UKUBAR KISHIYATA 1-END

UKUBAR KISHIYATA Page 31 to 40

Kunya maganar shi ta karshe ya bata ta rufe idonta da hannu tana dariya,cakulkuli ya fara mata shima yana taya ta dariyan.

Saida suka gama wasannin su,sannan ta zuba musu abincin suka fara ci.sai zuba yajin daddawa da Hajiya ta aiko mata take tana ci har tana lumshe ido.

“Kasa yajin kaji yafi dad’i wallahi” tace tana k’ara zubawa a gabanta.

Girgiza kai yayi yana…” Um-um ci kayanki da alamu me kada’i Hajiya ta aikowa”.

A ranan ma ba bai bar gidan ba saida Hajiya ta kora sannan ya tafi gida badan ranshi yaso ba.

Da washe gari misalin sha biyun rana Umma da Fateema suka iso gidansu Al’ameen duba Ameera.

Albarkacin hutu na k’wana 2 da tasamu a gidan Hajiya yasa tayi d’an dama-dama,raman da tayi shi kuma sun danganta shi da zazzabin da take.dan haka Umma bata kawo komai a ranta ba.

Hannu bibbiyu Hajiya ta sauke su,nan da nan Altine ta cika gabansu da kayan sanyi dana marmari.

Ameera dad’i kaman ya kashe ta yau taga Ummarta.

Bayan sun gaisa Ameera taja hannun Fatima zuwa d’akinta dan su d’an taba hira,suka bar Umma tare da Hajiya suna hira 

Haka baje suna yi can Fateema tace..” Naji jiya kina complain akan zuwa gidanki Wallahi Ameera kullum ina son zuwa amma Umma da Abba suke hanani wai gaki da abokiyar zama kuma mutane zasu ce Dan kin auri mai kud’i shiyasa muka zuba k’afa gidanki tunda muna jinki a ways aiya wadatar”.

“Ni dai tunda ita Umma tunda ita ba zuwa take ba ai ya kamata ke kina zuwa koda sau 1 a wata ne,amma zanyiwa Umma magana ana barinki”.

Cikin jin dad’i Fateema tace…” Good sister”.

Ameera tunda suka shigo d’akin take yunkurin fad’awa Fateema abinda yake cinta a rai amma ta kasa daga tayi niyya sai taji bakinta yayi nauyi,hak’ura tayi suka cigaba da hiransu.

Bayan sallahn azahar Umma ta shigo d’akin Ameera su d’an zanta kamin su tafi,nan ma Ameera tayi-tayi ta kasa fad’awa Ummanta komai tana ji tana gani sukayi mata sallama suka tafi.

Kuka tayi sosai bayan tafiyansu har saida taji kanta yana ciwo kaman ya rabe 2 sannan ta rarrashi kanta tayi shiru.

Tana magana cinkin ranta.. Wannan wani irin rayuwa ce ace ke da gidan mijinki ki koma tamkar baiwa?ita da za’a shawarceta sai tayi zamanta an an yafi mata zama a can,nan Hajiya tana kula da ita kaman k’wai ga uwa uba samun kulawan mijinta da take samu a koda yaushe sab’anin gidanta da ko ganinahi batayi sai dai ya saci k’afa yazo ya dubata tsakiyar dare.

K’iran sallahn la’asar da taji anayi yasa ta mik’e ta fad’a bathroom tayi wanka tare da d’auro alwala.

Saida ta tsaya ta d’an tsara make up dan bata son Al’ameen ya fahimci halin da take ciki.

Ta idar da sallahn la’asar amma bata tashi akan pray mat d’in ba tana zaune tana tunani Al’ameen yayi sallama ya shigo.

Suna had’a ido suka sakarwa juna murmushi.

” ya jikin Babyna?”ya tambaya a lokacin da yake zama a bakin gadon yana facing d’inta.

“Alhamdullilah da sauki ” ta amsa mishi lokacin da take zama kusa dashi,” ya aiki zance koya office zance?” 

” huuh all d same ba sauki dan yanzuma gudowa nayi saboda aiki ya min yawa”.

Haka rayuwar Ameera tayi ta gudana a gidan Hajiya dan yau satin ta d’aya da zuwa taji sauki sosai kuma ta murmure kaman ba ita ba .

Bayan sallahn la’asar as usual Al’ameen ya dawo daga office suna zaune suna hiransu Hajiya ta aiko tana k’iransu.

Ba b’ata lokaci suka iske ta a parlour tana zaman jiransu,waje suka samu suka zauna.

