UKUBAR KISHIYATA 1-END

UKUBAR KISHIYATA Page 41 to 50 (The End)

Fateema batayi magana ba ta juya ta koma gida can sai gata ta fito da d’ari 5 a hannunta suka karasa bakin titi tare da tsaida mai adaidaita suka shiga suka tafi.

Pls kuyi manage da wannan.

????????????????????????

*UKUBAR KISHIYATA*

????????????????????????

(Its all about love and betrayal)

Story by *~UMMEE YUSUF~*

  (Maman Yusuf)

*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*????????????

❄~*we bearer’s of golden writer’s assiduously percieven No pain so Magical our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain~*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*part forty five*

A bakin gate mai a daidaita ya sauke su,Fateema ta bashi kud’i ya karb’a tare da maida mata change sannan suka nufi cikin gidan.

Bala driver suna zaune da Baba mai gqdi suna hira suka shigo.

Da sauri Bala ya mik’e ya tare su yana..” Haba Hajiya da kinyi waya naje na dawo dake,in Alhaji yaji ba zaiji dad’i ba”.

Murmushi kawai tayi tace mishi…”bakomai Bala”.

Cikin suka shiga ba kowa a main parlour hakan ya basu daman shigewa part d’in Ameerar ba tare da kowa ya gansu ba.

A parlour Ameera suka k’wantar da Fadeel da Fadeela sannan suka wuce bedroom.

Cikin abinda baifi 20 mins ba suka warware gadon.

Mamaki da tsoro su suka daskar dasu waje d’aya ba wacce ta iya motsi cikinsu.

Can Fateema tayi karfin hali tace…” Bani wayarki in kira Abba in fad’a mishi abinda muka gani”

“Ba kud’i a wayan Fateema”.

” nima babu a nawa amma bari in fita in sayo yanzu ina zuwa”

Fateema tans fad’an haka ta d’auki change da mai a daidaita ya basu ta fita.

Bata jima ba kuwa ta dawo da recharge card na m.t.n.

Ameera tana nan tsaye a inda ta barta bata matsa ba.

K’iran Abba tayi bayan ta loda katin a wayarta.

Wayar tana shiga Abba ya d’aga da sauri dama yana zaune shida Umma ya kasa fita ko bakin k’ofa suna jiran k’iran daga gare su.

 ” Fateema kun samu me kuka gani?”Abba yake jerowa Fateema tambayar nan.

“Eh Abba abubuwa da yawa muka ga…”

“Kaman su me? Gaya min inaji” Abba ya katse ta.

Nan ta shiga lissafo mishi abinda suka gani tace…” Akwai layu guraye sanda harda rigar Ameera dana mijinta da wasu k’ulle-k’ullen magani”.

Abba yace…”kada ku tab’a komai ku fara yin alwala sannan ku karanta suratul Iklas,Falaq,Nasi da Ayatul qursiyyu ku shafe jikinku dashi,kusa tsintsiya da abin k’washe shara ku k’washe da shi ku fitar waje”.

Kashe wayan Fateema tayi ta ajiye a gefe bayan ta amsa mishi.

 Parker da dustbin suka d’auko suka fara k’washewa kenan wayar Fateema ya fara ringing.

Tsaida aiki sukayi Fateema ta amsa wayan taji muryan Abba yana cewa…” Ku kona duk abinda kuka fitar Fateema karku bar komai”.

“Insha Allah Abba ” tace sannan suka cigaba aikinsu.

Ta bayan gidan suka fita da kayan can arean su Rabi,wuta suka cinnawa dustbin d’in ba tare da sun juye surkullen a k’asa ba.

Wuta ya kama yana ci bal-bal ga wani irin hayaki bak’i kirin na tashi wanda ya k’ara firgita su Fateema da suka koma gefe d’aya suna kallo.

Wutan yana k’asa Ameera ta yanki jiki ta fad’i a wajan.

A rud’e Fateema tayi wajan Rabi tana cewa tazo ta taimaka mata.

Rabi tana tambayarta me ya faru amma Fateema bata tsaya bata amsa ba ta fita da gudu,ganin haka Rabi bata tsaya b’ata lokaci ba ta rufa mata baya.

Salati Rabi ta fara har tana tafa hannu tare da tambayar meya same ta amma ba amsa.

Haka suka ciccib’e ta sai cikin bedroom d’inta suka k’wantar da ita suna aikin fifita.

Ruwan sanyi Rabi ta shafa mata a fuska.

Ajiyar zuciya tayi ta bud’e ido a hankali tana binsu da kallo suna yi mata sannu.

Tashi tayi ta zauna tana tambayar Fateema meya faru?

