana ka bari mana kar wani ya shigo ya ganmu a haka”.

Ba tare da ya sake ta ba yace…” let me feel u Ameera yau ina cikin farinciki wanda ban tab’a tsintan kaina a ciki ba, bani kad’ai ba all my family re happy because of u”.

D’ago kanta tayi tana kallonshi taga idonshi duk yayi ja alamun hawaye zai iya saukowa at anytime.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button