UKUBAR KISHIYATA Page 31 to 40

Hajiya bata bar gidan ba saida ta had’asu tayi musu nasiha mai ratsa jiki wanda Lateefa yake shiga 1 kunne ya fita ta 1.
Bata wani dad’e ba a gidan ta mik’e dan ta koma gida, suma duk suka mik’e dan yi mata rakiya ” koma ki huta Ameera keda baki gama warwarewa ba” Hajiya tace mata.
Ba tayi gardama ba ta koma ciki dama tana tsoron zama cikinsu bata san wani rashin mutuncin zasuyi mata ba bayan tafiyan Hajiyan.
Lateefa kuma ta k’asa take hararar Hajiya a zuciyarta tana zanyi maganinku duka.
Direct part d’inta ta wuce cikin sauri ta bud’e k’ofa ta shiga ta mayar ta rufe tare da jingina a jikin k’ofan,wasu zafafan hawaye ne suka gangaro mata data tuna yanzu wani hali zata shiga.
A nan ta zube tasha kukanta na tausayin kanta da kanta ta more da kyar ta rarrashi kanta ta mik’e zuwa cikin bedroom d’inta.
Wanka kawai tayi ta haye gadonta ta kwanta zuciyarta a cunkuse.
Da washe gari da sassafe ta tashi ta nufi kitchen kaman yanda ta saba,dama Lateefa tun cikin dare ta sanar da masu aiki dawowar Ameera kuma ta umarce su da su sakar mata aiyukan gidan.
Duk da Lateefa ta hana su bai hana Rabi fitowa dan taya taba saboda har cikin zuciyarsu suna tausaya mata sosai.
A zaune ta same ta a cikin kitchen d’in tana firen dankali, Ameera da saurinta ta karaso cikin kitchen d’in tana cewa “haba Rabi ba kya gudun laifina ya shafe ki?”
D’an tsagaita firan Rabi tayi ta d’ago tana kallonta fuskarta cike da fara’a tace…” nasan suna bacci a wannan lokacin balle inji tsorin zasu fito su same ni anan,dan haka ki k’wantar da hankali ki ba abinda zai faru sai alkhairi”.
K’arasa shigowa ciki tayi tana jin hawaye na taruwa a idonta,kusa da ita tazo ta durkusa tace…” Nagode Rabi da taimakon da kike min a gidan nan,dame zan taimaka miki yanzu dan mugama da wuri?”
” d’auko d’anyan kifi a friji ki wanke min kamin in gama firan”tace tana cigaba da aikinta.
Murmushi kawai Ameera tayi ta juya zuwa deep freezer ta bud’e ta d’ebo su yanda tasan zasu ishi gidan .
Wanke su ta farayi a sink d’in cikin kitchen,k’arnin kifin ne ya fara damunta sosai har ya haddasa mata tashin zuciya lokaci d’aya,duk dauriyanta amma saida amai ya kwace mata ba shiri.
Rabi dake firan dankali bata san lokacin da tayi cilli da wukan hannunta ba tazo da gudu ta riketa tana yi mata sannu.
Da’kyar ta samu ya tsaya,wanke fuskanta tayi tare da kuskure bakinta tana maida numfashin wahala.
Akan kujera Rabi ta zaunar da ita tace…” Zauna anan bari ni zan karasa aikin”.
Jingina tayi da kujeran ta lumshe ido saboda yanda take jin cikin ta yana wani irin murd’a.
Lemun tsami Rabi ta d’auko mata a frdge ta bata tace…”ki sha wannan zaki ji saukin tashin zuciyan.
Bata musa ba tasa hannu ta karba ta fara shan lemun.
Rabi kuwa duk Rabin hankakinta yana kanta,tana aikinta kuma ta na juyowa tana kallonta fuskarta d’auke da murmushi sakamakon ta riga ta gane cutar Ameera. Dan Rabi ba karamar mace bace a kalla zatayi 37 years a duniya.
Cikin ikon Allah Ameera taji saukin tashin zuciyan amma hakan baisa ta daina shan lemun ba saboda dad’i yayi mata sosai dan kwata-kwata bata jin tsamin saima wani zaki-zaki da taji lemun yana yi mata.
Suna aikinsu suna hira sai gashi sun gama cikin k’ank’anin lokaci.
Bayan sun zuzzuba a warmers Rabi tace…” Toh bari in tafi kar su shigo”.
Godiya Ameera tayi mata sannan ta kama hanyan fita, har ta kai bakin k’ofa ta juyo fuskanta d’auke da fara’a tace…” Hajiya ina taya ki Murna “.
