UKUBAR KISHIYATA 1-END

UKUBAR KISHIYATA Page 41 to 50 (The End)

Ranan suna yara suka cika sunan parents d’insu wato Mudassir mai sunan Alhajin Al’ameen sai Hadiza wacce taci sunan Umma Ameera.

Anyi shagali kaman ba gobe an bawa naira kashi sosai kowa da yazo sunan sai ya tafi da katuwar jaka cike da gifts.

Ameera da twins suma sun samu gifts daga ‘yan uwa kala-kala.tun daga kan uban gayya wato Al’ameen,iyayen shi da ‘yan uwanshi wanda ya kara hura wutan tsana su a zuciyar Lateefa..

Bayan suna da k’wana 2 Umma tace zata tafi da Ameera gida wanka.

Bori Sosai Lateefa ta tayar wai za’a rabata da ‘ya’yanta harda kukan munafurci.

Ganin yanda ta dage yasa Umma tace toh su zauna ita da Fateema kuma zata turo da Gwaggonsu ta cigaba da yi nata wanka.

Lateefa ba haka taso ba,taso ace ita kad’ai aka barwa Ameera da yaranta yanda zataji dad’in b’atar dasu ba tare da wani ya ankara ba.

Ta wani side kuma taji dad’i tunda komai zasuyi a gabanta za’ayi.

Kusan kullum a part d’in Ameera take wuni ana hira da kula da twins tare da ita. 

Sosai Gwaggo take jin dad’in zama da ita kuma take yabonta harta kai tana yiwa Ameera fad’a tabi ta su zauna lafiya dan a wannan zamani kamin ka samu mace kamar Lateefa sai an tona.

Shiru kawai Ameera take in taji Gwaggo tana irin wannan magana saboda ko tayi niyyan fad’awa Gwaggo halin da take ciki a sanadin Lateefa sai taji kaman ansa super glue an like mata baki.

Satin ta 2 da haihuwa babban jikan Gwaggo ya rasu ta tattara zata tafi zaman makoki Fateema ta rakata suka tafi tare.

Gida Fateema ta wuce daga gidan rasuwan wai tayi missing Ummanta.

Wuni tayi a gida suna hira da Umma sai bayan 5 tayi shirin komawa gidan Ameera nan Umma ta had’a mata kayan gyara tare da jadddawa Fateema ta fad’awa Ameera ta kula da kanta.

Da zata tafi Abba ya kawo ruwan Addu’a ya bata yace ta kaiwa Ameera su sha ita da yaranta kullum da safe kamin taci komai kuma in zasu k’wanta su shafa jikinsu dashi harna tsawon k’wana 7.

Fateema tana zuwa tayi mata bayanin kayan da Umma ta bata dalla-dalla sanna tayi mata bayanin ruwan addu’an.

A ranan suka fara amfani dashi har zuwa k’wana 7 kaman yanda aka umarce ta.

Kuma a ranan Fateema ta had’a kayanta zata koma gida soboda zasuyi resuming school.

Da daddare Al’ameen ya maida ta gida bayan sun cika ta da sha tara na arziki harda Lateefa wacce farinciki ya cika mata ciki sun watse sun bar Ameera zata cika burinta cikin sauki.

Da washe gari da safe Ameera tana shirin yiwa Fadeel da Fadeela wanka( sunan da Fateema ta zab’awa twins a rinka kiransu dashi kenan)su Fa’iza da Shamsiyya sukayi sallama suka shigo.

Amsawa tayi tana mamakin wai yau ita su Fa’iza kewa sallama.

Gaisheta sukayi ta amsa still a mamakince.

Fa’iza ta tambaya “ina twins ne?”

“Gasu can a cikin gadonsu yanzu nake shirin yi musu wanka”.

Shamsiyya tace …” Dama Aunty ce tace ki kawo su tayi musu wanka”.

“Wanka kuma” ta tambaye su.

“Eh saboda ta tayaki ne yau taga bakowa Fateema ta tafi”. Fa’iza ta amsa mata.

Kaman zata kara cewa wani abu kuma sai tayi shiru.

Wani k’aramin basket d’insu ta d’auko tasa kayansu kala 2-2 dasu diapper,su mai,powder da sauran kayan amfaninsu ta mik’a musu .

Shamsiyya ta d’auki Fadeel,Fa’iza kuma ta d’auki Fadeela suka fita.

Suna fita direct part d’in Lateefa suka wuce dasu,dama tana zaune tana jiransu.

Da sananin murna ta karb’i yaran tayi ciki, su kuma suka fita zasu tafi gidan binta tare da mamakin canzawar Auntyn nasu.

 

Ruwan sanyi Lateefa ta tara a bathtub sannan ta saka yaran aciki ta barsu suna ta tsala kuka kaman ransu ya fita.

