UKUBAR KISHIYATA Page 41 to 50 (The End)

Jiki a mace Mama tace…”ina su Fa’iza ban gansu ko basu san abinda ya faru dake ba?”
Murmushin takaici tayi sannan ta bawa Mama labarin abinda ya faru dasu.
Kuka Mama take sosai irin kukan nadama nan.
Lateefa tana kallonta tace…”lokacin kuka ya wuce Mama tunda kece sila na duk wani rayuwa da muka tsinci kan mu a ciki,run farko me kika lalata mana rayuwa Dan muddin zamu kawo miki kud’i ba ruwanki komai ma muyi gashi yau wa gari ya wayewa? ‘Yan Mayan ki 2 sun halaka ni da nake rayen ma gwara mutuwata kan rayuwar da zanyi a gaba”.
Mama kass cewa komai tayi sai kuka da take rizga saboda ita tasanmaganar da Lateefa ta fad’a gaskiya ce da hannunta ta watsar da yaran ta gashi yau duniya da rayuwar sun juya musu baya.
******************
Driving yake cike da nishad’i sun taso daga night club ya d’an kalli inda take yace…” Swthrt yau jina nake wani fresh dani”.
Dariya tayi tare da k’wantar da kan ta akan kafad’an shi tace…” Nima haka nake ji my love yanzu said Mu bud’e sabon rayuwa da zunzurutun kud’i naira million 150″.
Dariyan mugunta ya k’washe da ita yace…”kuma a banza muka same ta ba?”
Hirar su suke sosai cikin jin dad’e har suka zo gidan su.
Masu gadi har 2 sukayi rige-rigen bud’e musu gate suka wuce ciki.
Wanka suka fara yi sannan Aina’u ta jera musu abinci akan table.
Bayan tayi serving d’in shi yace…” Me ba zaki ci ba?”
Girgiza kai tayi tace…” Zuciyar ta tashi take ba zata iya cin abinci ba ruwan Lipton zata sha tasa ruwa a kettle.
Salees ya fara cin abinci suna hira yanda gobe zasu kai kud’ad’en su bank.
Aina’u tace…” My love dole Mu raba k’afa in ba haka ba akwai matsala.
D’an dariya Salees yayi sannan ya d’auki ruwan dake gaban shi ya shanye tare da ture gutun abincin da yake gaban shi ya dube ta yace…” Me meye tabbacinki na zan sure ki da har kikayi saurin amincewa haka?Ku mata k’wak’walwan Kifi ne daku,ita da taci amanar mijikin ta ta fifitani akanshi bai hana ni ci mata mutunci da wulakanta ta ba sai ke?kema kin San banida mutunci ko kad’an more especially akan money”
Murmushi Aina’u tayi tana kallon shi ko d’ar babu azuciyar ta tace…” Na sani ba sai ka tuna min ba kai kare ne mara mutuncti how can I trust u? But tunda kaci abincin nan plan na ya taxi dai-dai saboda ko 10mins ba zakayi a raye ba balle evil plans d’inka suyi aiki a kaina” ta k’arasa tana yi mishi dariyan mugunta.
Dariyan shima ya cigaba da taya ta dashi yace….” Wow!!! Kin birge ni sosai but u re too late “.
Had’e rai yayi kaman ba shine yake dariya yanzu ba
Pistol ya zaro daga aljihun wandon shi kamin Aina’u ta ankara ya d’auke goshin ta dashi.
Nan Aina’u ta fad’i ko shurawa ba tayi ba.
Tashi yayi yazo gaban trolleyn kud’in ya bud’e ya durkusa a gaban yana dariya yana shafa kud’in yana aiyana yanda plan d’in shi ya tafi kaman yanda ya tsara saboda yayi imanin Aina’u a yanda take matukar son shi ba zata iya Sa mishi wani abu a abinci ba.
Tari ya fara yi babu kakkautawa jini ya fara fitowa daga baki da hancin shi.
Nan ya fad’i yana shure-shure mutuwa ko minti 2bayi ba ya sandare a wajan .
Parlour ne ya fara tururin hayaki ,ruwan zafin da Aina’u ta saka a kettle ya kone adalilin haka wuta ya kama gadan.-gadan.
Kamin masu gadi su ankara had wutan yaci karfin gidan.
Fire fighters sunyi nasaran kasbe wutan amma Aina’u da Salees sun zama toka.
Lateefa da Mamar ta sun koma zariya sakamakon Koran kre da akayi musu daga asbitin Ya Sa’ad.
Lateefa taga rayuwa kasancewar ta zama mai larura ga rashin hannu ga gyabonta da kullum k’ara gaba yake dan haka a waje tske k’wana Mama taki yarda su k’wana d’aki 1a Cesar ta zata iya mutuwa in suka zauna wake 1.
