UKUBAR KISHIYATA Page 31 to 40

Dawowa yayi ya k’ara k’amk’ame Ameera yana mata godiya tare da kissing d’inta ko ta ina.
Da sud’in goshi Ameera ta samu ta kora shi massalaci dan har an tada iqama lokacin.
Number Fateema tayi dialling,a lokacin Umma ta shigo tashinta yin sallah.
Ido ta zaro tana kallon Umma tace…” Umma Ameera ce fa”.
“Ameera kuma da asuban nan,lafiya kuwa?”Umma ta tambaya da damuwa k’arara akan fuskarta.
” wallahi bansani ba nima”ta amsa itama cikin damuwa.
“Yi maza ki d’auka inji ko lafiya “.
Fateema tana d’agawa tace…” Aunty lafiya kuwa?”
“Lafiya lau” Ameera ta bata amsa sannan ta cigaba …”ina Umma?”
“Gata nan,ko in bata wayan?”ta tambaya.
Amsawa tayi da a bata d’in.
Mik’awa Umma tayi tace” ke take nema”.
Karb’a Umma tayi tasa a kunnenta tace…” Ameera lafiya kira da asuban nan?”
Gaisheta ta farayi,Umma ta amsa cikin kotsawa dan ita ba gaisuwarce a gabanta dalilin k’iran take son ji.
“Umma in kinyi sallah Ku taho yanzu”.
A rikice Umma tace…” Inzo yanzu lafiya?”
A kunyace tace… ” Umma ban iya yanke cibi bane kuma….kuma…”sai tayi shiru.
A take damuwar kan fuskarta ya koma fara’a tace…” Masha Allah!! tun yaushe kika haihu?”
Murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba .
Umma tace..” Toh gamu nan zuwa amma kamin zuwan Mu ki samu towel ko zani ki lullub’e su saboda iska”.
“To Umma sai kun iso” nan sukayi sallama ta ajiye wayan.
Umma ta juyo tana kallon Fateema da take dariya alamun taji zancen ba sai an mata k’arin bayani ba.
Had’a rai Umma tayi tace…”ba washe baki zaki tsaya yiba,yi maza ki yi sallah Mu tafi”.
Da gudu Fateema ta d’auki buta tayi bayi.
Al’ameen yana idar da sallah ya dawo wajan ‘ya’yanshi ya saka su a gaba yana kallo.
Saida tace mishi Umma da Fateema suna hanyan sannan ya hak’ura ya tafi part d’inshi.
Ya fita bai jima ba su Umma suka iso.
Umma ganin jikoki har 2 a lokaci 1 yasa ta kasa rufe baki sai sannu take ta hero mata.
Yanke musu cibi Umma tayi tare da musu wanka ta nannad’esu cikin d’an k’walin Ameera kasancewar ko wando ba’a saya ba.
Itama mai jego Umma ta had’a mata ruwa mai zafi sosai tayi mata wanka tayi fes da ita kaman ba ita ta haiho yara 2 nan ba.
Fateema kasa ajiye su tayi, tana rungume dasu saii jijjigasu take.
Suna zaune suna hira Rabi ta shigo dan dubata.
Turus tayi tana kallon su cike da al’ajabi tace…” Ikon Allah mu da muke cikin gidan ma bamu san anyi haihuwa ba,har kuda kuke nesa kunji kun iso?”
Umma ta dubi Ameera tace…” Dama ‘yan gidan naku basu san kin haihu ba?”
Girgiza kai tayi tare da sadda kai k’asa tana murmushi.
Ladi tana k’arasowa ciki tace..” Da mun sani ai anan zaki same mu Hajiya”.
Hannu tasa ta karb’i d’an dake hannun Fateema tana kokarin zama ta hango wani jaririn akan gado.
Fara’arta ne ya k’aru tace…” Dama wai ‘yan biyu ne?”
Dariya Umma tayi tace…” Wancan kishiya ce shiyasa kika ganta a yashe”.
Dariya suka k’washe dashi dukkansu,Rabi tace..” Ungo mai gidanki dan ni k’awata zan d’auka”
Nan ma dariyan suka saka.
Saida suka tab’a hira mai cike da bark’wanci sannan Rabi ta fita zuwa kitchen dan had’owa mai jego da bakinta abin kari ta kawo musu sannan ta fara had’a na masu gidan
Al’ameen tunda ya koma part d’inshi ya kasa zaune balle tsaye sai zagaye d’akin yake yana ta buga waya yana fad’awa ‘yan uwa da abokan arziki.
Jinshi yake kaman anyi mishi albishir da gidan aljanna.
Sallahn nafila ya rinka jerowa yana mik’a godiyarshi ga Allah na nuna mishi wannan babban rana a rayuwarshi.
Wanka yayi ya shirya dan tafiya office.
Lateefa yau bata samu baccin safe ba dan ta k’wana da maganan da sukayi da Aina’u a ranta.
Tana zuwa parlour taga kan dinning wayan ba komai.
Bud’e murya tayi ta fara k’walawa Rabi k’ira.
Da sauri Rabi ta iso gabanta ta zube a k’asa tace…” Gani Hajiya”.
“Wani irin rashin mutunci ne yasa har yanzu baki gama breakfast ba?” Ta tambaya tana harararta.
Rabi kai na kasa tace…” Kiyi hak’uri Hajiya gidan ne da baki shiyasa”.
“Baki,wani irin baki kuma ya ban gansu ba?”
“Suna can sashin Amarya” ta bata amsa.
Zuciyarta ne ya buga da karfi can kuma wata zuciyar tace…”ko Allah ya takaita mata wahala ta shek’a cikin dare.
Atake taji wani dad’i ya ziyarci zuciyarta,tana murmushi tace…”meye ya faru a part d’in nata?”
” *HAIHUWA* tayi Hajiya”Rabi ta bata amsa.
Share this
[ad_2]