UKUBAR KISHIYATA Page 21 to 30

” ni kuma me nayi haka?”ta tambaya idonta itama yana cikowa da hawaye.
Result d’in da yake rik’e dashi a hannu tun d’azu ya mik’o mata,karb’a tayi ta fara karantawa ai bata gama karantawa ba tayi jifa dashi ta rufe bakinta da hannunta na dama hannunta na hagu kuma tana yarfe shi tace…” na shiga 3 yanzu dukkansu sun sani?”
Dariya ma ta bashi ganin yanda yarintarta ya fito a fili,maimakon yayi dariya yab’ata fuska yace…” kinga kuwa kowa ya sani har Hajiya saida tayi fad’a”.
Waro ido idonta tayi gaba d’aya tana kallonshi cikin tashin hankali can kuma ta fashe da kuka tana ” wallahi ni ba zan zauna anan ba tafiyata zanyi”.
Kunshe dariyarshi yayi yace..” ki tafi ina? Ai kina tafiya kuma ace kinyi rashin kunya”.
Yarfe hannu ta cigaba dayi tana..” wayyo toh ya zanyi wai?”
Haka ya rink’a zolayarta tana k’ara rud’ewa da k’yar ya. rarrasheta tayi shiru ,yace mata wasa yake mata tare suka ci abincin suna hirarsu cike da nishad’i.
Bayan sun gama yana tattare wajan su Hajiya suka shigo suna k’ara mata ya jiki,ita kuma ji take kaman ta nutse k’asa saboda kunya.
Ya Sa’ad ne yace…” Alhamdullilah jikinta kam yanzu da sauki zan sallame ta amma ba zan yarda Al’ameen ya tafi da ita gida ba saboda bashida kula zan kaita gidana incigaba da kula da ita har cikin yayi k’wari sannan zan yarda ta koma gidanta”.
Hajiya tayi caraf tace…” ban yarda da wannan idean ba, ni zan tafi da ita ta zauna a karkashin kulawata sai dai kullum ka rinka zuwa gida kana duba min ita”.
Nan yace “shikenan Hajiya ai duk 1ne”.
Al’ameen yana jinsu baisa baki ba amma zuciyarshi fari kal jin cewa ba zata koma cikin *UKUBAR* Lateefa ba kuma yana ganin k’ila su samu solution d’in matsalarsu kamin ta samu lafiya.
Cikin ‘yan mintina suka harhad’a kayansu sukayi gidansu Al’ameen.
Alhamdullilah naji sauki sosai kuma ina mika gdy ta tare da jinjina ku my fans ,ina yinku irin sosai din na
[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: ????♀????♀????♀????♀????♀????♀
*~UKUBAR KISHIYATA~*
????????????????????????
(Its all about love and betrayal)
Story by ~UMMEE YUSUF~
(Maman Yusuf)
*~GOLDEN PEN WRITER’S ASSOCIATION~*✨✨✨
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*
*~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
*part thirty*
Ameera suna shiga d’akin,d’an k’aramin fridge dake gefen gadon ta nufa ta bud’e ta d’auki fresh milk mai sanyi ta kafa kai bata d’aga ba sai da ta shanye shi tas.
Al’ameen da yake zaune a kan kujera yana kallonta yace…”ke dai yanzu kina son wannan abin dayawa”.
Sai da ta sauke empty roban a bakinta sanna ta amsa mishi da…”wallahi yayana in bansha ba jina nake ba dai-dai nake ba kuma sai in rinka jina… “Turo k’ofan da akayi tare da sallama shiya dakatar da maganan da take.
Altine ce ta shigo d’akin d’auke da katon tray da warmers akwai ta ajiye a kan rug dake tsakiyan d’akin tare da gaishe su,amsa mata sukayi fuska a sake.
Fita ta k’arayi ta dawo da wani madaidaicin tray mai d’auke da tea flasks da plates da cups ta ajiye ta fice tare da rufo musu k’ofa.
Kama hannunta yayi suka sauka k’asa inda Altine ta jera musu kayan breakfast.
Al’ameen shi ya fara bubbud’e warmers d’in yana dubanta yace…” Me zaki ci in zuba miki?”
“Zuba min pepper soup d’in saboda bakina yafi son Abu mai yaji”.
Zuba mata yayi a plate ta fara ci,shi kuma chips ya zuba suna ci suna hiransu.
Al’ameen yace…” Babyna wai kin fad’awa su Umma rashin lafiyarki kuwa?”
“Um-um ” tace tana tura katon tsoka bakinta.
“mesa baki fad’a ba?” Ya bukata.
“Zan k’ira wayan Fateema anjima in fad’a mata sai ta gayawa Umma”.
