UKUBAR KISHIYATA 1-END

UKUBAR KISHIYATA Page 41 to 50 (The End)

Nan da nan aka d’ora shi a wheel bed suka tura shi emergency.

Basu dad’e da shiga ba iyayen shi suka karaso cikin tashin hankali.

Ganin doctors basu fito ba,ba wanda zai basu gamshashiyat bayani dan haka waje suka samu suka zauna suna jiran fitowarsu.

Sun kai good 1 hr a kanshi amma sun kasa gane me yake faruwa,gashi baya numfashi sai zuciyar shi da take bugawa kad’an-kad’an.

Fitowa sukayi jiki a sanyaye.

Wani doctor da ake kira da Abubakar shi yayi karfin halin yi musu bayanin abinda suka gani dan Ya Sa’ad kuka yake wiwi.

” Alhaji kuyi hak’uri ba abinda Al’ameen yake bukata daga gare Ku kaman addu’a saboda a yanayin binciken da mukayi in numfashin shi bai dai-daita ba cikin 30 mins masu zuwa ba toh gaskiya ba abinda zamu iya yi sai hak’uri”yana fad’an haka shima ya wuce office d’in shi.

Hajiya kuka take kaman ranta ya fita Alhaji yana bata baki duk da shima ta maza yake.

Haka sauran yaransu suma sun taru ana rarrashin Hajiya.

Da’kyar suka samu tayi shiru kowa ya nemi wake ya zauna da add’ua a bakinsu sunayi suna kallon agogo wanda ko wani mint da zai buga da zuciyarsu yake bugawa.

Zaman forty mins sukayi suna add’ua amma shiru ba labari hakan yasa Alhaji yace su tashi su yafi dashi ayi mishi wanka akai shi gidan shi na gaskiya.

Dole kowanne su ya daure zuciya tare da rungumar kaddara suka shiga d’akin da aka k’wantar dashi.

Sun shigo suna kokarin d’aga shi su d’aura kan wheel bed

Kaman daga sama suka ga yayi mik’a tare da salati a bakin shi ya bud’e ido.

Nasan wasu sun kusan samun heart attack saboda sun dauka Al’ameen ya sheka????????????

????????????????????????

*UKUBAR KISHIYATA*

????????????????????????

(Its all about love and betrayal)

Story by *~UMMEE YUSUF~*

  (Maman Yusuf)

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*

*_~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~_*

*part forty six*

Da ido yake bin mutane da suke zagaye dashi suna mishi sannu.

Mik’ewa yayi cikin hanzari ya zauna tare da tambayan meya faru,me suke yi a asibiti?

Amsa mishi suke da bakomai ya k’wantar da hankalin shi,Ya Sa’ad yazo ya k’ara duba shi ya tabbatar musu komai normal yanzu.

Tashi yayi yana cewa shi zai wuce gida dan a lokacin ba abinda yake bukata kaman ya saka Ameera a idon shi.

Alhajin shi yace ba inda zaije sai dai driver ya kaishi.

Dagewa yayi shi zai iya driving da kanshi saboda baya jin komai a jikin shi,nan Alhaji yace toh suje Shu’aib ya ajiye shi a gida dan ba zai yarda yaja mota da kanshi ba.

A mota Al’ameen ya tsare sectaryn shi Shu’aib akan ya fad’a mishi meya faru dashi har aka kawo shi asibiti?

Dolen shi ya bashi labarin abinda ya faru tun daga lokacin da ya yanki jiki ya fad’i har zuwa bayanin da doctors sukayi musu.

Mamaki ya hana shi cewa komai haka Shu’aib ya sauke shi ya wuce office dan kimtsawa saboda a wargaje suka bar komai.

Cike da nishad’i ya nufi cikin gidan yana jin shi kaman wani sabon halitta.

Ameera suna main parlour ita Fateema harda Rabi suna hirar su hankali k’wance ga twins suna zaune a gefe da kayan wasan su .

Rabi tana basu labarin wani yaro mara ji a kauyen su suna k’yalk’yalar dariya Al’ameen yayi sallama ya shigo.

Dukkan su suka amsa mishi amma banda Ameera da ta tsura mishi ido ko kiftawa batayi.

Shima idon ya zuba mata dukkan su ji suke kaman sun d’ebi shekaru basu ga juna ba.

Rabi ta mik’e da sauri tare da kama hannun Fateema sukayi ciki suka basu waje.

Karasowa yayi gabanta ya durkusa ba tare da sun d’auke idon su a cikin na juna ba.

Kamo hannayen ta yayi ya sumbata yace…” Babyna ina kika shiga kika bar zuciyata cikin kuncin rashin ki? Kece farincikin rayuwata I can’t live without u”.

