UKUBAR KISHIYATA Page 41 to 50 (The End)

Ihu Fa’iza tasa tana neman k’watan kanta amma ta kasa ga bakinta yaki mutuwa sai zagi take aikawa Ameera.
Buge bakin zagin Ameera tayi da iya karfinta sai ga bakin yana tsiyayan jini,wancalar da ita gefe ta fad’a kan glass center table.
Kasa tashi Fa’iza tayi illa dafe goshinta tayi da yake ta zubar da jini tana kula.
Tana juyowa d’ayan side sai ganin Fateema tayi ta haye ruwan cikin Shamsiyya sai bugu take kai mata kota ina.
Murmushi Ameera tayi ta juyo arean dining inda Lateefa take zaune.
Suna had’a ido Lateefa ta mik’e jiki na b’ari tayi hanyan part d’inta dama a tsorace take tana mamakin wani irin karfine dasu duk sun raunata mata k’anne.
“Ina zaki je?ki tsaya ki nuna min jarumtar ki,ki tsaya nace”.Ameera ce ke fad’an haka lokacacin da ta bin bayan Lateefa da gudu.
Tsantsin tiles ne ya k’washi Lateefa sai gata tayi zaman ‘yan bori a kasa.
Dakewa tayi ta juyo ga Ameera duk da a tsorace take hakan bai hana ta fara cika baki ba harda zagi…”Dan ubanki karki ga ina kyale ki ina nan a Lateefa ta da kika sani ba zan tab’a canzawa ba Kuma dole ki kasance a karkashin iko na in mulke Ki dan Abu Kazan ubanki..”
Ameera batayi niyyana tab’ata ba amma jin zagin da take antayo mata yasa ta jawo wire receiver da yake gefen kayan kallonsu ta shiga lafta mata ta ko ina.
Lateefa duk iya kokarinta na ganin ta kare kanta kasawa tayi.
Ganin in batyi da gaske ba zata sha wiya,hankad’a Ameera tayi da duka karfinta tayi hanyan part d’inta da gudu.
Tsayawa Ameera tayi tana dariya har da fad’uwa kan kujera ganin yanda Lateefa take k’wasan gudu jiki na rawa.
Da k’yar ta d’aga Fateema akan Shamsiyya da tasha mazga.
Zama Fateema tayi tana huci tace…” Wallahi Aunty ke kike sake musu har suke k’okarin tab’a lafiyarki,wallahi kun ci sa’a yau ina cikin mutunci if not hmmm mayu duk kunsa min ‘yar uwa a gaba ganin ba abinda ‘yar uwarku ta iya sai katon kashi.”
Ameera dai dariya take tayi mata tace…” Haba Fateema duk suburbud’an da kika yi mata kike cewa haka?”
Fa’iza da Shamsiyya da k’yar suka ja jikinsu suka fece daga gidan gaba d’aya ba tare da kowa ya lura dasu ba.
Lateefa tana cikin d’aki sai kaiwa da komowa take ta rasa me yake mata dad’i a rayuwa jikinta duk yayi rud’u-rud’u da shatin wire.
Waya ta d’aga ta k’ira Aina’u tasa mata kuka.
Hankali tashe Aina’u take take tambayar ta me yake faruwa?
Da’kayar ta tsagaita kukan ta bata labarin abinda ya faru dasu yanzu.
Ashar Aina’u ta fara d’urawa tana kunfan baki tace yau d’in nan zata taso wallahi sai sun koya mata hankali sannan su koma wajan boka yayi maganinta.
Da washe gari da sassafe Lateefa ta fita sannan ta k’ira Aina’u tace ta fito tazo su wuce.
Bata wani dad’e ba tazo ta same ta suka tafi.
******************
Dariya boka ya bushe da ita yana kallon yanda Lateefa da Aina’u sukayi tsuru-suru suna sauraron shi.
” dukansu 2 kike son akashe?”
Da sauri ta amsa da…”eh boka dan rayuwar yaran nan tashin hankaline a gare ni”.
“Za’a kashe su duka amma ba yanzu ba sai mun tura bak’ak’en aljanu suyi ta azabtar dasu zuwa shekara d’aya sai a kashe su,kin amince da wannan shawaran?”
Cikin jin dad’i ta amsa..” Na amince boka dan ni hakan ya min dad’i sosai kuma boka ina son a mantar da Al’ameen yaran nan da ita uwarsu gaba d’aya”.
Wani d’an k’aramin sanda da aka laulaye shi da guraye ya mik’o mata yace…bansan ya akayi kikayi sake har tasha abinda ya karya kusan duka sihirin da yake jikinta ba kuma a halin yanzu ba wani aljani da zai iya tunkarta saboda haka ki samu dama ki ajiye mata wannan sandan a karkashin gadonta kuma ki tabbatar a k’wance kika ajiye shi”.
