UKUBAR KISHIYATA Page 31 to 40

“Ni Ku gaya min me yake faruwa nace?” Lateefa ta k’ara tambaya cike da k’osawa.
Binta ta matso gaba tace…”Aunty wanka fa muke yarinyan nan tazo tana lekamu”.
Salati Lateefa tasa tana tafa hannu ta juyo ga Ameera tasa k’afa ta hamb’areta ta fad’i k’asa.
Bata tsaya yin tunani ko la’akari da me zaisa su many an ‘yan mata shiga wanka tare ba.
Ta cigaba da bala’i…”dama kana ganin idonta zaka san tayi nisa a harkan lesbian, toh wallahi ba a gidan nan ba sai dai kije can ki nemi abokan shashancinki”.tana magana bugunta sai da sukayi mai isarsu sannan suka k’yale ta dan Kansu.
Da k’yar ta iya jan jikinta dake mata ciwo ga uwa uba mararta daya kulle ji take kaman zai balle saboda azaba.
K’wanciya tayi cikin azaba da rad’ad’i tana ta juyo kuma tana tunanin alak’arta da Fa’iza da irin abubuwa da take mata,sai yanzu ta fahimci manufarta.
Godiya ta shiga yiwa Allah da bai bata nasara a kan ta ba har tasan wacece ita,ta gwammace ta dauwama a *UKUBAR* Lateefa da ta kasance a irin wannan halin.
Haka ta cigaba zancen zuci har baccin wahala ya d’auketa.
Har bayan 12pm Lateefa bata ga gilmawar Ameera ba yasa ta k’walawa Rabi k’ira tazo gabanta ta durkusa,nan take tambayarta ko Ameera tana kitchen?
Amsa mata tayi da… ” a’a ban ganta ba Hajiya”.
Wata k’atuwar ashar Lateefa ta lailayo sannan tace…” Tab lalle yarinyan nan ta rainani in har ban gyara mata zama ba,wata rana sai taci tuwo akaina”.
Tana gama fad’an haka ta mik’e a fusace tayi part d’in Ameera, Rabi tabi ta da ido tana girgiza Kai cike da jimami.
A kan tiles ta same ta zube tana baccin wahala,ga fiskan nan ya kumbura suntum.
Ba imani balle tausayi Lateefa tasa hannu ta wanka mata lafiyyar mari kan kumburaren fuskanta.
A razane ta mik’e tana muzurai,suna had’a da Lateefa ta zube a wajan tana bata hak’uri amma hakan bai hana Lateefa zazzaga mata bala’in data k’waso ba.
Tasa kyarta tayi har kitchen d’in tana balbale ta da masifa kuma tace maza ta d’aura musu abincin rana.
Ko d’ago da kai ba tayi ta kalleta ba har ta gama ta fice.
Goge hawayen fuskarta tayi,ta fara kiniyan d’aura girgin.
Rice and stew tayi niyan girkawa dan haka duka 2 ta d’aura su lokacin d’aya,tana soya kayan miyanta da tasa kayan kamshi harda curry a ciki.
Ka min ta gama soya miyan saida tayi amai har sau 2 saboda yanda take jin curryn yana hawa mata kai.
D’an k’walin kanta ta cire ta rufe hancinta dashi,d’ayan hannunta kuma rik’e da lemun tsami tana tsotsa.
A haka ta gama musu girkin ta jera musu akan dinning sannan ta wuce part d’inta dan yin wanka.
Ruwan d’umi ta had’a ta gasa jikinta dashi,k’wanciya tayi lamo cikin ruwan tana jin dad’inshi ga mararta ma har yanzu bai daina ciwo ba.
Tana fitowa daga wankan mai kawai ta shafa tasa wata jallabiyar ta ash colour babu zancen k’walliya saboda an haramta mata shi a gidan.
Hijabi ta d’aura akan jallabiyan tayi sallahn azahar.
Tana idarwa tayi hanyan kitchen saboda wata zababbiyar yunwa da take ji,tana addu’an Allah yasa sun rage mata.
Allah ya taimake ta dan ta samu sun rage dayawa.
Sai dai kuma ba zata iya cin miyar ba saboda warin curry.
A plate ta d’ebi white rice tasa man gyad’a tare da marmasa maggi kad’an akai,albasa da attargu tasa a turmi ta d’an jajjagasu shima ta juyesu akan white rice d’inta ta zauna ci.
Sosai abincin tayi mata dad’i sakamakon sunfi shiri da abinci mai yaji yanzu dan haka taci dayawa.
