UKUBAR KISHIYATA Page 41 to 50 (The End)

” wai Ameeran ce tace miki haka?”Aina’u tace cike da mamaki.
Kwafa kawai Lateefa tayi ba tare da tace komai ba.
Aina’u ta cigaba cewa…”lalle akwai matsala dole mu koma wajan boka but before then ya kamata ki koyawa shegiya hankali kamin in dawo muje dan yanzu haka ina hanyan zuwa Kano nida Alhaji nura amma k’wana 2 kawai zanyi,ki nuna mata ko ba boka kinfi karfinta”.
Cike da k’warin guiwa Lateefa tace…” Off course wallahi ubanta zanci a gidan nan dole tasan ni Lateefa nafi karfin uwarta bare ita useless da ita”.
Shawara sosai Aina’u ta bawa Lateefa wanda yasa mata natsuwa da courage akan gallazawa Ameera sannan suka rabu akan sai tazo jibin.
Ameera tana shiga part d’inta ta hada ruwa mai zafi sosai tayi musu wanka dashi tare da shafa musu baby oil jikin su sosai sannan ta saka musu kayan sanyinsu,ta had’a musu madara ta basu suka sha suka koma bacci.
Saka su tayi agaba tana kallon yanda suke had’a gumi a goshinsu,sai a lokacin hankalinta ya k’wanta.
Tana zaune tana accusing kanta meye dalilinta na basu yaranta bayan tasan ba k’aunarta suke ba bare abinda ta haifa.
A yanda take jin yaranta a cikin ranta zata iya yin komai kuma da kowa da yayi niyar cutar mata dasu.
Har dare basu had’u da Lateefa ba ko wacce tana part d’inta.
Al’ameen yauma ya shigo da daddare duk suka isheta da fitina da shida twins,bata samu bacci ba sai kusan asuba.
Koda tayi sallahn asuba komawa baccinta tayi tare da tura Fadeel da Fadeela wajan Rabi dan tayi musu wanka.
Tana tsakiyan baccinta kaman daga sama taji saukan ruwan sanyi a jikinta Wanda yayi sanadin farkawarta agigice.
Lateefa ta gani tsaye a kanta rik’e da k’ugu tana girgiza cike da masifa.
Tashi Ameera tayi tana gyara zaman Rigan bacci ta.
Lateefa ta fara zuba mata ruwa bala’i.
“Samun guri da k’wanciyar hankali,iyyeh har baccin safe kika samu yanzu Dan kinga k’wana 2 ina d’aga miki k’afa kina jin kanki kamar wata toh bari in gaya miki as from now hutun da na baki ya kara daga yau zaki dawo bakin aikin kamar yanda kike da.ki wuce yanzu ki had’a min breakfast kuma 5 mins na baki just 5mins ko minti d’aya kika k’ara akai kema kinsan sauran”.
Tunda ta fara magana Ameera take kallonta tana mamaki .
Ganin ta ida masifarta yasa itama ta shanye nata mamakin ta fara maida mata martani.
” na farko ke wacece wama ya baki izinin shigo min har bedroom saboda rashin tarbiya,maganan ina d’aukan kaina ni wata ce kinyi kuskure anan ni ba wata bace amma ina da matsayin da wasu suna nema da milliyoyin kudi amma basu samu ba,ni UWACE nayi miki gya…”
Lateefa al’ajabi ya gama daskar da ita ta NASA cewa komai sai ido da ta zuba mata amma kalamanta na karshe su suka harzuk’ata har ta d’aga hannu da niyan marinta amma Ameera tayi caraf ta rik’e hannun.
Tana murmushi tare da girgiza mata kai tace…” Don’t ever make this mistake in ur life saboda in har baki rik’e girmanki ba ni kuwa zansa k’afa in taka ta”tana gama fad’an haka tayi jifa da hannun abinka da mai kib’a tayi tangal-tangal ta fad’a kan stool din gaban mirror Ameera har ta na buge goshinta.
Ameera ko kallonta bata k’arayi ba ta fad’a bathroom tare da bango mata k’ofa da karfi.
Lateefa jiki duk jiki yayi yayi tsami more especially goshinta har ya taso haka taja jiki ta fice mata a daki.
Al’ameen mamaki fal a ranshi wai Ameera ce tayiwa Lateefa haka,tayaya hakan ta faru?amma can k’asan zuciyar shi kuma dad’ine fal.
Basarwa yayi yana wani yamutsa fuska yace..”wacece haka sabuwar ‘yar aiki kika samu?”
