UKUBAR KISHIYATA 1-END

UKUBAR KISHIYATA Page 31 to 40

Lateefa bata san lokacin da hijabin ya sub’uce ya fad’i a hannunta ba.

Mama tace…” Yanzu kinga zahiri ko?”

Wani mahaukacin mari ta d’auketa dashi wanda yasa har ta kifa a k’asa.

Binta tayi ta cigaba da dukanta tana taka cikin da k’afa tana sumbatu kala-kala kaman wata sabuwar kamu kana ganinta kasan bata cikin hayyacinta.

Mama da k’yar ta samu nasaran janye ta gefe tare da zaunar da ita akan kujera tana ta haki.

Ameera kuwa tuni ta fice daga parlour da rarrafe dan tsira da ranta.

Mama ta dubeta taga har yanzu bata dawo hayyacinta ba sai huci take,kamo hannunta tayi ta girgizata tace…”ke ki nutsu ki dawo hayyacinki kiji abinda zance miki,ba haka ake yi ba in kin kashe ‘yar mutane fa?da sannu ake bin komai duk da kema kinyi sake sosai a zamanta a gidan nan da haka bata faru ba.karki damu tunda kina dani yanzu zan baki shawaran yanda cikin zai bare cikin sauki”.

Sai a lokacin ta samu daman sauk’e nauyayyen ajiyar zuciya tare da gyara zama tace…”ina jinki Mamana ya za’ayi?”

“Aiki zaki k’ara mata yafi na yanzu,dan ‘yan aikin nan da take ba masu wuya bane.abinda nake so sake shine duk kayan ku na wanki da guga ita zaku tarawa,ke harda sharan wannan tafkeken gidan naku ciki da wake karki tausaya mata kiyi haka zuwa sati 1,in baki ga wani cigaba ba kimin waya balle nasan za’ayi nasara saboda da alamu cikin k’arami ne”.

Rungumeta Lateefa tayi tana murna da godiya mama tace…” Haba sai kace baki sanni ba?ba zamuyi sake gidan hutun ya sub’uce mana ba”.

Nan suka cigaba da hirarsu wanda kusan gaba d’aya akan yanda zata Lateefa zata musgunawa Ameera ne.

Sai bayan a zahar tayi shirin komawa gida bayan Lateefa tayi mata goma na arziki ta rakota har parking lot.nan take fad’an har zata koma bataga su Fa’iza ba.

Nan Lateefa take shaida mata sun tafi rabon katin auren k’warsu Binta wanda za’ayi nan da 2weeks.

Sak’on a gaishe su ta bari wajan Lateefa tashiga mota driver ya maidata Gida .

Komawa cikin gida tayi tana ayyana sabon rashin mutuncin da zatayiwa Ameera.

Kayan sawanta dana Al’ameen sun kai kusan set 30 ta fito dasu tana kwalla mata k’ira.

Tana jan k’afa ta fito daga part d’inta zuwa cikin parlour inda Lateefa take jiranta ,tana shirin tsunguna taji an watso mata fuska.

“K’washe kayan nan kije ki wanke minsu tas sannan ki jira su bushe ki goge su duka a yau and bana son machine wash dan yana b’ata min kaya dan haka use ur hands and wash them” tace tana watson matso mugun kallo dan bata ki ace ta shak’eta su mutu ita abinda yake cikinta ba.

Tsungunawa tayi da k’yar tana tattara kayan saboda tunda Lateefa ta tattaka mata ciki take cin mararta yana mata wani irin zogi.

Haka ta fita dasu can compound d’in gidan zuwa bakin tap dan wanke su.

Mai wankin gidan yana ganinta ya taso da gudunshi da niyan karb’a amma ta dakatar dashi tace ya barsu ita zata wanke su da kanta.

Jikin shine yayi matuk’ar sanyi dan haka ya rasa bakin magana yaja gefe yana kallonta harta kai bakin tap tana shirin fara wankin da hannu kaman yanda aka umarceta .

Wajen maigadi yaje yana maida mishi zancen.

Girgiza kai yayi cike da jimami yace… “Yarinya ‘yar k’arama da ita amma matan ba d’igon imani bata dashi take azabtar da ‘yar mutane”.

Driver yace…” Nifa laifin maigaidan nake gani tunda shi ya kamata ya tsawatar mata amma ya kasa”.

Mai gadi ya girgiza kai yace…” Kai dai bari wannan lamari sai Allah tunda yasha sayo mata abubuwa yana bani ajiyarsu sai can cikin dare zai dawo ya karba”.

“Hakane kam wannan abu sai Allah” inji mai wankin.

Ameera tana can tana tikan wankin tana zubar da hawaye tana kuma nadaman kin amicewa da shawaran Al’ameen na bata da yace zai saya mata gidanta daban taki gashi tunda ta dawo abin k’ara gaba yake.