” Fateema kenan sarkin rawan kai bansan meya hanata zuwa gidanmu ba”yace yana murmushi.
Bata fuska tayi tace…” Hmmm tana son zuwa amma Abba ya hana dan ba abinda ya tsana kaman fita anguwa daga makaranta sai gida”.
Gyad’a kai yayi yana ajiye tea cup dake hannun shi yace…” Abba yana da gaskiya cos ‘ya mace sai da kula”.
Bayan sun k’are cin abincin,k’wanciya yayi a cinyarta suka bud’e sabon shafin love.
Ameera tana wasa da gashin kanshi tace…”yayana ka manta maganan Alhaji ne?”
“Wanne magana kenan?” Ya tambaya yana b’ata fuska kaman mai tunani.
Dariya tayi tana ture kanshi akan cinyarta tace…”kasan abinda nufi tashi ka tafi office “.
Tashi yayi ya zauna suna facing juna ya rik’o fuskanta da hannayen shi yace…” Kora ta kike ko Babyna?”
Zaro ido tayi tana kallon shi tace…” Na isa in kore ka…..”bata samu daman k’arasa maganan ba sakamakon had’a bakinshi da nata da yayi.
Sun jima a haka har yana k’okarin zarcewa Ameera ta k’wace kanta da k’yar tace…” Ka manta a gidanku muke?in Hajiya ta shigo ta same mu a haka fa?”
Yana gyara riganshi yace…” Ni nasan ba wanda zai shigo nan koda k’wana zamuyi a cikin d’akin nan”.
Rau-rau tayi da ido cikin shagwab’a tace…” Yayana ka manta meya kawo mu nan ko sai kasa Hajiya ta koremu”.
” hmmm wai ke wayo ko?gashi daga zuwa gidan Hajiya kin warke”.
Ajiyan zuciya tayi tana kallon gefe tace…” Yayana ina su Aunty dash Fa’iza?”
Had’a rai yayi kaman wanda aka gayawa sak’on mutuwa yace…” Muna zaune lafiya shine kike son b’ata min rai ko?”
Matsowa tayi ta d’ora kanta akan kafad’an shi tace…”ba haka nake nufi ba kayi hak’uri dan Allah”.
Rungomota yayi ta gefe ya fara magana…”ki yafe min Ameera akan abubuwa da suke faruwa a gida bansan me yake faruwa dani ba musamman in a gaban Lateefa ne sai in rasa ina kaina yake ga kuma wani shakkarta da nake ji ko kallonki bazan iya yi aganta ba,wannan abu yana matuk’ar damuna.ina son in kika k’ira Umma tazo ki fad’a mata su taya mu da addu’a nima zan fad’awa su Hajiya”.
Hawaye na sauka a kan fuskarta tace…”abu d’aya muke fuskanta yayana Umma tana zuwa zan fad’a mata ta gayawa Abba ya taimaka mana da addu’oi”.
Suna cikin magana Ya Sa’ad ya shigo yana yiwa Al’ameen tsiya wai Baban twins.
Shiko sai dariya yake yana amsawa da Allah yasa ya fad’a a bakin mala’iku.
Bai jima ba ya duba Ameera tare kad’a kan Al’ameen suka fita tare.
Bayan tafiyansu ne Ameera tayi dialling number Fateema,bai dad’e yana ringing ba ta d’aga tare da tambayan waye
“Ke dallah Teema nice fa” Ameera ta amsa mata a d’ayan b’angaren.
Ihu Fateema tayi cikin murna tace…” Sisto kece wayyo I missed u ina wayar ki take kika kirani da wannan?”.
Dariya Ameera tayi tace..” Ke kar ki cika min kunne,wayar Al’ameen ce. meya hanaki zuwa in kinyi missing d’ina da gaske?kuma ko a waya in ban kira ki ba,ba kya kirana”.
Marairaice murya Fateema tayi tana… ” ya kike magana kaman baki san halin Abba ba?yanzu abin nashi ya kara gaba dan cewa yayi in muna yawan zuwa gidanki mutane zasu ce mun zuba k’afa a gidanki sabida k’wad’ayi munga mijiki mai kud’i,shiyasa baki ganni ba “.
” toh shikenan ki bawa Umma wayan ” .
Fita tayi zuwa tsakar gida inda Umma take zaune tana gyara gyad’an miya,mik’a mata wayan tayi tace Ameera ce ta k’ira.
Karb’a Umma tayi bayan sun gaisa Ameera take fad’a mata abinda ya faru, nan tayi mata Allah ya sauwake tare da alkawarin zasu zo gobe su dubata ita da Fateema.