D’an dakatawa yayi sannan ya cigaba…”ina gaya miki koda yayi satan k’afa ya shiga d’akinta toh ba abinda zai iya tsinana mata balle harta k’ara haihuwa a gidan”.
Farinciki mara misali ne ya lullub’e Lateefa jin abinda boka yace mata.
Godiya suka mishi tare da tula mishi mak’udan kud’i suka fito.
Lateefa bata samu tangard’a wajan aiwatar da duk wani sharad’i da boka ya bata ba komai ya tafi dai-dai yanda take so.
Aikin boka yayi k’yau as usual dan yanzu Al’ameen ya manta hanyan part d’in Ameera balle ita da yaranta..
Haka Ameera take rayuwarta da yaranta duk da rashin kula da Al’ameen yake musu yana damunta amma ta daure tana sha’aninta.
Lateefa tunda tasha suburbud’a a hannun Ameera bata k’ara shiga harkanta ba,hankali k’wance take jiran time d’in da boka ya bata yayi taje a gama mata dasu.
Fadeel da Fadeela yau kusan suna da 6 months amma in ka gansu zasu baka tsoro saboda kamanninsu gaba d’aya ya canza ko zama basu iya ba sai mugun cin abinci.
Ranan wata talata Fateema ta kawo musu ziyara tare da fad’a mata auren ‘yar k’anwar Umma da za’ayi nan da 3 weeks.
Fateema tunda ta shigo take kallon yaran da damuwa a fuskanta tace…” Ameera ya nake ganin kaman abin nasu gaba yake dan last time da nazo kaman bai kai haka ba”.
Sauke ajiyar zuciya Ameera tayi da matuk’ar damuwa akan fusksnta tace..” Bansan ya zanyi ba Fateema hakan ma da kike gani da sauki dan d’azu nayi musu addu’a na shafa musu ajiki”.
“In na je gida zan fad’awa Umma ta fad’awa Abba yayi musu addu’a”. Fateema tace haka tana d’aukan Fadeela.
Girgiza kai Ameera tayi tace…” Karki fad’a musu ki tayar musu da hankali nafi son inje da kaina ya gansu”.
” shikenan ba zan fad’a ba Allah ya kaimu lokacin kije da kanji”inji Fateema.
Haka Fateema ta wuni mata sai yamma lis ta koma gida.
Ameera tana son fita zuwa bikin amma ta rasa ya zatayi taga Al’ameen ta tambaye izinin fita.
Ana gobe zata je bikin ta fito ta zauna a main parlor ko zata gan shi.
Tana nan zaune har bayan sallahn isha’i sannan tagan shi ya shigo dawowar shi daga masallaci kenan.
Suna had’a ido dukkansu saida zuciyar su ya buga a tare.
Ameera ganin duk ya lalace ya rame yayi baki kaman bashi ba shiyasa zuciyarta bugawa tana tunanin me yake damun shi ya lalace haka?.
Shi kuma ganinta da yayi yau shiya tuna mishi da ita a rayuwar shi.
Yana son sake kallonta amma yaji wani haushinta yake ji dan haka ya d’auke kai yayi hanyan part d’in shi.
Da sauri tace…” Yayana…” Tsayawa yayi can ba tare da ya juyo ba.
Ganin ya tsaya yasa ta taso da sauri tazo ta tsaya a bayan shi tace…”yayana meya faru ko ince me nayi maka ne ka yanke yi mana wannan babban hukuncin nida yaranka?”
Tafiyan shi ya cigaba dayi ba tare da ya tanka mata ba.
Hawayen idonta ta share tace..” Ina Neman izininka zanje gida gobe saboda muna da biki zanyi k’wana 2 kamin in dawo”.
Ware hannayen shi yayi irin who cares d’in nan ya k’arasa bakin stairs inda Lateefa take jiran shi da murmushin farnciki a fuskanta tace…” My Ameen meya had’aka da wannan idiot d’in?”
“Pls ki daina b’ata bakin ki akan useless thing my Lateefa”.
Dariya tayi suka haura sama suka barta nan tsaye tana hawaye.
Ranta bai tab’a b’aci akan halin ko in kula da Al’ameen yake musu kaman yau ba,toh me yake nufi da ita? In har ya daina sonta ne ya sauwaka mata ta koma gidan iyayenta ko zataji sauki.
Saida tasha kuka sosqi a wannan daren da k’yar ta samu bacci ya d’auke .
Da washe gari da sassafe ta tashi ta had’a musu kayansu a d’an k’aramin trolley.
9am sun gama shiri tafiya tsab.
d’aukin yau zata je gidansu yasa ko breakfast bata tsaya yiba su Rabi suka rakota da kayanta har wajan mota.