UKUBAR KISHIYATA 1-END

UKUBAR KISHIYATA Page 41 to 50 (The End)

Bala driver yana ganinsu ya taso da sauri ya fito da mota sannan ya karb’i trolley a hannun Rabi ya saka a boot sanna yaja mota suka fita su Rabi suna ta d’aga mata hannu cike da kewanta.

Bala yana parking a k’ofar gidansu ta fito tana mamakin yaushe aka gyara musu gidan ya koma haka.

Kota kan kayansu bata bi ba ta Shiga gida da matuk’ar sauri kaman ta kifa tare da k’walawa Umma k’ira.

Fateema ce ta fito da gudu suka rungume juna a zaure tasa hannu ta karb’i Fadeel suka karasa shigowa cikin gida.

Umma ta fito cikin farinciki daga kitchen inda take aikinta tana musu lalle marhabin.

Tabarma Fateema ta shinfid’a musu a bakin sabon parloursu suka zauna ana gaisawa.

Bala yayi sallama ya shigo da trolley su tare da gaishe da Umma sannan yayi musu sallama ya tafi.

Nan Ameera take tambaya ina Abbanta?Umma ta amsa mata daya tafi duba wani abokin shi da bashida lafiya.

Ajiye mata yaran sukayi suka shige d’akin Fateema data sha gyara tana bata labarin Ai Al’ameen ne yayi musu gyra nan.

Tunda suka shiga Umma take kallon yanda yaran suka canza kaman basu ba,ga Ameera itama duk ta canza kana ganinta zaka San tana cikin matsala ba sai an fad’a maka ba.

Cike da damuwa Umma ta k’wantar dasu ta koma kitchen ta cigaba da aikinta zuciyarta a cunkushe.

Ameera suna d’aki Umma ta gama jefa d’an waken da take ta k’ira Fateema ta kai musu d’aki suka faraci.

Sun kusa gamawa suka ji muryan Abba yayi sallama ya shigo.

Da matukar Murna Ameera ta fito da gudu tana yi mishi sannu da zuwa baki har kunne..

Abba cike da farinciki yake amsawa yana tambayarta yaranta.

Fateema ta shigo dasu tana “Abba ga takwaran Umma nan ita zaka fara d’auka”.

Suna had’a ido Fadeela ta callara ihu,yariyan da ko zama bata yi yau sai gata tana rarrafe tana Neman hanyan fita daga parlour.

Tsoro,figici da mamaki ya hana kowa tab’a ta illa zuba mata ido da sukayi.

Murmushi Abba yayi yana kallon Ameera da take hawaye yace…”mesa yaran nan basu da lafiya baki kawo min su ba?”

Cike da rashin fahimta Umma tace” wani irin rashin lafiya kuma Mallam?”

????????????????????????

*UKUBAR KISHIYATA*

????????????????????????

(Its all about love and betrayal)

Story by *~UMMEE YUSUF~*

  (Maman Yusuf)

*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*????????????

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*

*_~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~_*

*part forty four*

“K’warai kuwa amma ba haka aka haife su ba ko?” Abba ya tambaya yana kallon Ameera da take kuka.

Umma ce ta mishi bayanin yanda suke lokacin da aka haife su,nan Abba ya bukaci a shigo da Fadeel da yake bacci a waje.

Fateema ce ta shigo da shi a hannu,aiko shima suna had’a ido da Abba ya fara ihu amma shi baiyi yunkunrin guduwa ba.

Gyara zama Abba yace…”duk yanda akayi yaran nan da aljanu a jikinsu.

Jin haka duk suka kid’ime musamman Ameera da tasa kuka da karfi.

” Ku k’wantar da hankalinku zanyi musu ruquyya ba abinda yafi karfin ayar Allah”.

Cirko-cirko sukayi suna sauraron Abba.

“Fateema ki shiga d’akina ki d’auko min ruwan zam-zam,man zaitun dana habba ki kawo min”.

Fateema har tuntub’e take saboda sauri, cikin lokaci sai gata ta dawo dasu a hannun.

Abba cewa yayi duk su fita su bashi waje su jira zai fara.

Mik’ewa sukayi suka fita dukansu suna ta waiwayen su.

Suna fita Abba ya shafe su da man zaitun dana habba sannan ya fara karanto ayoyin alqur’ani mai tsarki da ake ruquyya dasu.

Wanda yake jikin Fadeela shiya fara wani irin ihu da murya mai rikitarwa yana rokon Abba da yayi hak’uri ya barshi ba laifin shi bane boka ne ya turo su.