Dan mugunta irin na Lateefa wasu kayan ma a wanke suke ta had’a dasu.

Haka ta gama ta shanyasu gaba d’aya akan igiyan shanya,sannan ta koma cikin gidan tace tagama.

Harara tabita dashi idon nan kaman zasu fad’o k’asa tace…”wallahi inna Cuba kayan nan naga jik’a-jik’a kika min,hmmm..” Yatsunta 2 ta had’a ta Mirza sukayi k’ara kana tacigaba” kema kinsan sauran ba said na fad’a miki ba tashi ki bani waje”.

Harta ta tashi zata tafi tace…”yauwa sak’wara nake son ki mana duka gidan hard a masu aikin gidan nan”.

Kasa magana tayi kawai kitchen d’in ta wuce kai tsaye ta d’auko manyan doya guda 3 ta kama fira, bayanta mararta duk sun rike sai azaba take ji,ga yunwa da take ji dan rabonta da abinci tun safe.

A haka ta had’a musu lafiyayyar miyan egusi da yaji ganyan ogu da cry fish ga naman rago,gidan sai kamshi yake.

Bari d’aya kuma doyanta data d’aura da d’an gishiri ya nuna.

Turmi da tab’aryata ta d’auko ta fara kirb’awa,tanayi tana tsayawa sakamakon azaba da cikinta da bayanta ke mata.

Haka Rabi ta shigo ta sameta ta Mike sharkaf da gumi.

Da sauri Rabi ta k’arasa tana…” Hajiya kawo in kib’a miki amma wannan rashin imanin yayi yawa ,Allah ya saka miki Hajiya wallahi koba dad’e koba jima Allah ba zai barta ba karshenta ba zai tab’a k’yau ba”.

Zubewa tayi a k’asa tana juyi akan tiles d’in kitchen, Rabi tana kirb’awa amma hankalinta gaba d’aya yana kan Ameera sai hawaye take tana mata sannu .

Cikin ikon Allah kamin Rabi ta gama taji ciwon ya lafa,dan haka tazo tasa hannu ta fara tayata yin malmala suna zubawa a warmers.

Rabi tana hanata amma taki tace taji sauki shiysa.

Bayan sun kammala ta koma wajan kayan dan gogesu ta tatar da mai wankinsu yana aikin gogr mata su.

Nan ta nemi ya bar mata ta k’arasa yace bakomai taje bakomai zai k’arasa mata.

Bata koma cikin gida ba gudun kada Lateefa ta ganta ta shiga 3,dan haka can garden d’in gidan ta wuce ta samu waje ta zauna.

Sai bayan 9 ya gama gugan ta k’waso kayan ta shigo cikin gida, bakowa a parlor,wucewa tayi dasu d’akinta ta ajiye da safe ta bata.

Wanka ta farayi sannan tayi sallahn isha’i,da rarrafe ta k’arasa kan gadonta ta k’wanta tana maida numfashi.

Ko 30 mins batayi da k’wanciya ba taji cikinta ya fara wani irin murdawa na yunwa.

Ba shiri ta tashi ta nufi kitchen dan samawa cikinta wani abu.

Duk dube-dubenta bata samu komai ba a kitchen d’in,tana son d’aura ko indomie ne amma tana tsoron a kamata a kitchen a nad’a mata na jaki saboda tasan wannan shirin Lateefa ne dan in bata son taci abinci a gidan Sai tasa a k’washe abincin akai can layi ko kan soak away azubar.

Dawowa tayi d’akinta ta k’wanta,bata jima da k’wanciya ba taji motsin mutum a parlour ta.

Bata motsa ba daga kwacenta saboda tasan mutum 1 ne mai shigo mata d’aki a irin wannan lokaci.

Yanda ya ganta ya matuk’ar razana shi,da sauri ya k’araso ya hau kan gadon tare da sa hannu ya d’agota yana tambayarta meya sameta.

Da hannu ta nuna mishi cikinta da bayanta.

Kwantar da ita yayi ya fita da sauri zuwa parlour,ya samo mata ibomol cikin first aid box ya dawo ya same ta kaman yanda ya barta.

Tambayanta yayi ko taci abinci?ta amsa mishi da bata ci ba.

Fita ya k’arayi zuwa kaman 15mins Sai gashi ya dawo da plate a hannun shi cike da indomie sai tururi yake da alamu yanzu ya dafa shi,d’ayan hannunshi kuma rik’e da wani k’aton shopping bag ya ajiye a k’asa ya hau gadon.

D’agota ya jinginar da ita a jikinshi sannan ya fara bata abincin abaki,nan da nan ko ta cinye shi tas..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button