UKUBAR KISHIYATA Page 31 to 40

Rabi taji dad’in yanda taga ta watsake haka tace..” Uhum Hajiya hiran ba zata k’are ba kuma tunda naga ciwon ya d’an lafa bari inje in d’ora girki”.
Sai a lokacin Ameera ta tuna ashe fa bata da lafiya…” Rabi wallahi na daina jin komai wani irin magani kika bani nasha?”
Baba Bello ne ya miki addu’a a cikin ruwa na kawo miki,ko a kauye mutane suna tururuwa wajan karb’an ruwan addu’a a wajanshi kasancewar k’auyenmu d’aya dashi shiyasa na sanshi”.
Ameera tace…”Allah sarki Baba,Rabi dan Allah ki fara mik’a mishi sak’on godiyata kamin inje da kaina”.
Yunkura Rabi tayi ta tashi tana..” zaiji insha Allah”.
Tana fita Ameera itama taja jiki ta tashi ta fad’a bathroom tayi wanka dan ta k’ara jin dad’in jikinta.
Rama salloli da ake binta ta farayi sannan ta kimtsa ta fito kitchen wajan Rabi wacce harta kusa gama aikinta.
Kallonta Rabi ta tsayayi saboda mamaki can tace..” Haba Hajiya ya zaki fito?aida zamanki kikayi saboda na kusa kammalawa”.
Murmushi Ameera tayi tace..”aiko da wanke-wanke zan taya ki”.
“Barshi ki koma d’aki kada tazo ta iske ki anan, kuma karki bari tasan kin samu sauki kiyi k’wanciyarki ki na k’wana 2.ina tsamanin matsalar da ya sameki yana da nasaba da aikin wahala da kikeyi”.
Ameera bata musa mata ba ta amsa da ” toh ” ta koma part d’inta.
Rabi tana gama girki ta zubawa Ameera a warmer ta kai mata har bedroom.
Bata fita a d’akin ba saida ta tabbatar da Ameera taci ta koshi sannan ta k’washe kayan ta fita tana k’ara jaddadawa Ameera tayi k’wanciyarta kuma tayi yanda tace mata dan tasan yanzu duk yanda akayi Lateefa tana kan hanyar dawowa,sabida duk tsiyarta bata yarda Al’ameen ya rigata dawowa.
Rabi tana fita idonta ya kai kan wayarta da yake tarwatse a tsakiyar d’akin.
Da sauri ta d’auka ta had’a shi ta kunna tana Allah sarki Yayana nasan ya neme in bai samu ba.
Kunna wayar tayi ta ajiye a gefenta tana kallon yanda a in cikinta ya isheta da motsi,hannu ta kai tana shafawa da murmushi a fuskarta.
Wayanta ne ya katse mata abinda take,wayar ta jawo tarw da receiving call din.
Sallama tayi tana murmushi kaman yana ganinta.
Lumshe ido Al’ameen yayi tare da ajiyan zuciya tace…” Haba Babyna kin kusa zautar dani yau,kinsan zan kiraki Dan inji lafiyarku shine kika kashe min Waya?kodai wani laifin nayiakayi min irin wannan horon mai tsanani a haka?”
Bata katse shi ba harya kai aya sannan ta bashi amsa da…” Ko d’aya Yayana ai kai haka laifi a wajanmu just dai na manta ne ban kunna way an ba”.
Nan suka cigaba da hiransu kaman basu da wata matsala a rayuwa.
Lateefa cikin sauri take driving cos a yanzu babban burinta shine taje taga wani hali Ameera take ciki.
Yau kwata-kwata bata so ta motsa ko nan da can ba saboda tana son yin amfani da shawaran Aina’u tana fara haihuwan ta karasata kowa ya huta.
Sales shiya hura mata wuta a Waya kan dole taje su had’u wai yayi missing d’inta,da taso yi mishi gardama amma ganin ranshi ya back yasa ta hak’ura tabi shi badan komai ba sai dan bata son bacin ranshi.
Tana shigowa cikin gidan direct part d’in Ameera ta nufa tana aiyana abu iri-iri a ranta.
Da d’an fargaba ta tura k’ofan ta shiga.
Ameera suna cikin waya da Al’ameen taji motsin mutum a parlournta.
Kashe wayan tayi gaba d’aya ta tura shi can kan gado sannan ta rungume cikinta da hannu 2 tare da runtsr ido ta fara murkususu.
Lateefa saida taji zuciyarta ta bada *DUM* ganin har yanzu da sauran ranta kuma nataccen cikin nata yana nan bai b’are ba.