Abba yace…” Akan wani dalili bokan ya turo ku kuke wahalar da jinjiraye?”

” Hajiya Lateefa matar babansu ita tasa aka turo mu muyi ta azabtar dasu har zuwa shekara 1 sannan mu kashe su”.

Abba ya jinjina kai ya kara tambayan shi yace….”iya abinda aka saka ku kenan koda saura?”

Murya a galabaice ya bawa Abba labarin irin tuggu da Lateefa ta shirya shekara da shekaru har zuwa yau,sannan ya roki Abba da ya yafe mishi karya kona shi zai fita kuma yayi alkawari ba zai sake zuwa ba.

Atishawa Fadeela tayi ta jerawa har 3 sannan ta bingire da baccin wuya.

Abba ganin Fadeela ta samu lafiya yasa ya maida hankalin shi gabaki 1 zuwa kan Fadeel daya zuba mishi ido ya mishi wani kallo kaman ya shake shi.

Irin kallon da yake mishi yasa Abba sanin cewa wannan yana da taurin kai,dan haka ruwan zam-zam daya sha addu’oi ya d’auko yana watsa mishi a jiki yana cigaba da karatu.

A tsawace yaji wacce take jikin Fadeel d’in tace…” Wai kai wani irin mutum ne mai nacin tsiya?gara ka rabu dani saboda ni duk nacinka sai dai kayi ka gama dan bazan fita ba sai na aiwatar da abinda aka sakani”.

Abba yace…”shikenan kada ki fita ni kuma zan kona ki da ayoyin Allah”.

Wani dariyan rainin hankali tayi irin na kayi kad’an d’in nan.

Karatu Abba yake yana zuba mishi ruwn zam-zam d’in,tun tana ganin Abba yayi kad’an ya k’ona shi har ta fara k’onewan.

Nan itama ta shiga magiyan Abba ya daina k’ona ta zata fita amma Abba yace shi bai yarda ba dan zata iya dawowa.

Alkawari tayi mishi in ta tafi ta tafi har abada kenan sannan Abba ya tsagaita da karatun da yake.

Atishawa masu karfi shima yayi ta jerawa sannan ya kama bacci kaman na ‘yar uwar shi.

“Alhamdulillah!!” Abba yake ta jerawa.

D’aga murya yayi yace suna iya shigowa.

Fuska shame-shame da hawaye suka shigo dama suna tsaye sun kasa zama suna jira.

Umma ta d’auki tak’warta tana share hawayen fuskanta da gefen zaninta tace…” Wannan mata me zamuyi mata ne muji sauki a cikin ranmu?”

” kul kar in kara jin haka daga bakin ki,mutum duk abinda zaiyi maka ka barshi da Allah dan baki ji sauran abubuwa da tayi bama”.

A hargitse Umma ta d’ago tana kallonshi tace…” Me kuma tayi bayan wannan?”

Nan Abba ya maimaita mata abinda d’ayan ya fad’a.

Kuma wiwi Umma take tana”Ashe wannan faram-faram da take mana na munafurcine? Oh mutum abin tsoro amma wannan mata Allah ya isa tsakanin mu da ita”.

Fateema ita ta fad’i abinda ta sani ciki harda dambe da sukayi Ameera ta hana ta fad’a.

Umma ta jawota jikinta ta rungume tana rarrashinta tace…” Ki yafe mana Ameera duk laifin mu da bama ziyartan ki kuma muka hana kowa namu zuwa gudun kada mutane suce an zuba k’afa a gidanki dan k’wad’ayi ashe kanmu muka cuta da matar nan batayi nasaran wukanta min ke haka ba.”

Abba ya katse ta yace…”ya isa haka nan komai da kuke gani muk’addarine na ubangiji,in Allah ya hukunta faruwan abu to dole ne sai ya faru.yanzu abinda nake so ku tashi ke Ameera ku koma gidanki keda Fateema ku rusa kayan d’akin duk abinda kuka gani kada ku tab’a ku Kira ni awaya”.

“Toh ” suka ce tare da mik’ewa nan Umma ma ta mik’e tace lalle tare zasu tafi kar wani abu ya samu ‘yan matan ta.

Abba yace ta zauna ba abinda zai faru tunda su aljanun da aka turo su dan aikin ma sun gudu toh komai ya k’are tayi hak’uri suje.

Haka Umma ta hak’ura ta zauna ba dan taso ba,Ameera ta goyi Fadeel Fateema kuma ta goyi Fadeela suka fita.

Har sun kusa bakin titi Ameera tace…” Dame zamu tafi dan ni ko naira banida shi”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button