UKUBAR KISHIYATA 1-END

UKUBAR KISHIYATA Page 41 to 50 (The End)

Wani abu mai kama da mashi Lateefa taji ya soke ta a kirji,ga wani d’aci daya taso mata Wanda bata san ta ina yazo ba saiji tayi ya cika mata mak’ok’oro.Da k’yar ta saita kanta gudun kada Rabi ta fahimci halin da take ciki tace…”naji tashi ki tafi ki k’arasa aikinki”

Mik’ewa Rabi tayi tana dariya a cikin ranta tace…”duk *UKUBAR* da zaki gana mata baki isa ki canza abinda Allah ya tsara ba.

Rabi tana b’ace mata ta fad’a kan kujera ta baya dab’as ta zauna dan dama jiri take gani daurewa kawai take..

Ta rasa wani irin tunani zatayi,wani sashi na zuciyarta yace kije ki gani da idonki kamin ki yanke hukunci.

A zabure ta mik’e kaman wacce aka tsikarawa allura tayi part d’in Ameera.

Tana shiga ta samesu sun saka kayan breakfast da Rabi ta kawo musu a gaba Umma tana yiwa Ameera fad’an ta shanye tea d’in da ta had’a mata.

Zama tayi kusa da Ameera tana dariya wanda yayi kama da mai nishin kashi.

Gaida Umma ta farayi sannan ta juyo tana duban Ameera tace… “Haba k’anwata muna cikin gidan nan amma ki haihu ke kad’ai ba k’ya tsoron wani abu ya faru dake?”

“Yanzu na gama yi mata fad’a kada ta sake irin wannan koda a gaba ne”Umma tace mata.

Lateefa ji yayi kaman an watsa mata tafashasshen ruwa ajiki.

Tana yiwa Umma wani irin kallo ta k’asan ido kuma tana magana a zucoyarta tace kaji min munafukar tsohuwar nan har wani haihuwa ‘yar taki zata k’arayi a gidan nan wannan ma sakaci nane but zan baku mamaki a gaba.

K’ara had’iye damuwarta tayi tace…” Ina jinjiran ko jinjiri muka samu?”

Umma ce ta bata amsa da..”gasu can kan gadi”

Cike da fargaban me Umma take nufi gasu can ta juyo ta dubi kan gadon.

Idanunta kusan zazzagowa suka yi ganin twins a kan gado,zuciyarta kuma kaman ya fashe take ji.

Da k’yar ta daure ta rarrashi kanta ta mik’e ta iso bakin gadon tana lek’ensu. 

Wannan karan da k’yar ta hana bakin ta kurma ihun da yazo mata ba shiri.

Umma da Fateema suna cin abinci basu lura da yanayinta ba amma Ameera tana kallonta ta k’asan ido.

Ko d’aukansu batayi ba tace…” Ina zuwa ta fice cikin sauri saboda ta tabbata tana k’ara minti 2 a gaban yaran nan zata iya aikata abinda bashine ba a gaban mutane.

Tana fita yayi daidai da sauk’owar Al’ameen daga part d’inshi.

Ya lura da yanda ta birkice amma ya basar yace..” Ya naga kan table bakomai ko masu aikin basa nan ne?”

Da gudu Lateefa tayi kanshi tare cin k’walan rigan shi tana jijiga shi ta fara bala’i..”Al’ameen wallahi kayi kad’an ka wulakantani a gidan nan daga kai har ita baku isa komai a wajena ba,munafuki kawai in banda munafurci kaida nayi maka iyaka da wannan yarinyan ta yaya ka ka tsallake kaje kayi mata ciki? Iye tambayarka nakeyi” 

Murmushi kawai Al’ameen yake yana kallonta,a haka Aina’u ta shigo ta same su.

Da k’yar Aina’u taja ta zuwa part d’inta.

Gyara zaman rigan shi yayi ya shige part d’in Ameera hankalin shi k’wance.

A parkour ya iske Umma da Fateema suna kintsa mata.

Durk’usawa yayi har k’asa ya gaida Umma,Fateema ma ta gaishe shi sannan ya wuce ciki bedroom inada Ameera da twins d’inta suke.

Ameera tasa twins a gaba tana ta kallo tana mamakin wai a jikinta suka fito.

A haka Al’ameen ya shigo ya same ta.

Zama yayi a bakin gado suka sakarwa juna murumushi ya shafa gefen fuskarta yace…” Maman twins kinyi kokari ya jiki ?”

“Da sauki” ta bashi ansa.

D’aukan Baby boy d’in yayi yayi mishi hud’uba yayi pecking goshi shi sannan ya rungume shi yana k’ara jin k’aunar yaron yana ratsa ko’ina a jikin shi.

