UKUBAR KISHIYATA Page 31 to 40

Ledan da ya shigo dashi ya b’ude,cake ne da sauran snacks zallah a ciki,shima ta hau ci hannu baka hannu k’warya,kallonta yake cike da tausayi saboda mutum yana ganin yanda take abinci zaka san yunwa ya gama cinye ta.saida taci mai isarta sannan ya bata maganin tasha.
K’wantar da ita yayi yana lapping d’inta kaman ‘yar jinjira har baccin mai dad’i ya k’washeta.
Shi bai bar d’akin ba saida yaga baccinta yayi nisa sannan ya fita ba dan yaso ba ya ayyana abubuwa a ranshi.
[3/31, 11:33 PM] Ummee Yusuf: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
????♀????♀????♀????♀????♀????♀
*~UKUBAR KISHIYATA~*
????????????????????????
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*
*~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
*part thirty five*
Washe gari bata farka ba sai wajan karfe shida da rabi na safe.
Garau ta tashi ba ciwon mara dana bayan da take ji jiya,wanka tayi tare da alwala tayi sallah sannan ta fito aika-aikacenta da yanzu ya zame mata jiki.
Rabi ta iske a kitchen tana girki harta kusa kammalawa.
Da murmushinta ta k’araso tana mata sannu da aiki.
Bayan sun gsisa Rabi take tambayarta ya jikinta?
“Da sauki wallahi dan yau na tashi bana jin ciwon komai” tace tana murmushi.
“Alhamdulillah Allah ya k’ara lafiya ya raba Ku lafiya” inji Rabi.
Ta amsa da “Ameen”.
Hannu tasa suka k’arasa aikin tare suna hira abinsu,dan yanzu Rabi ita zame mata tamkar k’awa.
Da ita kad’ai zata zauna tayi hira cikin k’wanciyar hankali.
Yau sati 1 kenan Lateefa take gallazawa Ameera dan cikin jikinta ya b’are amma shiru ba labari,sai ciwon mara da baya da kusan suka zame mata jiki amma tana shan ibomol da Al’ameen ya ajiye mata su a d’aki harda paracetamol sai taji sauki.
Ganin ba canji yasa Lateefa tayi shawaran k’iran Mama dan su canza shawara.
Can cikin bedroom d’inta ta shiga sannan ta k’irata,bayan sun gaisa take fad’a mata cikin yana nan bai zub’e ba.
” kada ki tada hankalinki ki turo min d’aya daga cikin k’annenki tazo in bata wani magani dana tanadar miki, da zarar ta sha cikin nan ba zai k’wana a jikinta ba”Mama tace mata cikin rarrashi.
Dariya tayi na jin dad’i tana jin ba wanda ya kaita sa’an uwa na gari.
“Yanzu zan turo Shamsiyya tazo ta karb’a”.
Mama ta katse ta da …” Yau zata zo bazaki bari sai gobe ba? Naga yanzu yamma tayi”.
“Hak’urina ya kare Mama na k’osa inga babu cikin nan ajikinta dan haka zan iya jurewa zuwa gobe ba”tace tana huci kaman wata macijiya.
Suna gama wayan tayi dialling number Shamsiyya tace tazo bedroom d’inta ta sameta.
Cikin minti biyar ta shigo tace…”gani Aunty”.
” zariya zan aike ki akwai sak’ona a wajan Mama ki karb’o min kuma pls karki k’wana duk yanda zakiyi ki dawo yau”.
Shamsiyya tace… ” toh ba zan k’wana ba saboda muma muna nan muna shiye-shiryen auren Binta”.
Lateefa tace…”oh ashe auren ya matso ko?”
“Eh saura 5 days, bari inyiwa driver magana muje mu dawo da wuri” tace tana mik’ewa.
Dakatar da ita Lateefa tayi tace…” Kije ke kad’ai ba tare da driver ba saboda sirri ne “.
” shikenan Aunty saina dawo”.tace tare da ficewa daga bedroom d’in.
Wani maganin gargajiya Mama ta bata cikin goran faro ta kawo.
Cikin tsananin murna Lateefa tasa hannu ta karb’a ta ajiye a gefenta sannan ta fara k’walawa Ameera k’ira.
Ameera tana jan k’afa ta shigo parlour saboda yanda cikin nata kullum yake k’ara girma da nauyi.