Tana dariya ta fito parlour ta kira Aina’u tace…” Gasu can na saka su a cikin ruwan sanyin kaman yanda kika ce”.

Dariya Aina’u tayi tace…” Kai Besty baki da wasa wallahi yanzu kukan sune nake ji haka?”

Dariyan itama ta shek’e dashi tana…” Ta ina zanyi wasa da wannan babban dama da na samu”.

” gaskiyane yanzu saura step 2″ inji Aina’u,suka sa dariya a tare.

Tana gama wayan ta koma wajansu duk sun galabaita ba bakin kukan sai idonsu da yake a lumshe.

Fito dasu tayi a cikin ruwan ta dawo d’aki ta k’wantar dasu a kan tiles babu kaya a jikinsu balle ta lullub’e su da towel.

Kara karfin a.c d’akin tayi ta fito parlour ta k’wanta bayan ta kulle k’ofan harda murza key.

Ameera tunda aka fita da yaranta taji sam hankalinta bai k’wanta ba.

Bayan tayi wanka ta shirya ta d’an kishingid’a akan 3 seater tace bari ta bada 10 to 15 mis in basu dawo dasu ba zuwa zatayi ta karb’o kayanta.

Tana k’wanciya wani bacci mai nauyi yayi gaba da ita sakamakon jiya daddare Al’ameen ya hanata bacci da wuri da fitinan shi dama kaman jira yake Fateema ta tafi.

Bayan good 2 hrs Lateefa ta tashi cike da d’aukin ganin halin da suke ciki ta bud’e k’ofan ta shigo.

Farinciki fal zuciyar Lateefa ganin basa motsi.

Turus tayi tana kallon yanda suke fitar da numfashi a hankali da alama baccin su yayi nisa.

Cike da takaici take tsaye akansu tana tunanin abinyi wata zuciyar tana bata shawaran ta shake su kawai su mutu ta huta amma wata zuciyar ta hanata.

Basket d’in kayan su ta jawo tasa musu diaper da kaya ko mai bata shafa musu ba ta fito tana k’walawa Ameera kira.

A nan parlour sukayi clashing da Ameera da farkawarta kenan kuma ta fito neman yaranta .

Mik’a mata su tayi tace …”wuce kije ki basu nono yunwa suke ji”.

Ameera tana karb’ansu taji jikinsu sanyi kalau kaman kankara.

A razane ta d’ago tana kallon Lateefa wanda har saida itama Lateefan ta firgita jin tambayar da Ameera tayi mata.

” meye ya faru dasu naji jikinsu sanyi kalau haka”Ameera ta tambaya tana kallonta.

Wani yawu Lateefa ta hadiye na mamaki had’e da tsoron me yake shirin faruwa a gidanta.

Cikin inda-inda tace…” Ke ni kikewa tambayan rainin wayon nan?”

Murmushi Ameera tayi tace…” Ki sani ni Ameera ba zan tab’a zuba miki ido ki cutar min da yara ba,amma in kina ganin zaki ita toh bismillah kuma ina tabbatar miki in har wani abu ya samu yarana hmmm” tana gama fad’an haka ta juya tayi part d’in ta da yaranta ko d’ar babu a zuciyarta bata san dalilin da yasa ta rage tsoron Lateefa ba Dan cikin 100℅ 70℅ ya ragu.

Lateefa kam daskarewa tayi a wajan ko yatsanta ta kasa motsawa dan bata gama yarda wai Ameera ce ta gaya mata wa’yan nan magagganun ba.

????????????????????????

*UKUBAR KISHIYATA*

????????????????????????

(Its all about love and betrayal)

Story by *~UMMEE YUSUF~*

  (Maman Yusuf)

*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*????????????

❄~*we bearer’s of golden writer’s assiduously percieven No pain so Magical our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*forty two*

Lateefa da k’yar ta dawo hayyacinta tana tambayar kanta meke faruwa ne?

Juyawa tayi cikin sauri ta koma part d’inta tare da dannawa Aina’u k’ira.

Bai dad’e yana ringing ba ta d’aga tana cewa…” Nasan kin kira ne dan bani good news,yah sun shek’a?”

Lateefa a hasale tace…” Ke yi min shiru wani good news zan baki yara da shegen taurin rai,ba abinda ya same su lafiyarsu k’alau.ni ba wannan ba yarinyan nan wai yau har ita take kallon tsakiyan idona ta gaya min magana”.

” wacce yarinya kuma kika samu?”Aina’u ta tambaya.

A zuciye Lateefa ta amsa mata da…” Wace yarinya kuwa banda wannan ‘yar iskan gidan nan,akan way’an nan b’erayen nata ta dubi cikin idona tace in wani abu ya same su in kuka da kaina”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button