UKUBAR KISHIYATA 1-END

UKUBAR KISHIYATA Page 31 to 40

Kaman yanda ta fad’a ba tafi 15 mins tana jiranta ba ta iso wajan cikin adaidaita sahu.

Fitowa itama tayi suka shiga ciki tare da samun wuri suka zauna.

Suna zama Aina’u tace..” Kinga ni yunwa nake ji,kiyi mana order abinci”.

Tabe baki Lateefa tayi tace…”ke kike ta abinci saboda dani matsalata daban ta kawo ni nan amma kiyi order duk abinda kike so akawo miki”.

Abinci mai rai da lafiya tasa aka kawo mata ta fara ci.

Aina’u ba tayi magana ba sai da tayi kusan rabin abincin sannan ta d’ago da kai tana kallon Lateefa data zuba mata na mujiya tana kallonta.

“Menene matsalar taki Hajiya?”

Sauke tagumi tayi tare da sauke ajiyar zaciya tace…” Kema kinsan baya wuce maganan yarinyan nan cos ita kad’aice matsalata a yanzu”.

Aina’u batayi magana ba sai da ta gama shanye juice d’in da ta d’ora a bakinta sanna ta fara maganan.

“But I think mun gama da chapternta tun last week,ko wani abine ya bullo bayan shi?”

“Shi d’inne Aina’u,taki haihuwan balle in samu daman aikata abinda nayi niyya.ga cikin shima yaki lalacewa sai dai kullum tana d’aki tana murkususu”.tace cike da damuwa.

Tunda ta fara Aina’u take kallonta,bata katse ta ba sai da ta kai aya sannan tace..” Wallahi kina bani mamaki yanzu ,Lateefa kaman ba kece mai bani shawara ba da komin saukin abu yanzu sai ki kasa samun bakin zar…..”

Katse ta Lateefa tayi da…” Ke ni dan Allah ki bar surutun nan ki bani shawara insan abinyi dan ni kaina ya kulle na rasa wani irin tunani zanyi”.

Aina’u saida ta numfasa tace…” Abune mai sauki Besty tunda kina da kudi,abinda zakiyi gobe ki samu private hospital mai k’yau ki kaita a matsayin kin kaita haihuwa daga nan ki samu babban doctor ki lallab’ashi ya mata alluran da zata shek’a kowa ya huta”.

Zaro ido Lateefa tayi tana kallonta tace…”Aina’u so like asirina ya tonu?wani doctor zaka kaiwa wannan babban al’amari ya saurare ka?”

Aina’u cikin k’wanciyar hankali take cin naman kaza dake gabanta tace…” Dad’ina dake saurin karaya,a duniyan nan wa zaik’i kud’i?millions zaki bashi nasan tabbas da gudu zai share miki hawaye nima zan shigo goben sai mu kaita tare,kada kiji wani abu saboda inaji a jikina matsarki tazo karshe”.

Haka tayi ta bata shawara tare da karfafa mata guiwa harta amince sannan suka rabu akan sai gobe ta iso.

Sai bayan 5:39 Lateefa ta dawo gida, ko ta kan Ameera ba tabi ba tana jiran wayewar gari su aikata barza’u.

Ameera cikin baccinta ta fara mafarkin tana jin wani azaba a mararta tun tana daurewa har ta fara juyi na azaba.

Wani irin juyi taji cikinta yayi wanda yayi sanadiyar farkawanta ba shiri,kuma sai a lokacin ta tabbatar ashe ba mafarki bane a zahiri take ji ga jikinta duk ya b’aci kaman na lokacin da Lateefa suka d’ura mata magani.

Addu’a ta farayi tana hawaye tana cewa a ranta inama ace rana ne da Baba mai gadi yayi mata tofi ta sha ko zata daina jin wannan azaban.

D’ago kai tayi tana kallon wall clock dake manne a d’akinta taga 1:30 na dare.

Tun tana hawaye tana add’uoi har hawayen suka kafe bakin ma ya mutu murus saina zuci da take.

K’ara kallon agogon tayi taga 2:00 ne kawai.

Cikin wani wahalalen murya tace ” wayyo Ummata ki yafe min nasan yau mutuwa zanyi.

Gumi duk ya wanke mata jiki kaman ba a.c a d’akin.

Ita kanta ta tabbatar ciwon yau da take ji ya nika wanda da take ji da nikin ba nikin.

Har karfe uku da rabi tana nan zaune ko k’wanciya ta kasayi balle wani abu wai shi bacci gashi yau Al’ameen bai shigo ba da ya taimaka mata.