Sai dai ta wani side d’in taji sanyi a ranta tunda da alamu bata ciki. hayyacinta.
D’an dariya Lateefa tayi na jin dad’i sannan tasa kai ta fice.
Ameera bata juyi da murkushe-murkusen ba said a ta tabbatar da Lattefa ta sannan ta mik’e zaune Rana murmushi saboda taji dadin shawaran Rabi.
Lateefa tana fita part d’inta ta wuce.
Bayan ta rage kayan jikinta ta zauna a bakin gado tare da kitan Mamanta.
Bayan sun gaisa Lateefa ta bata abinda ya faru tunda daga ranan da suka mata maganin har zuwa yanzu da ta fito a d’akinta.
“Ba wacce maganin nan ciki ya zauna a jikinta,ba dai kince bata cikin hayyacinta ba?” Mama ta tambaya.
Lateefa ta bata amsa da “eh”
Mama tace…”ki bata kwana 2zai zube “.
Cikin jin dad’e Lateefa tace ” shiken nan Mama nagode”
” INA k’anenki ne yau kusan kwana 4ban jisu a Waya ba”
“Suna can wajan shiye-shirye bikin kawarsu”
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
????♀????♀????♀????♀????♀????♀
*~UKUBAR KISHIYATA
????????????????????????
(Its all about love and betrayal)
*Story by*
*UMMEE YUSUF*
(Maman Yusuf)
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*
*~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
*part thirty eight*
Suna gama waya da Mama ta fad’a bathroom hankali k’wance tayi wankanta tare da tsantsara make up ta zauna jiran Al’ameen ranta fari sol.
Al’ameen bai samu daman shiga part d’in Ameera ba sai wajan karfe 2 na dare.
Tana tsakiyan baccinta ya shigo.
Yaye bargon yayi shima ya shiga ya k’wanta tare da k’ara lullube su.
Jawota yayi jikin sosai ya rungume ,sai faman shinshinata yake kaman wani sabon maye.
Bud’e ido tayi ta ganshi mak’ale da ita,kara shigewa jikin shi tayi dan sunyi missing d’in juna.
Al’ameen dama kaman jira yake ya shiga aika mata da sak’oni,shi bai barta ba sai suka farantawa juna rai.
Daga nan suka shiga hirarsu cikin k’wanciyar hankali, bai bar d’akin ba sai da ya tabbatar da ta koma bacci sanna ya koma part nashi.
Haka Ameera tacigaba da zamanta a cikin d’aki ko parlourta bata fitowa sai dai taci tayi wanka ta kwanta.
Lateefa bata daina mata sintiri a d’aki ba,wai ko zata ga tana labor ta k’arasatan.
Ameera itama tana jin motsinta zata fara murkususun k’arya,ba zata daina ba har sai ta fita.
Wannan abu yana yiwa Lateefa ciwo ace yau kusan sati da bata maganin amma ciki yaki ya zube,kuma da zarar tayiwa Mama complain sai tace ta k’ara hakuri zuwa k’wana 2n da Lateefa bata son ji dan haka tayi niyyan d’aukan mataki da kanta.
Yau Saturday yazo dai-dai da ranan d’aurin auren Binta da mijinta Major General Ibrahim Hassan.
Su Fa’iza sun kai sati da tarewa a gidansu Binta kasancewarsu manyan k’awaye.
Lateefa tayi shirinta tsab na zuwa bikin,tasha ky’au cikin purple shaddanta with purple veil in short komai purple tayi amfani da shi.
Sai dai Kasan zuciyarta ba bikin bane dalilin fitanta,so take daga can ta wuce su had’u da bestynta ta bata shawara akan Ameera da d’an cikinta dan yanzu ta gaji da ganinta haka gara ayita ta kare.
Ameera tana jin fitanta ta fito main parlour tayi zamanta dan rabonta da fitowa tun ranan da Lateefa da kannenta suka d’ura mata magani.
Lateefa bata wani jima a gidan bikin ba ta wuce Neman Aina’u.
Numbernta tayi dialling kusan 3 missed call ta bata kamin ta samu ta daga wayan tana magana da k’yar tace” Besty ya akayine?”.
A zuciye Lateefa tace..” Wai a ina kika ajiye wayan ina ta kira baki d’aga ba?”
Hak’uri Aina’u ta bata tace tana tare da Alhajinta ne yanzun amma ta bata nan da 15 mins zata fito Sai su had’u a at home restaurant.
Ba b’ata lokaci Lateefa taja motantan sai can,sai dai bata fito ba ta zauna a cikin motorn tana jiran isowarta.