UKUBAR KISHIYATA Page 41 to 50 (The End)

Cak kukan nata ya tsaya kaman d’aukewar ruwan sama sakamakon abinda idonta ya gane mata.
Fa’iza da Shamsiyya ta gani a bayan moton sojoji fuska duk a kumbure.
Bata san lokacin da ta juya kan motan ta ba ta fara binsu a baya har zuwa jaji.
Zata shiga wasu manyan sojoji masu kama da samudawa suka dakatar da ita.
Rokonsu ta farayi kan suyi hak’uri su barta ta wuce kannenta ta gani an shiga dasu ciki.
D’ayan yace..” wa’yan nan ne k’annenki?”
Amsawa tayi tana k’ara kusanto su.
Tsawa suka daka mata kan ta tsaya inda take.
Duk baya sukayi suna toshe hanci tare dayi mata kallon k’yama.
D’ayan cikin su yace…
“Hey chidimma make u call oga and tell him”.
Wani k’aramin d’aki ya shiga ya d’auki waya irin lane line d’in nan yayi k’ira.
Bayan sun gama magana ya fito yace…” Joseph escort her in”.
Mota ta shiga tace shima ya shigo su tafi.
Kallon banza ya fara aika mata sannan yace…” Ban shirya mutuwa ba ji yanda kike wari kaman mushe in na shiga motarki suna na marigayi”.
Bata ce k’ala ba ta fara Jan motanta a hankali take bin bayan shi har zuwa wani area mai ban tsoro wajan tsit baka jin motsin komai sai wani k’aton soja mai manyan idanu gasu jawur dasu kaman barkono da suka gani a wajan da alamu shi yake tsoron wajan.
Tambayar Joseph yayi daga ina?
Nan Joseph yayi mishi bayanin komai.
Ido ya tsura mata na wani lokaci sannan ya tambaya…” K’annin ka ne?
“Eh dan Allah kuyi hak’uri ku sake su” tace tana mai zubda hawaye.
Girgiza kai yayi yace…” Kasan menene sunyi kana cewa a sake su? ”
Da sauri ta girgiza kai dan gaba d’aya ta gama tsurewa ganin wasu d’ika-d’ikan sojoji sun zo wajan da manyan bindigogi a hannun su.
“Those bloody bitches an kama su a gidan oga kuma a cikin bedroom na oga wit his wife suna yin iskanci,or I think u re among them abi?” Yace yana zaro mata manyan idanu shi.
Jiki na karkarwa ta fara basu hak’uri tace…” Wallahi ban san suna aikata irin wannan mummunar d’abi’a ba dan Allah ku rufa min asiri ku bar ni in tafi”.
“Then get out before oga come and sees u here” yace mata cikin tsawa.
Da gudu ta fad’a motarta ta fita daga barack d’in tana kukan bakin ciki na ba yanda zata yi ta fita dasu daga wannan bala’in,koda yake su suka jefa kansu a ciki.
Toh ya akayi suna cikin irin mutanen nan amma bata tab’a sani ba .
Sai yanzu idonta yake hasko mata yanda suke rayuwarsu su 2 kaman wasu masoya ta d’auka zallan shak’uwa ce ashe su abinda suke aikatawa kenan.
Da haka ta k’araso gida cikin tashin hankali.
Addu’a take Allah yasa ba kowa a parlour.
Cikin sa’a kuwa babu kowa ta samu parlour sai t.v da yake ta aiki shi kad’ai.
Ba b’ata lokaci ta fad’a part d’inta tare da murza key.
Zama tayi dirshan a k’asa ta rushe da kukan nadama,wai yau su duniya ta juyawa baya haka? Daga ita har k’annenta suna cikin *UKUBAR* rayuwa.
*UKUBAR* da suka jefa wasu a ciki yau gashi suna cikin wanda yafi karfin tunaninsu.
Ga wacce suke wulakanwa a baya yau gata cikin k’wanciyar hankali.
Dama haka duniya take?.
Har karfe 2 tana zaune a wajan ta kasa tashi.
Dama ba damuwa tayi da sallah ba,amma yau ganin azabar rayuwa yasa ta tashi tayi sallahn azahar.
Komawa tayi ta zauna kuma a lokacin ne ta tuna ashe ba taci komai ba tun safe.
Tunanin ya zatayi ta fita ta samu abinda zata ci take,can ta tuna ashe tana ajiye kayan tea a cikin d’aki.
Jiki na rawa na nufi drower ta bud’e taga kayan tean suna nan harda su snacks.
Bata damu da ta nemi ruwan zafi ba.
Bathroom ta shiga ta taro ruwa a cup tazo ta had’a tea tasha da snacks ta koshi.
Gado ta hau ta k’wanta tana tariyo tarihin rayuwarta.