Hajiya ta tattaro hankalinta gare su kana tace…” Ameenu ina son yau d’in nan Ameera ta koma gida tunda taji sauki saboda bana son Lateefa ta fahimci abinda yake faruwa”.

Kirjin Ameera ne ya buga da karfin gaske jin furucin Hajiya, ta saci kallon Al’ameen taga yayi k’asa da yana son sanar mata halin da suke ciki shima ya kasa cewa komai.

Hajiya ta juyo ga Ameera tace…” Ina son ki kula da kanki sosai in kin koma gida,kada ki kuskura kiyi sakacin da zata gane cewa juna 2 gare ki,ina son ki yawaita saka Mayan hijabai saboda wasu dalilai.kin fahimce ni ko? ”

Kasa motsa labb’anta tayi saboda nauyin da suka mata dan haka da kai ta amsa mata.

Al’ameen shima kasa magana yayi,tace…” Kai ka tafi yanzu anjima da daddare zan kawo ta da kaina”.

Amsawa yayi ya tashi jiki a mace ya koma d’akin Ameera dan d’auko hulan da car keyn shi.

Ameera bata motsa daga inda take ba Hajiya tace…” Tashi kije ki fara had’a kayanki kamin lokaci yayi”.

Mik’ewa tayi sum-sum kaman wacce k’wai ya fashewa a ciki tabi bayan shi.

Hajiya taso ta fahimci wani abu amma ganin basuyi mata bayanin komai ba yasa ta kawar da zargin da yake ranta.

Pls masu korafi kuyi hakuri kubi novel din a sannu zaku gane wani sako name son isarwa.

[3/26, 7:05 PM] Nabeelah Shu’aib: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀

*~UKUBAR KISHIYATA

????????????????????????

(Its all about love and betrayal)

Story by *~UMMEE YUSUF~*

(Maman Yusuf)

*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*

*~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*

*part thirty two*

Yana zaune a bakin gado yasa hannayen shi duka biyu ya rike kanshi dasu yana kallon k’asa.

Bud’e k’ofan da Ameera tayi shiya dawo dashi hayyacin shi daga duniyar tunani da ya fad’a,suna had’a ido kowannensu ya kakalo murmushi yake na son kawar da damuwa ga junansu.

Tsayawa tayi a bakin k’ofa ta hard’e hannayenta a kirji tace…” Ya naga ka zauna bayan kuma tafiya ya kamata kayi?”

Da hannu ya mata alama tazo,zuwa tayi a hankali ta zauna a gefen shi,kamo hannayenta tayi duka 2 ya rike cikin nashi yana kallonta da idanuwansa da suka rine da fari zuwa ja yace…” Ameera bana son komawarki gidan can nafi son ki zauna a nan ko in saya miki gidanki daban yanda zaki zauna cikin k’wanciyar hankali har Allah ya sauke ki lafiya,I tried to tell Hajiya amma bansan meyasa ba na kasa fad’a mata komai ” ya karasa maganan cikin matukar damuwa.

Murmushi kwance a kan fuskanta take dubanshi tace…” Karka damu yayana tunda Hajiya tace in koma zan koma mu zauna nasan nan da d’an lokaci komai zai daidaita”.

Har yanzu fuska ba fara’a yake kallonta ya fara magana…”gaskiya na riga na yanke hukunci baza ki koma gidan nan ba “.

Cikin muryan rarrashi da k’wantar da murya tace…” Kayi hak’uri in koma saboda kada Hajiya taga kaman mun tsaba umarninta,beside na fad’awa Umma na tabbatar zata taya mu da addu’a “haka tacigaba da tausan da kalamai da tasan zai k’wantar mishi da hankali har saida taga ta sama mishi natsuwa tare da danne nata damuwan,

ko kad’an bata yarda yaga wani abu a fuskan ta ba illah murmushi dake tashi a kyakkyawar fuskarta

Bayan fitarsa ta kama hada kayanta tana mai zubar da hawaye saboda tausayin kanta da Kanta take ji, dama ya ta kare kuma bare ace lateefa taji labarin juna biyu gareta? girgiza kai tayi ta cigaba da had’a duk wani abu nata.

Bayan sallahn isha’i Hajiya tasa ta a gaba suka kama hanyan gidanta zuciyarta sai dukan 3-3 yaje,a mota Hajiya sai k’ara jaddada mata ta kula da kanta har suka isa gidan .

A parlour suka iske Al’ameen da Lateefa suna kallo,hannu 2-2 Lateefa ta karbe su harda rungume Ameera a gaban Hajiya wai tayi missing d’inta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button