UKUBAR KISHIYATA 1-END

UKUBAR KISHIYATA Page 41 to 50 (The End)

Turawa yayi ya shiga ciki tare da dube-dube.

Lateefa ya gani d’aure kan kujera cikin jini male-male bata cikin haiyacin ta.

Da gudu ya k’arasa wajanta yana ambaton sunanta tare da girgiza ta amma bata san ma yanayi ba.

Waya ya fito dashi ya k’ira Ya Sa’ad da shi,shi kuma yace ya fara k’iran police tukunna suna zuwa.

yana nan tsaye cikin tashin hankali dan ya rasa dame zai fasaara wannan al’anari.

Within 15 mins ambulance da police suka zo at d same time.

Bayan ‘yan geaje-gwaje da bincike da police suka yi aka saka ta a ambulance akayi Hospital da ita.

Al’ameen shima motan shi ya fad’a ya bisu a baya.

Suna isa asibitin aka wuce da ita emergency,doctors kusan su hud’u harda Ya Sa’ad suka taru a kanta wanda a dole suke aikin saboda warin da jikinta yake fitarwa.

Mamanta ya k’ira ya sanar da ita abinda yake faruwa.

Cikin rud’u da gigita tace gata nan zuwa.

Iyayen shi ya k’ira suma ya sanar dasu,nan suka taya shi jimami tare da cewa suna zuwa .

Haka yayi ta sanar da duk wanda ya dace ya sanar,bayan ya gama wayar doctors suka fito da nasaran cewa an samu dakatar da jinin kuma anyi sa’a blood group d’inta A ne dan haka har an k’ara mata zuwa nan da 1 hr zata iya farkawa.

Godiya ya musu sannan yace zai je gida ya dawo.

Ameera tana zaune ita kad’ai a parlour ta rafka tagumi da hannayenta duka 2 .

Tana ganin shi ta mik’e da sauri ganin ya dawo kaman ba yanda ya fita ba.

A tare suka zauna akan kujera 2 seater yace …” Ki shirya muje hospital ”

“Hospital kuma meya faru waye ba lafiya?”Ameera ta katse shi da tambaya.

” Lateefa ce”ya bata amsa a gajarce tare da bata labarin abinda ya gani .

Salati ta rinka maimaitawa tare da mamakin waye yayi mata wannan aikin.

A gurguje ta gama shiryawa harda twins d’inta cikin kaya masu k’yau suka nufi hospital gaba d’ayansu.

A can suka tarar dasu Alhaji da sauran ‘yan uwa duk sunyi jugum dasu .

Bayan sun samu waje sun zauna Hajiyar shi take tambayar shi ya akayi hakan ta faru?

Nan itama ya maimaita musu abinda ya gani.kowa ya rink’a tofa albarkacin bakin shi,sun d’an jima zaune suka hango Maman Lateefa wujiga-wujiga tana tahowa.

Idonta ya riga da ya rufe dan haka bata ma lura dasu ba har zata wuce Al’ameen yayi mata magana ta tsaya ta dawo wajansu .

Hajiyar Al’ameen ta sauke Fadeela dake kan cinyarta ta kamo hannunta suka zauna tare da tambsyar ya jikin’yarta?

Hajiya tace…”gamu nan dai muna jiran farfad’owarta dan sunce nan da awa 1 zata farka amma gashi har awa 2 ta wuce”.

Kuka tasa tana…”dan Allah ku gaya min ko ta mutu ne?”

Hajiya ta bud’i baki da niyan bata amsa wata nurse tazo tana tambayar INA Al’ameen da Ameera?

A tare suka mi’ke suna kallonta.

“Ta farka kuma tace tana son ganin ku”

Gaba d’ayan su suka d’uru cikin d’akin.

A take sauran suka koma baya suna toshe hanci sakamakon warin da suka ji ya tare su.

Kuka take kaman ranta ya fita tana duban su d’aya bayan d’aya .

Cikin kuka tace…”Al’ameen,Ameera ku yafe min nasan alhakin kune yake bibiyata na cuci kaina na cutar daku a bata ta fanni da yawa”.

Nan ta fara zaiyane musu abubuwan da ta shuka tun kamin auren ta da Al’ameen har zuwa yanda Al’ameen yazo ya same ta a hotel.

Tunda ta fara jawabin Al’ameen yake ji kaman ba shi ba kuma sai a lokacin ya fara tuno abubuwan da suka faru wanda da yake ganin kaman a mafarki ya faru ashe da gaske ne.

Wani irin tsanan ta ya rinka ji wanda baya tsammanin akwai wani halitta da ya tab’a tsanan abu kaman yanda ya tsani Lateefa ba a yanzu.

