UKUBAR KISHIYATA Page 31 to 40

“Uhum ina jinki,zuciyata ce take tafasa shiyasa kika ga na kasa hak’uri” Aina’u tace mata.
Lateefa saida ta k’ara dariya sannan tace…” Bazan iya k’watanta miki tashin hankali dana shiga ba a wannan lokacin,idona rufewa yayi na hauta da duka ta ko ina.da k’yar Mama ta k’wace ta,tace min ba haka make ba ta bani shawaran kara mata aiki masu wuya zuwa sati,nayi ta d’aura mata amma ba nasara shine yanzu ta aiko min da wani jiko muka d’ura mata wanda Mama ta tabbatar min ba zata k’wana dashi a jikinta ba.farinciki ne ya cika ni shiyasa na kiraki ki tayani murna”.
Dariya mai kama da shewa Aina’u tayi tace…” An gaishe da Maman Mu,sai yanzu naji hankaluna ya k’wanta,yanzu tana ina?”
“Tana can d’akinta tana fama da kanta”Lateefa ta bata amsa.
Aina’u tace…” Bari in k’ara miki wata idea nima,ki kula da takunta da zarar kinga ta fara labour sai kiyi amfani da wannan chance d’in ki k’arasata kowa ya huta.kuma ba wanda zaiyi doubting d’inki dan kowa cewa zaiyi ta mutu a wajan haihuwa”.
K’yalk’yalewa tayi da dariyan jin dad’i tace…” Gaskiya yayu Besty shiyasa nake ji dake”.
Sallama sukayi ta ajiye wayan bayan Aina’u ta k’ara mata evil ideas .
Fa’iza da Shamsiyya sun saka Binta a gaba suna ta kuka wiwi wai a dole sunyi rashin masoyiya.
Binta tazo ta rungumesu tana rarrashinsu tace”haba Ku daina bata hawayenku kusan auran nan zanyi ne Kawai ba dan ina so ba kawai saboda matsayinshi yasa zan aure shi ku tuna fa major general ne fa? kunga akwai naira da zamuyi abinda muka ga dama bayan haka kuma alakarmu tana nan ba abinda zai canza kunsan nima ba zan iya rayuwa ba ku ba dan kun zama jinin jikina”.
“Shamsiyya tace…” Are u sure?”
” off course yes”ta tabbatar musu.
Cike da farinciki suna shiga shasshafata tare da sauran abinda ba zan iya tsaya in gani ba balle in d’auko muku.
Ameera bata tashi a baccin wahala da take ba sai wahan 8:39pm.
Tana farkawa tajita jakam a jik’e.
Cike da tashin hankali tayi yunkurin mik’ewa amma ta kasa,ji tayi kaman an kulle mata mara.
Komawa tayi ta k’wanta.
A tsorace tasa hannunta a hankali karkashinta inda take jin danshin.
Hannunta har rawa yake saboda tsaban fargaban me zata gani.
Wani ruwa mai yauk’i ta gani had’e da jini yana bin k’afanta.
Kuma ne mai karfi k’wace Mata mata,ta rasa wani irin tunani zatayi.
A duke tana bin bango har ta shiga cikin bathroom zama tayi dirshan akasa tana kallon ikon Allah,jinin dai ya tsaya amma ruwan bulbulowa yake kaman an bud’e famfo.
Bata san ma ta ina zata fara ba shiyasa tayi zamanta,sai kusan 9:45 ta samu ya tsagaita zuba,da k’yar ta mik’e tayi wanka ta fito tare da canza kayanta ta k’wanta tana jiran hukuncin Allah.
Azaba take ji kota ina ga abin cikinta nata da yake k’ara damunta da motsi.
Juyi take tana hawaye ba mai taimakonta,sai bayan karfe biyu da rabi na dare sannan ta samu wani wahalallen bacci ya d’auke ta.
Tana ta zuba ido ko Al’ameen zai shigo amma har tayi bacci ba labarinshi.
Koda same da ta tashi ciwon da take ji ya d’,an lafa saidai ruwan ne bai tsaya ba…
Zamanta tayi cikin bedroom d’inta ko parlournta bata lek’a ba balle tayi gigin fita aiki.
Tana nan zaune ta fara jin motsi a parlournta,zuba ido tayi tana jiran taga ko wayene saboda tasan Al’ameen ko kallonta bai isa yayi ba balle har ya kaiga shigowa part d’inta.
Zuru tayi tana kallon k’ofan shigowa bedroom d’inta.
Turo k’ofan akayi aka shigo.
Lateefa ta gani tsaye a bakin k’ofan da murmushi akan fuskarta.