Farinciki ne ya lullub’eta ganin har yanzu asirin bai bar jikin shi ba.
” ka kirata yanzu ka korata gidansu dan nagaji da ganinta cikin gidan nan”.ta fad’a in a commanding way.
Mik’ewa yayi ya nufi hanyan part d’inshi yace…”tunda a karkashin ki take ke ya kamata ki Kore ta bani ba dama me kike d’ebo ‘yan aikinki”.
Takaici duk ya cikata ta rasa ya zatayi can wata zuciyar yace ta k’ira k’annenta su dawo mana tasan su zasu iya maganinta.
Nan take ta k’ira Shamsiyya tana d’auka ta fara sauke mata bala’i da take dannewa a ranta.
“Bansan wani irin hankali gare Ku ba,in banda shashanci daga yiwa k’awarku aure sai kuje Ku tare mata a gida haka akeyi?toh ina gaya muku duk abinda kuke Ku bari Ku dawo gobe ina nemanku kuzo Ku min maganin k’aramar ‘yar iskan gidan nan”.
” Aunty wa kike nufi wai kuma meya faru?”
Nan ta basu labarin abinda ya faru tsakaninta da Ameera.
Fa’iza sai huci take har ji take kaman ta faso ta cikin wayan .
Hakuri suka bata suka ce gobe da sassafe zasu shigo su gyara mata zama.
Al’ameen daya sauk’o k’asa yaga Lateefa ta tashi bata parlour,bai tsaya bata lokaci ba ya fad’a part Ameera ya same ta tanawa babies d’inta wasa hankali k’wance .
K’arasowa yayi ya zauna tare da sa hannu ya d’auki Fadeela ya fara mata wasa yace….”Maman twins kin ganki kuwa kullum k’afa k’yau kike meye sirrin ne?”
Ajiye Fadeel tayi ta juyo gare shi haba d’aya tana fuskantan shi…” Kaine sirrin Yayana”.
Kanne mata ido d’aya yayi yace…”kin tabbata?”
Dariya tayi tana gyad’a mishi kai.
Zama yayi sunsa yaransu a tsakiya suna ta hira,anan yaci abincin shi na dare.
Shi bai koma part d’inshi ba sai bayan sallahn asuba.
Wanka yayi ya shirya ya fita office.
Ameera zama cikin d’aki ita kad’ai ya isheta,yau suka fito ita da yaranta main parlour dan shan iska.
Canza channel tayi daga MBC Bollywood zuwa saudi2 tana sauraron karatun alqur’ani.
Bata dad’e da zama ba Lateefa ta fito tana yamutsa fuska.
Daram zuciyarta ya buga da karfin gaske ganin Ameera ta baje tana kallo.
Tana son tanka mata amma wata zuciyar ta hana ta ,kar ta gama zubar da ajinta bari ta hira zuwan su Fa’iza.
Kan dinning ta wuce ta fara breakfast tanayi tana satan kallon Ameera da take harkokinta ta d’auke kai kaman bata san da ita ba a parlour.
Tana mamakin yanda abin ya juye lokaci 1 haka kaman ba Ameerar da bata iya mata magana sai a duke ba kamar ba Ameerar da in ba cewa tayi tashi anan ba bata isa ta motsa ba kaman ba Ameerar da…shigiwar su Shamsiyya shi ya katse mata zancen zuci da take.
Suka wuce Ameera suna mata kallon banza ita ko ta bawa banza ajiyarsu.
Bayan kus-kus da sukayi da Auntynsu suka nufo ta gadan-gadan dai-dai lokacin kuma Fateema tayi sallama ta shigo.
????????????????????????
*UKUBAR KISHIYATA*
????????????????????????
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*????????????
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*
*_~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~_*
*part forty three*
Shigowan Fateema bai hana su Fa’iza k’arasowa gaban Ameera ba kowacce tana k’okarin kai mata bugu.
Da gudu Fateema tazo ta shiga tsakaninsu tana…”me zan gani haka wani irin dabbobi ne ku?”
Ameera ko k’ala bata ce musu ba saida ta k’washe yaranta ta kaisu safe place sannan ta dawo ta samu har sun fara gabazawa da Fateema,Lateefa tana gefe tana suyi kasa-kasa da ita sannan su bi Ameera data gudu.
Ameera tana zuwa batayi wata-wata ba ta finciko Fa’iza ta gashin kanta da yasha Brazil.