Maganin ta mik’o mata tace…” Gashi maganine shanye ki bani roban”.
“Magani kuma Aunty? Lafiyata k’alau fa” tace tana shirin mik’ewa ta bar wajan.
Murmushin mugunta tayi tace…”wato bazaki sha girma da arziki ba ko?Ku rik’e min ita in bata”.
Kamin ta rufe baki Fa’iza har ta iso inda take tana janta cike da mugunta dama yanzu ba wanda ya kaita jin haushin Ameera tunda ta kasa cimma burinta akanta.
Shamsiyya tazo tayi joining suka rirriketa,Lateefa ta taso da roban maganin a hannunta.
Cikin tashin hankali Ameera ta fara mata magiya kan taji kanta ta k’yaleta amma Lateefa ko d’igon imani babu a ranta balle tausayi burinta kawai shine taga ta b’atar da abinda yake cikinta ko hankalinta zai k’wanta.
Murmushine shimfid’e a fuskanta harta k’araso gaban Ameera tace…” Kada ki damu ‘yar k’anwata,wannan magani da kike gani zai taimaka miku sosai wajan haihuwa kinsan ina ji dake bana son ki sha wuya shiyasa kika na nemo miki maganin da kaina”.
Tana gama fad’an haka ta matse mata baki ta fara d’ura mata maganin su Fa’iza suna tayata suna dariya.
Basu k’yaleta saida taga goran ya zama empty sannan suka k’yaleta.
Gaba d’aya Ameera ta galabaita ta fita haiyacinta ido jawur take kallonsu,har yanzu basu bar mata dariyan ba.
Daddafa kujeru tayi ta mik’e da kyar tayi hanyan part d’inta tana layi,a ranta kuwa tana ayyana karshenta yazo bata cire d’aya cikin biyu maganin mutuwa ta d’ura mata.
Ba yanda zatayi sai dai taje ta jira mutuwarta.
Tana shigowa parlournta taji mskoshinta yacika da wani irin bauri da d’aci wanda ya haddasa mata tashin zuciya lokaci d’aya.
Da gudu tayi bathroom kamin ta k’arasa ta kece da amai mai tsanani kaman zata amayar da kayan cikinta.
Aman bai tsaya ba saida ta komai na cikinta ya fita sannan ya tsaya.
Shower ta sakarwa kanta sannan ta fito ta k’wanta akan gadonta tana kuka tana mik’awa Allah lamarinta a haka har baccin wahala yayi gaba da ita.
Pls manage dis.kuma masu complain akan Ameera Ku kara hakuri.
[4/1, 8:34 PM] Ummee Yusuf: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
????♀????♀????♀????♀????♀????♀
*~UKUBAR KISHIYATA
????????????????????????
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*
*~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
*part thirty six*
Lateefa tana k’wance a parlournta ajan 3 seater cike da nishad’i take danne-danne a wayarta,kana ganinta zaka san tana cikin farinciki.
Number Aina’u tayi dialling tasa a kunnenta,fuskarta cike da annuri take cira ta d’aga wayan.
“B’atan hanyan kikayi ko kuma ince sai yau kika tuna dani?” Aina’u tace bayan ta d’aga wayan.
Dariya mai cike da farinciki ta k’washe dashi tace…”Besty yau ina cikin farinciki shiyasa na kiraki ki tayani farinciki ”
” a haba! Meya faru ?bani insha mu taya juna murna”
“Hmmm Aina’u wai ashe wannan yarinyan munafurta ta take”.
Cikin sauri Aina’u ta katseta tace…” Wace yarinya kuma?”
Lateefa saida taja numafashi tace…” Wannan tsinannaiyar Ameeran nan mana ashe ciki ne da ita”.
Zumbur Aina’u ta mik’e daga zaune dafe da kirji tace…” Me kika ce Lateefa,ya akayi kikayi wannan saken har hakan ta faru?”
K’ara gyara k’wanciyarta Lateefa tayi sannan ta bata amsa…” Bar shegiyar yariyan nan b’oye cikin tayi ban tashi sani ba saida Mama tazo gidan nan ta ganta,dan munafurci kullum hijabi take jurmuk’awa…”
Da sauri Aina’u ta katseta…”yanzu wani mataki kika d’auka ko shine abin farinciki da kika k’ira ki gaya min?”
” ke dad’ina dake gajan hak’uri”Lateefa tace mata tana dariya.