Tsoro k’arara ya baiyana akan fuskan Ameera ganin Lateefa yau har cikin bedroom d’inta, ta san dai alkhairi ba zai tab’a shigowa da ita ba sai dai akasinta .
K’arasowa tayi gabanta tana kallon ta har yanzu da murmushinta.
“Ya jikin ‘year k’anwata?” Tace lokacin da take tsugunawa a gabanta .
Da k’yar bakinta ya iya cewa “da sauki”.
” ina da ina ke miki ciwo”ta tambaya still wit her smiling face.
Da hannu ta nuna mata cikinta da bayanta.
Matsowa ta k’arayi gabanta taxa hannu ta danna mata mara da iya karfinta har saida tayi k’aran azaba tace…” Nan ko?”
“Sannu kinji,ina son in kika ji ciwon ya k’aru ki min magana mu tafi hospital ko?”
Gyad’a kai tayi kawai dan batada bakin magana.
Mik’ewa tayi tare da nufan hanyan fita.
D’an dakatawa tayi ta waigo tace…”ina parlour in kina nema na”.
Tana fad’an haka tasa kai ta fice.
Wayarta ta lalubu da yake gefenta da niyan k’iran Ummanta ko Al’ameen dan su san halin da take ciki sai dai Nash ashe wayar ba kota flashing.
Cilli tayi da wayan a tsakar d’akin har komai na wayan ya tarwatse saboda haushi wayar ma ya bata.
Daga bata kuma taga in wayar tana kunne kila Al’ameen ko Fateema wani ya neme ta a cikinsu.
Yunkura tayi da niyan d’auko wayarta dan ta had’a amma ta kasa motsa koda kafartane .
Hak’ura tayi ta kwanta tana jiran mutuwarta .
Motsi ta kara ji a parlournta kuma yanzu cikin sand’a.
Hakan ba k’aramin taxa mata hankali yayi ba,kar dai Lateefa ce ta k’ara dawowa dan ta k’arasata.
Zubawa kofa ido tayi tana jiran taga mai shigowa.
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
????♀????♀????♀????♀????♀????♀
*~UKUBAR KISHIYATA
????????????????????????
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*
*~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
*part thirty seven*
K’ofan taga an turo a hankali wanda ya k’ara mata tsoro da fargaba da take ciki.
Rabi taga ta lek’o da kanta itama a tsorace.
K’arasowa tayi da sauri ganin Ameera a yashe a tsakar d’akin tana…” Subhanallahi ‘yar nan jikin ne haka?ni dama tunda safe da ban ganki ba hankalina yaki k’wanciya.ina son shigowa in dubaki amma tsoron Hajiya ya hanani shigowa,yanzuma wannan mutumin nan da suke yawan fita tare shiya zo suka fita shiyasa nayi amfani da wannan daman na shigo dan duba lafiyarki.ashe haka jikin ya k’ara tsanani?”
Ameera kawai sauraronta take dan bakinta ya kasa furta komai.
Rabi tace…” Yanzu ina yake miki ciwo?”
Da k’yar ta bud’i baki tace…” Rabi cikina bayana zai karye,Rabi zan mutu ki k’ira min Ummata”
“Ba zaki mutu ba Hajiya alamun nak’uda nake gani a tare dake, Sai dai kaman lokacin haihuwar da saura.ko kuma jirani ina zuwa” tana fad’an haka ta fice da saurinta.
Bata tsaya a ko ina ba sai wajan Baba mai gadi,tana zuwa bata b’ata lokaci ba ta sanar dashi halin da Ameera take ciki.
Nan da nan yacewa Rabi ta kawo ruwa ya mata addu’a in dai haihuwa ce toh da izinin Allah ba zata dad’e ba zata haihu,in kuma wani abinne daban shima da izinin Allah zai zo mata da sauki.
Da gudu Rabi tayi cikin gida tazo da ruwa a cup ta mik’a mishi.
Shima kamin ya tazo yayi Alwala yana jiranta.
Tana bashi ruwan ya zauna ya fara addu’oi yana tofawa a cikin ruwan.
Ya d’auki lokaci mai d’an tsawo kamin ya gama ya bata yace…
“Gashi in kinje ki zaka k’ankara a ciki yayi sosai a bata tasha da bismillah.
Godiya Rabi tayi mishi sannan ta koma cikin gida da saurinta,saida ta saka k’ankara yayi sanyin sannan ta kaiwa Ameera tasha.
Abinci ta kawo mata ta tilasta mata taci kad’an.
Zama tayi kusa da ita tana mata hira samama,zuwa kaman 40 mins Ameera harta manta da wani da take ji,suka kama hira sosai harda dariya.