Tana gamawa kuwa ta kama kiciniyar d’aura na dare,saboda tasan tana k’wanciya bacci zatayi azo ana masgarta a banza.
Bayan dawowarta daga gidan Hajiya kaman da wata 2 Fateema da ya kumbonsu suka zo mata yini kuma Allah ya taimake ta ranan Lateefa bata nan sun fita watsewarsu ita da Salees d’inta su Fa’iza ma basa nan dan haka lafiya lau suka wuni suna tafi.
A k’wana a tashi ba wuya dan yau cikin Ameera ya shiga wata na 7 kenan,amma duk gidan ba wanda ya sani in ka cire Al’ameen da Rabi.
Cikin ikon Allah cikin yabi jikinta da yake Allah ya mata baiwan diri da na Fulani dan haka su suka rike mata cikin .
Wata safiyar Wednesday Ameera tanan goge-goge a parlour,Mamarsu Lateefa tayi sallama ta shigo.
Lateefa cike da murna ta tare ta.
Ameera dak’yar ta kai k’asa ta gaisheta.
Fuska ba yabo ba fallasa ta amsa suka wuce part d’in Lateefa .
Ameera ajiye dustern hannunta tayi ta shiga kitchen dan had’owa Mamar Lateefa ruwa da abin motsa baki.
Cikin dauriya take komai sakamakon nauyi da cikin tayi mata.
Katon tray ta cika shi da drinks da snacks ta nufi part d’in Lateefa dashi.
Hirarsu suke suna k’wasan dariya kaman wasu k’awaye,Ameera tayi sallama ta shigo.
Tafiya take a hankali harta k’ataso tsakiyan parlour ta ajiye tray akan center table dake tsakiyan parlourn.
Tsiyaya juice d’in tayi a glass cup tazo gaban Maman Lateefan ta mik’a mata tare da k’ara mata sannu da zuwa.
Mik’ewa tayi da k’yar ta fice, duk akan idon Maman Lateefa ta k’asa cewa komai.
Bayan fitan Ameera ta juyo ga ‘yarta tace…”wacece wannan ko sabuwar ‘yar aiki kika samu?”
Dariya Lateefa tayi har rana rik’e ciki tace…” Mama kenan wannan Ai itace amaryar Al’ameen amma kinga yanda na maidta mai aikin gidana duk wani aikin gidan nan ita take yinsu na hana masu aiki….”
” me dallah dakata shasha”ta katse ta cikin tsawa.
Lateefa sororo tayi ta na kallon Mamanta ita kuma ta cigaba …”Ai kuwa kece mai aikinta nata dan kina gab da zama ‘far kallo a cikin gidan nan,ke da nake ganin ba wacce ta tako k’afana cikin ‘yan matan da Allah ya bani sai me Ashe kuwa ba haka bane”.
Turo bani Lateefa tayi tace… “Haba Mama keda na d’auka zaki tayani farincikin ina jiya kishiyata amma sai ki hau yi min fad’a akanta?”
Tsaki Mama tayi tace…” Baki da idone Lateefa, ba k’ya ganin abinda yake jikinta wannan kishiyar taking?”
Zaro ido tayi ta na kallon Mama tace…” Bangane ba,Mama me kika gani a jikinta?”
“Bud’e kunnenki kiji duk yanda akayi yarinyan nan ciki ne da ita”.
[3/31, 3:03 PM] Ummee Yusuf: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
????♀????♀????♀????♀????♀????♀
*~UKUBAR KISHIYATA
????????????????????????
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*
*~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*
*part thirty four*
Wata irin zabura Lateefa tayi ta mik’e tsaye tare da d’aura hannayenta duka akai tace…” Na shiga 3,dan Allah Mama da gaske kinga ciki a jikinta?”
” k’irata ki gani da idonki”Mama ta bata tabbaci.
K’wala mata k’ira ta farayi da dukkan karfinta.
A tsorace Ameera ta shigo ta zube a k’asa tace…” Gani
Aun…”
Katse ta tayi cike da karaji tace…” Mik’e daga tsugunen nan munafuka”.
Yunkura tayi ta mik’e tsaye da k’yarta tana kallon yanda duk ta hargitse.
Wawuro hijabinta Lateefa tayi zata cire mata,Ameera tayi saurin rik’ewa tana…” Aunty ki hak’uri,me nayi ne?”
Lateefa bata ma jin me take cewa babban burinta ta cire wannan hijabin da bata rabuwa dashi dan ta tabbatar da maganan Mamanta.
Da karfin tsiya ta samu nasaran cire hijabin, ai kuwa cikin tagani ya d’an fito kaman an kifa k’warya.