A lokacin ne kuma taji fitsari ya cika mata Mara.

Yunk’ura tayi da niyan tashi amma ta gagara da haka da rarrafe ta k’arasa bathroom danyin fitsarin amma abin mamaki ta kasa tsugunawa.

Zamanta tayi dirshan a cikin bathroom d’in tare da mimmike k’afa.

Yunkura tayi da niyan fitsarin amma taji wani abu daban da bata san dame zata k’watanta shi ba yazo ya danne ta ga wani azaba da tunda tazo duniya ko labarin shi bata tab’a jiba take ji.

Fasa fitsarin tayi tana yarfe hannu ta rasa ina zata saka ranta taji sanyi.

Sau uku tana gwadawa amma sai ta kasa na hud’une taji wani nishi mai karfi yazo mata wanda saida ta toshe baki da hannu dan ji take kaman ta k’wala ihu saboda zaba.

Maimakon taji tayi fitsari sai jin wani abu daban tayi ya fad’o harda kuka.

A firgice ta kalli wuri yaro ta gani fari sol dashi.

Mamaki da tsoro ya hanata tab’a yaron.

A wautarta bata San cewa labor take ba ta d’auka irin ciwon nan me da take yi yana lafawa.

Zuba mishi ido tayi tana kallon yanda yake tsotsan hannu tare da bin bulb light dake bathroom d’in.

Sababbin azaba ta fara ji tana juye-juye,ba’a d’auki lokaci ba ta sankato da baby girl.

Cikin ikon Allah tare da mabiyan suka fad’o ta fara cancara kuka.

Motsi mutum taji a cikin d’akinta wanda ya haddasa mata tsoro da fargaba.

Motsin na kara kusanto bathroom d’in yayin da zuciyarta me kara lugude.

Ba kowa take tsoro ba illa Lateefa,cikin daren nan ta same ta da yaran nan komai zai iya faruwa.

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀

*~UKUBAR KISHIYATA

????????????????????????

(Its all about love and betrayal)

Story by *~UMMEE YUSUF~*

(Maman Yusuf)

*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*

*~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*

*part thirty nine*

Knocking k’ofan bathroom d’in taji anyi wanda saida hanjin cikinta ya kad’a saboda tsoro.

Murya k’asa-k’asa taji yace…”Babyna are u alright? ”

Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi sannan ta saita muryanta da ya dashe tace…”Yayana kaine a wannan lokacin?”

“Mafarkai nake tayi akanki shiyasa na kasa daurewa nazo in duba lafiyarki”.

Murmushi tayi jin furucin shi tace…” Ka shigo mana”.

“Me kike yine a cikin bathroom at this time har kike cewa in…” Maganan ce ta mak’ale mishi a mak’ok’oro ganin Ameera zaune da ‘ya’ya 2 a tsakanin k’afanta.

Da sassarfa ya shigo ciki jikinshi har b’ari yake.

Idon shi cike da kwalla ya tsuguna kusa da ita.

Hannun shi yana karkarwa ya kai yana shafasu cike da so.

Juyowa yayi yana kallon Ameera da hawaye shame-shame a fuska dan yama kasa magana.

Girgiza mishi kai tayi tana murmushi,kasa daurewa yayi ya jawota jikinshi ya rungume yana kukan farincikin k’yautar da Allah ya bashi,yau shekara goma sha hudu da wani abu da yin aure bai samu haihuwa sai yau.

Wani sabon k’aunarta yake jin yana ratsa ko ina na jikinshi.

Da k’yar Ameera ta k’wace kanta tace..” Yayana ya isa haka,kaji ana kiran an k’ira sallah tashi ka tafi massalaci”.

Girgiza mata kai kawai yake yana k’ara matse ta a jikinshi.

“Pls ka tafi zaka makara a jam’i don’t worry we will be fine”.

Da k’yar ta samu ya sake ta ya nufi hanya fita,har ya kai bakin k’ofa ya dawo yace…” Kin iya yanda ake yankan cibi?”

“Ban iya komai ba amma ka bani Waya in k’ira Umma dan ta iya har gida ake zuwa ana kiranta tana taimakawa masu haihuwa”.

Bata gama rufe baki ba ya fita da gudu ya d’auko mata wayan ya bata.

Wajan da yaran yaje India suke k’wance suna tsoson hannu.

Shafa gashin Kansu dake k’wance har wuya ya shiga yi,dariya ce ta tsubuce mishi wanda baisan lokacin da yazo mishi ba ji yake kaman ya maida su ciki yake jin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button