Da k’yar ya ajiye shi sannan ya d’auko Baby girl itama yayi mata d same thing ya ajiye ta.

Yana juyowa yaga Ameera ta zuba musu ido tana murmushi,gira d’aya ya d’aga mata yace…” Ya dai?”

“Bakomai kallo nake” ta bashi amsa tana murmushi.

Dungure mata kai yayi yana dariya yace …” ‘Yar sa ido kawai”.

Dariya itama tayi batayi magana ba.

Nan yake tambayarta abinda ya kamata ya sayo musu.

Cewa tayi ya tambayi Umma ta gaya mishi.

“OK ke bazaki gaya min ba?”ya tambayeta.

Amsa mishi tayi da…”kasan tafini sanin abinda ya dace”.

” hakane,na tafi saina dawo”yace tare bata Peck sannan ya fito parlour wajansu Umma.

Dukawa yayi ya tambayi Umma abinda ya dace ya sayo,nan tayi mishi bayanin abubuwan da ya dace ya sayo irinsu madaran da zasu sha towels,kayan sawa,kayan sanyi da sauransu.

Ya mik’e da niyan fita Hajiyar shi tayi sallama ta shigo.

Komawa yayi ya zauna suka gaisa ya mata jagora zuwa d’akin mai jego sannan ya fita siyan abinda aka lissafa mishi.

Lateefa tana zaune sai cika take tana batsewa tana ciccize leb’e.

Aina’u tace” wai meya faru na ganki haka,ki tashi tunda ya fita mu kai shegiya ayi mata alluran mu huta”.

“Komai ya lalace Aina’u komai ya wargaje”

Cikun rashin fahimta Aina’u take kollonta tace…”bangane komai ya lalace ya wargace ba”.

Murmushin takaici Lateefa tayi tana kallonta k’awarta tace..”ta haihu,ta haifi ‘ya’ya har 2″.

D’ora hannayenta duka 2 Aina’u tayi tana salati tace…”2? Lateefa bama d’aya ba?”

“Saima kin gansu zuciyarki zata iya bugawa” Lateefa tace tana goge hawayen daya zubo mata.

“Haba dole in ganki cikin tashin hankali,kuttt ya akayi kika bari ta haihu baki kashe shegiya ba?” Aina’u ta tambaya cikin tashin hankali.

“Cikin dare ta haihu kawai ganinta nayi yara da safen nan,ita kuma munafukar uwarta harda cewa nayi mata fad’a haihuwa ita kad’ai koda gaba ta nemi mutum kusa da ita” ta karasa maganan cikin k’waikwayon muryan Umma.

“Kaji ‘yar abu kazan uba,kinsan abinda zamuyi wajan boka zamu koma ya kashe yaran shima munafikin mijin naki muyi maganin shi ya kasance naki ke kad’ai”.

Ajiyar zuciya Lateefa tayi tace…” King Aina’u na fara tsinkewa da al’amarin nan kuma….”

Pls kuyi manage da wannan.

????????????????????????

*UKUBAR KISHIYATA*

????????????????????????

(Its all about love and betrayal)

Story by *~UMMEE YUSUF~*

  (Maman Yusuf)

*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*????????????

❄ *~we bearer’s of golden writer’s assiduously percieven No pain so Magical our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*❄

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*Part forty one*

“Ke dallah dakata” Aina’u ta katse ta tana huci.

“Karki bani kunya mana sai kace ba Lateefa ‘yar k’walisa ba,ta yaya zaki basu chance suyi winning akanki.just ki bani wuka da nama kiga abinda zai faru but for now dole ki daure zuciyarki karki sake ki nuna musu ba k’ya farinciki da haihuwan nan yanda koda daga baya wani abu ya faru ba wanda zai zarge ki.bayan suna sai mu koma wajan boka”….

Lafuza da shawarwarin Aina’u sunyi tasiri wajan k’wantarwa Lateefa hankali tare da d’aukan alkawari zata daure ayi komai da ita.

Al’ameen yana fita wani babban shopping mall da ake saida kayan babies suka je shida driver.

Kaya Al’ameen yake ta k’wasa kaman ba gobe,yawanci bala ke nuna mishi abinda ya dace ya saya kasancewar shi yana da yara har 3.

Saida suka cika trolley 3 da kayan babies sannan suka dawo gida.

A lokacin gidan a cike yake tap da ‘yan barka,kama daga matan brother’s d’in Al’ameen da ‘yan uwan Ameera duk sun iso gani.

Haka gidan ya kasance kullum cike da ‘yan barka.

Lateefa ta daure zuciyarta akayi ta hidima da ita mutane sai yabon k’yan halinta suke.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button