Ta dad’e a k’wance sannan ta tashi ta d’auki wayarta ta k’ira number Salees.
Saida ya kusan tsinkewa ya d’aga yace…”yah ne Babyna?”
“Ba lafiya Salees i na cikin wani yanayi na tashin hankali ga rashin lafiya ya sani gaba” tace muryanta na shaking alamun tana kuka.
“Subhanallah!! Babyna meya faru,meke damunki?” Salees ya tambaya cikin tashin hankali.
Saida ta face hanci sannan tace …” Labari ne mai tsawo honey amma ina bukatan kud’ad’ena na wajanka saboda in samu daman fita abroad neman lafiya”.
Cike da tashin hankali yace..”abun har ya kai haka Baby na?kada ki damu gobe mu had’u a hotel sai in zo miki dasu ko?”
Wani sanyi taji ya ratsa ta na jin ya rik’e mata alkawari tace…”nagode Salees daz y I love u”.
” I love u 2 my Lateefa”.yace mata tare da katse wayan.
Tana k’wance a part d’inta taji Al’ameen yazo yana knocking amma tayi biris dashi kaman bata jiba.
Shima bai damu ba ya juya yayi kowan shi dama Ameera ce ta takura mishi lalle sai yazo ya duba lafiyarta duk da abinda Lateefa tayi mata bata rik’e ta a zuciya ba illa damuwa da tayi da ita.
Gari na wayewa tayi sammakon ficewa daga gidan ta tafi hotel inda sukayi alkawari da Salees kan zai kawo mata kud’i.
Anan tayi ordern kayan breakfast tayi ta zauna har zuwa 9am sannan tayi mishi waya.
Shi kuma ya tabbatar mata da ba matsala yana nan zuwa.
Zuwa thirty minutes sai gashi nan ya shigo jaye da wata katuwar trolly da wata madaidaiciyar jaka a kafada.
Tana ganin shi ta mik’e cike da murna dan ta tare shi.
Warin daya ji ya tare shi,shiya hana shi shigowa ya tsaya a bakin k’ofa yana yatsina fuska.
Ganin haka yasa itama tayi turus ta tsaya ba tare da ta k’arasa wajan shi ba.
“Kaga babban dalilin da yasa nake neman kud’in kenan Salees”ta fad’i haka tana duban shi tare da marairaicewa.
Ta cigaba da cewa…” Banyi zaton kaima kana cikin masu guduna ba,saboda kai kad’aine hope d’ina Salees”.
“No don’t say so Lateefa” ya fad’i haka yana k’arasowa ciki.
Sannan ya cigaba…”kema kinsan bazan tab’a gudunki ba no matter how, saima in k’ara tausaya miki”.
Sauke jakunan da yazo dasu yayi tare da zuge zip d’insu duka.
Dollars ne tab a cikin babban trollyn,sai k’aramar kuma dubu Dubu ne a ciki.
D’ago kai yayi yana murmushi yace…”ga dukiyar ki nan na dawo miki dasu kaman yanda kika bani amana”.
Durkushewa tayi a wajan tana hawaye tace…”da za’a samu irinka a duniyan nan da duniya bata lalace haka ba dan rik’on amana yayi k’aranci a wannan zamanin .ban san da wani baki zan gode maka ba Salees sai dai ince Allah ya barmu tare.insha Allah in na sami lafiya na dawo zan baka sharen ka”.
Murmushi yayi yace…”don’t worry Baby just buri na ki samu lafiya.let’s go in kinsan nayi missing d’inki sosai”.
Cikin murmushi tayi ciki yana binta a baya ta hau gado ta k’wanta.
“Oh gosh ” yace yana dafa goshin shi sannan ya cigaba …”na manta ban rufe kofa ba ,bari in rufe in dawo kuma nazo miki da surprise sai dai ina so ki rufe idonki har sai nace ki bud’e sannan ki bud’e kinji Babyna?”
Cikin zumud’i ta saka tafin hannayenta ta rufe fuskanta.
Tana ji ya fita zuwa parlour har ya rufe k’ofan ya dawo ya tarar har yanzu fuskarta a rufe yake.
“Babyna bud’e idonki….” Yace cikin romantic voice.
A hankali ta bud’e idonta tana murmushi.
A zabure ta mik’e tana nuna su da yatsa bakinta yana motsi amma sauti yaki fitowa saboda kid’ima.
Salees ya k’ara rugumo Aina’u suna mata dariya yace… ” haba Babyna meye na kid’imewa haka?wannan shine first surprise saura na 2 kenan”.
Kukan kura tayi tayo Kansu da gudu.
Tun kamin ta k’araso Salees yasa mata k’afa ta fad’i.
Kamota sukayi suka fito parlour da ita Salees ya zaunar da ita akan kujera, Aina’u ta bud’e hand bag da tazo dashi ta fito da igiya ta bashi.