Ko tana nema taimako ba mai taimaka mata duk sanyi da iska hard a damina akan ta suke k’arewa,in mutum ya ganta sai ya rantse da Allah ba Lateefa bace ‘yar k’walisa tayi kuka har ta saddakar.
Yanzu sosai abin nata yayi gaba saboda har kayan cikinta ya tab’a bata iya ci balle sha.
Tana jefe a cikin gidan sauro ba mai kula ta had tsutsosi saida suka fara cinyeta.
Kwana 2Mama bata ji motsinta ba tazo ta duba ta taga ashe rai yayi halin shi da dad’ewa dan harta fara kumburi.sakamakon in da gyambon ta yake fitarwa shiyasa basu lura da mutuwar ta balle suji warin gawa.
Allahu Akbar!!! Shiyasa ake so mutum ya shuka khairi in kayi akasinta kuma tun a duniya zaka fara gani kamin muje kiyama.duk abunda mutum zaiyi ya tuna akwai Allah yana ganin mu kuma mu kuma mutuwa dole zata riske Mu ko kana so kp baka so.Dan haka Mu koyi rungumar kaddara a rayuwa mai dad’i ko akasinta Mu kai zuciya nesa.*ALLAH KA SHIRYA MANA ZUKATAN MU AMEEN.
Al’ameen sabuwar rayuwa mai tsabta suke shida Ameerar shi da k’yawawan twins d’in su hankali k’wance.
Duk Wanda ya gan shi zai San ya canza daga Al’ameen d’in baya.
Iyayen shi sunfi kowa farinciki saboda kullum said yaje ya gaishe su ga ‘yan uwan shisuna zumunci sosai bakaman da sai sunyi kusan shekara basu ganshi a gidajen su ba.
Katafaren Gida Nagani na fad’a ya ginawa iyayen Ameera suka koma, aciki akayi auren Fateema,ta samu miji na gari a can garin gombe ba laifi shima yana da rufin asiri rayuwar suke gwanin sha’awa.
Matan Yayun Al’ameen su duka 3 suka kawo musu ziyara da yaransu suka wuni har dare mazajen su suka zo d’aukansu .
Nan ma suka dasa Sabon hira sannan suka raka su har bakin mota,basu bar wajan ba har saida suka ga tafiyarsu.
Shigowa parlour sukayi tare da twins d’insu da suka k’ara girma da wayo nan suka zube kan kujera Ameera tace…”wash na gaji”.
Hararan wasa ya aika mata yana…”gaya min aikin da kikayi harna gajiya”?
Cike da shagwab’a tace” haba Yayana ai wayan nan ma sun isa su gajiyar da mutum” ta k’arasa rana nuna twins da hannu.
“Kuma fa hakane amma kin san me? Ya kamata ace suna dak’ani”. Yace yana d’aga mata gira 1.
” kani!!! Haba wallahi saina huta”.
“Wani Hutu kuma yara sun kai 3 years?” Yace yana tsare ta da ido.
Cunno baki tayi ta juya mishi bata tana…” Ni kam ban shirya ba”.
Dariya yayi yana..” zaki ga shiryawa yarinya”.
K’iran twins yayi yace suje wajan Rabi ta basu ice cream su sha.
Da gudu sukayipart d’in masu aiki suna tsallen murna.
Tana ganin haka tasan nufin shi dan haka da gudu ta tashi tayi hanyan part d’inta tana dariya
Shima mara mata bata yayi yana dariya yana “baki isa ba yarinya” kamin ta kai har ya kamo ta ya daga ta sama yana juyi da da ita suna dariya.
*tammat bi hamdullilah*
Alhamdulillah INA mika godiya ga rabbi da ya nuna min karshen novel d’ina lafiya kaman yanda na fara shi lafiya.
Ina godiya gare Ku my fans na yanda kuka rinka bibiyar novel nan tun daga farko har karshen ta.INA mai Baku hakuri akan masu msg both fb and watsapp in kuka ga banyi reply ba toh abinne yafi karfina amma ina son Ku Sani INA kaunar Ku sosai fiye da tunanin saboda in babu Ku babu ni luv u all.
My special thanks goes to big brother *UMAR DALHA*
Godiya da jinjina zuwa ga *SIS NABEELERT* golden pen tana matukar alfahari daku without u guys things seems to b difficult..
Ban manta daku ba yan *GOLDEN PEN* kun amsa sunan Ku golden saboda yanda kuke haskawa a ko INA kun fita daban Allah ya kara baseera da karfin ido.
At d end INA rokon Allah daya nuna mana azumi lafiya tare da wadata Ameeen.