“Bakomai just tiles ne ya k’washe ki kika fad’i” Fateema ta bata amsa tana b’oye hawayenta.

Kukansu Fadeela suka ji a parlour Fateema ta tashi ta d’auko su ta shigo dasu.

Ameera wasu abubuwa take ji kaman sun faru amma sai take gani kaman a mafarki ya faru.

K’iran Abba ne ya kara shigowa wayar Fateema,parlour ta fita sannan ta d’aga yake tambayar ta ya sukayi.

Abinda ya faru tun daga kan k’ona kayan tsafin harda fad’uwar Ameera duk ta bashi labari.

Godiya ga Allah Abba ya fara yi na Allah ya bawa ‘yar shi lafiya,nan yace mata ta kaiwa Ameera wayan zaiyi magana da ita.

Komawa cikin d’akin tayi ta bata wayan tace Abba ne zaiyi magana da ita.

Karb’a tayi taxa a kunne bayan tayi mishi sallama ya amsa ya shiga yi mata nasiha da fada akan rike addu’a da yin azkar saboda addu’a itace makamin mumini sai mutum yayi sake da azkar Sannan duk wani mugun abu zai iya shafar shi amma da mutum zai kiyaye kaman yanda manzon Allah (s.a.w) ya umarta toh bi izininllahi ya tsira sai sai wani ikon Allah.

Ameera sai amsawa take da toh sabida ita tasan bata wasa da azkar bata san tunda tasha juice d’in da su Fa’iza suka bata ta daina duk wani Abu mai suna addu’a ba.

Bayan sun gama waya da Abba ta dubi Fateema tace…” Fati Dan Allah ki gaya min me yake faruwa kaina ya kulle”.

Tiriyan-tiriyan Fateema ta maimaita mata iya abinda ta sani.

Rungume twins d’inta tayi tana kuka sai yanzu take gani ashe abinda take gani kaman a mafarki da gaske ya faru da ita.

Rabi ta dafa kafad’arta tace… ” Hajiya yanzu ba lokacin kuka bane godiya ya kamata kiyiwa Allah da ya warware wannan kulle mai wuyar warwara”.

Bayan sun natsu suka had’a gadon yanda yake suna hira da ‘yar uwarta tana jinta kaman wata sabuwar halitta.

Kitchen ta fito tana cewa Fateema ta kula dasu Fadeel zata sama musu abinda zasu ci.

Abinci mai sauki ta girka musu tayi musu pepper soup na kaza ta shirya a d’an madai-daicin tray ta d’auka zata fita Rabi ta shigo tana…”haba Hajiya ai da kinyi min magana zan girka muku duk abinda kuke so”.

Murmushi Ameera tayi tace…” Bakomai Rabi taimakon da kike min a baya ba abinda zance sai sai ince Allah ya saka mini da alkhairi”.

Tana gama fad’an haka ta d’auki trayn ta fita daga kitchen d’in Rabi ta rakata da murmushi.

******************

Al’ameen yana zaune a office aiki yasha mishi kai,Shu’aib sectaryn shi yana nuna mishi files yana signing.

Wani matsanacin ciwon kai had’e da jiri yaji ya ziyarce shi lokaci d’aya har wani duhu-duhu yake gani.

Dafe kan shi yayi da hannun dama har pen d’in hannun shi yana fad’uwa.

Tambayar shi Shu’aib ya farayi ko lafiya,maimakon ya bashi amsa sai gani yayi ya yanki jiki ya zube a wajan.

A rud’e ya fara k’walawa Massinger kira Wanda yayi sanadin Jan hankalin sauran mutane dake kusa da office d’in.

Mota suka saka shi suka nufi hospital d’in Yayan shi.

A hanyan su ta tafiya Shu’aib ya kira sauran ‘yan uwan da iyayen shi ya sanar dasu halin da ake ciki.

Innalillahi wa inna ilahi rajiun Alhaji yake ta maimaitawa yana sharce gumin da suka tsastsafo mishi a goshi.

Hajiya ce ta fito daga kitchen hannunta rik’e da ludayin miya tace…” Alhaji lafiya kuwa,me yake faruwa?”

“Al’ameen ne wai ya yanki jiki ya fad’i a office yanzu haka suna kan hanyan zuwa hospital dashi”.Alhaji yace yana saka hula alamun fita zaiyi.

Nan Hajiya ta bukaci ya jira ta su tafi, bai ki ba ya tsaya jiranta. 

Ita kuma ta kira Altine tace ta karasa mata aiki ta d’auki hijabi tabi bayan mijinta cike da tashin hankali.

Su Shu’aib suna isa hospital suka Tatar da Ya Sa’ad da wasu doctors 3 suna jiran zuwan su.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button