Rokonsu ta farayi tana magiya harda hawaye kan su yafe mata wanda Al’ameen yake ji kaman ruwan dalma take zuba mishi.

A zuciye Al’ameen yayi kanta ya shake mata wuya yanda ko numfashi bata iya shak’a nan da nan idonta suka firfito waje tare da firfitowa.

????????????????????????

*UKUBAR KISHIYATA*

????????????????????????

(Its all about love and betrayal)

Story by *~UMMEE YUSUF~*

(Maman Yusuf)

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*

*_~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~_*

*part fiffty*

*last page*

Da gudu yayun shi sukayi kanshi suna kokarin b’anbare hannun shi daga wuyanta amma suka kasa.

Alhaji ne yazo ya k’washe shi da mari tare da hankad’a shi gefe.

Bango ya nausa da duka karfin shi na haushin bai samu nasaran halakata ba inama ace Alhaji baya wajan da sai ya raba ta da duniyan inyaso duk abinda zai faru ya faru.

Lateefa sai tari take Mamarta tana rik’e da ita gaba d’aya ta fita haiyyacinta.

Ameera tana gefe sarkin tausayi sai sharar hawaye take tace…Anty kiyi shiru ni kam na yafe m….”.

Tsawan da Al’ameen ya daka mata yasa ta katse maganarta tana kallon shi a tsoro ce saboda a iya zamansu hakan bai tab’a faruwa ba.

“Baki da hankali ne?kina jin abinda tace ta aikata miki harda yaran mu da bakinta amma ki wani ce zaki yafe mata?” Ya k’arasa maganan cike da takaici yana huci.

Ta bud’i baki da niyar magana kenan police duka shigoda hakan kud’in da Sslees ya bar mata.

Gaishe da mutanen d’akin sukayi sannan d.p.o ya fara bayani kan cewa basu samu evidence d’in komai ba,da alama mutanen sunyi da gloves amma dai zasu cigaba da bincike har sai sun gano wanda yayi wannan d’anyen aikin.

Juyowa Al’ameen yayi wanda tunda suka shigo ya juya musu baya yace…”kaga d.p.kuyi tafiyarku ba sai kun wahala ba na yafe binciken Ku bar shi kawai”.

“Amma yallabai aiko kace mu bari ba zaiyu ba saboda dole hukuma ta nemo mai laifi a duk inda yake a hukunta shi and ga kud’in da muka samu a d’akin” ya k’arasa gaban Al’ameen ya ajiye jakan.

“Ku d’auka bana bukata ” yace Yana juya musu baya.

Matsowa d.o.p yayi yana…” A gaskiya yallabai ba zamu iya d’auka ba saboda….”

A harzuke ya juyo yace….” Nace ku d’auka in bakwa so ku jefar a hanya is not my problem but pls leave me alone “.

Alhaji ne yasa baki yace su tafi kawai tunda yace baya so.

D.p.o yace…” Shikenan Alhaji mun gode zamu tafi mu cigaba da bincike”.nan suka juya suka fice,constable sai murna suke kaman suyi tsalle ganin makud’an kud’in nan ance ya zama nasu.

Suna fita Al’ameen ya dawo da duban shi kan Lateefa da ta gama shan jinin jikinta yace…” Kina wani cewa kin cuce mu toh ki sani bamu kika cuta ba face kanki kuma ba wajan Mu zaki nemi gafara ba sai wajan mahaliccinki Dan shi sab’awa ba wani ba,anan kuma a gaban kowa zan fad’a in Al’ameen na saki Lateefa saki 3….”

“Kai!!! Haka da hankali ne” Alhaji ya katse shi a tsawace.

Hajiya ce tayi saurin cewa…”haba ya zaka hana shi?wannan shine dai-dai da ita sai taje can ta samu irinta ta aura ba dai d’ana ba wallahi kuma tsakanin Mu dake Allah ya isa macuciya kawai”.

Tana gama fad’anta ta fice a zuciye,alokacin ita da Alhaji ne kawai suka saura Dan Al’ameen da yayun shi sun dad’e da barin d’akin.

Alhaji ma fita yayi ba tare da yace komai ba saboda shima hukuncin yayi mishi dai-dai ya dai yi magana ne kawai a matsayin shi na babba a wajan.

Mama kanta a k’asa tayi shiru ba tace komai ba har suka gama ficewa a d’akin suka bata daga ita sai ‘yar ta.

Ita kanta abin ya bata mamaki da takaici dan duo shekarun nan bata tab’a sanin wannan mummunan halin ‘yarta ba,ta d’auka tunda tayi aure ta watsar da komai a titi ashe abin ba haka yake ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button