Da wuri Ameera ta waigo tana dubanta cike da fargaban me zata ce mata ta tako a hankali zuwa gabanta tace…” Murnan meye Rabi kike tayani dashi?”
Rabi bata daina murmushi ba tace…” Hajiya ga dukan alamu juna 2gareki”.
Zuciyarta ne ya buga da karfi,ashe dai ana ganewa da ake cewa ta boye?
Baki na rawa tace…”yanzu kowa ya gani zai gane?”
Rabi ta fahimci damuwar da take ciki dan tace… ” ki k’wantar da hankali ki ba mai ganewa a gidan nan tunda ba wacce ta tab’a haihuwa a cikin su balle su lura da canzawarki,ni kaina amai da kika yi a gabana shiya tabbatar min da hakan sai dai ina baki shawaran ki guji Inda suke ki nisance su sosai dukda dama ba wata alaka bace tsakaninku kinji?Allah zai kare ki daga sharrinsu kuma Allah ya sauke ki lafiya”.
Nauyayyen ajiyan zuciya ta sauke tare da sakin fuskarta tace…”nagode Rabi Allah ya saka da alkhairi”.
Komawa tayi cikin kitchen dan k’arasa sauran aikin ita kuma Rabi cikin sauri ta koma part d’insu na masu aiki.
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
????♀????♀????♀????♀????♀????♀
*~UKUBAR KISHIYATA
????????????????????????
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*
*~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*
*part thirty three*
Kan dinning ta shirya musu kayan breakfast d’in sannan ta koma d’aki duk abin duniya ya isheta saboda yau tun tashinta bata sha mutumin taba wato fresh milk.
Duk da tasan fridge d’inta babu komai a ciki amma hakan bai hanata bud’ewa ba ko zata samu wani abun,ga mamakinta fridge d’in cike yake da fresh milk harda ice cream.
“Allah sarki Yayana” tace lokacin da ta d’auki roba 1 ta koma kan kujera ta zauna tana sha,tana jinjina mishi tasan shine kad’ai da wannan aikin kila dare yabi ya tanada mata abinda yasan tana matuk’ar bukata.
Tana gama sha ta d’auko burmemen hijabinta dogo har k’asa amma mai hannu ta saka ta fito parlour.
Suna kan table suna breakfast ta same su,durkusawa tayi har k’asa ta gaishe su.
A wulakance Lateefa ta amsa,Al’ameen ko d’agowa baiyi ya kalleta ba balle tasa ran zai amsa.
A tsawace Lateefa tace…” Ke dan ubanki ban hanaki zuwa inda mijina yake ba?sai ana magana ki kama sunkuyar da kai sai kace wata mutuniyar arziki”ta karasa maganan tana harararta.
Tsum- tsum Ameera ta mik’e tayi hanyan part d’inta.
Wata tsawar ta kuma daka mata…”ke ina zaki tafi kuma bayan ban gama dake ba?ki wuce part d’insu Fa’iza ki gyara musu kamin su dawo daga sch”.
Al’ameen yana jinsu amma ko d’ago da kanshi ya kasa balle yayi yunkurin hanawa.
Part d’insu Fa’izan ta wuce ta bud’e parlour ta shiga, gani tayi duk sunyi kaca-kaca da parlourn komai a warwatse.
Cikin k’ank’anin lokaci ta kimtsa ko ina ya zama fes.
Cikin bedroom ta nufa shima da nufin kimtsata,tana bud’e k’ofan bata san lokacin da ta k’wala wata irin razanannen kara ba sakamakon abinda idonta ya gane mata.
Ihun da tayi shi ya dawo dasu cikin hayyacinsu ,a razane suka rabu da juna suka juyo suna kallonta.
Jikinta gaba 1b’ari yake,Fa’iza,Shamsiyya da wata sabuwar k’awarsu mai suna Binta ta gani tsirara akan gado suna murkususu.
Shamsiyya ta wawuro towel ta d’aura a lokacin da take saukowa daga kan gadon,ta nufo Ameera da ta kasa motsi ta sandare waje 1.
Wani gigitacen mari ta fara d’auketa dashi tana nunata da yatsa tana huci ta fara surfa mata ruwan bala’i.
Kan kace me sauran ma sunyi joining,nan suka taru suka nad’a mata na jaki.
Haniyarsu ce ta cika gidan har Lateefa taji ta iso wajan tana tambayan ko lafiya?
Shamsiyya tayi caraf tace…”Aunty ace karuwancin yarinyan nan yayi nisa kuma ta rasa inda zatayi sai gidan nan?”