Kasa magana tayi ta sunkuyar da kanta k’asa tana kuka mara sauti.

Hannu yasa ya d’ago da fuskarta suna kallon juna,girgiza mata kai yake alamun baya son kukan da take.yasa hannu yana share mata hawaye.

Fad’awa tayi jikin shi ta k’ank’ame shi tana kuka sosai.

Shafa bayanta yake a hankali yana aikin rarrashi.

Kaman daga sama suka ji muryan Lateefa ta danno wata muguwar ashar.

A razane suka juyo suna kallonta ba tare da sun rabu ba.

“Al’ameen me zan gani haka,kana cikin hankalin ka kuwa?meya had’a ka da wannan k’azamar karuwar da…”

Lafiyayyar mari da taji a kuncinta shiya katse mata bala’in da take.

A rud’e ta juyo tana kallon shi rike da kuncinta tace…” Al’ameen ni ka mara?”

Ido a rine yana huci yace…”u re lucky marin ki kad’ai nayi a yau,but am warning u in kika k’ara attempting k’iran mata ta uwar ‘ya’yana da mugayen suna makamancin wannan wallahi zan baki mamaki shasha kawai”.

Kasa gaskanta abinda yake faruwa tayi ta tsaya tana binsu da ido kaman wata doluwa,sai da ta d’auki some seconds sannan ta dawo hayyacinta.

Hannayenta duka 2 ta d’aura a kai tare da fasa wani ihun da sauran mutanen gidan suka fito.

” na shiga 3 na lalace ni Lateefa”.

Da gudu tayi kan Ameera tana…” Wallahi baki isa ba yau zan nuna miki kinyi kad’an kija dani”.

Ameera tana tsaye tana kallonta ko motsi batayi daga inda take ba har Lateefa ta kusan karasowa gabanta wanda takun da yake tsakanin su baifi 3 ta goce gefe Lateefa kuma ta taho da karfinta hakan yasa ta fad’a kan center table ta fasa goshi.

Ko zugin da goshinta yake bata ji ta mik’e da gudu tayi kan Al’ameen taci k’walar shi tana… “Wallahi baka isa ba duk nafi karfinku wallahi karya ne…”

Ameera ce tazo a zuciye ganin abinda take kuma Al’ameen yayi shiru yana kallonta ba tare da ya d’auki mataki ba.

Finciko Lateefa tayi ta jefata kan kujera tana nuna ta da yatsa tace…”wani irin dabbanci kike mana a cikin gida haka?ki sani komai kika min zan d’auka amma ba zan tab’a zuba miki ido kina abinda kika dama akan mijina ba “.

Mik’ewa tayi bakin nan nata bai mutu ba sai zage-zage da tsine-tsine take ta wuce part d’inta.

Ameera kamo su Fadeel tayi tana rarashi saboda razana da suka yi.

Al’ameen shima yazo joining yana tayata rarrashinsu.

Lateefa tana shiga d’akinta sabon kuka ta saka tana…” Shiken nan asirina ya tonu komai ya lalace min”.

Wayarta ta d’auka ta nemi number Aina’u ,ringin 2 yayi ta d’aga tana…” Sarauniya a gida Al’ameen ya aka yine?”

“Aina’u na shiga 3 duk asirin da mukayi duk sun warware yau ni Al’ameen ya mara a gaban tsinanniyar matarshi” tace cikin tashin hankali da matsacin kuka.

Aina’u cikin tashin hankali tace…” Ya akayi haka ta faru ko dai kinyi kuskure wajan aiwatar da abinda boka ya saka ki?”

“Ba tambayoyi nake nema ba Aina’u mafita nake nema”. Lateefa ta amsa mata tana face hanci.

Nan Aina’u tace mata mafita 1 ce shine su koma wajan boka.

Babu musu Lateefa ta yarda kan gobe da safe zata same ta sai su wuce.

Tana gama waya da Aina’u ta kira number Maman ta taji switch off,ta gwada nasu Fa’iza suma still a kashe.

Haka ta k’wana a cikin part d’inta ita kad’ai dan koda wasa bata yi yunkurin fitowa ba kuma suma ‘yan gidan babu wanda ya lek’a ta.

Da washe gari da sassafe Lateefa ta tashi ta shirya tare da tattara ‘yan kud’ad’e da suka rage mata ta fito dan tafiya wajan boka.

A parlour ta had’u da Ameera tana shirya kan table ta d’ago suka had’a ido,harara ta Watso mata tare da cewa…” Kiyi abinda kike so in just 2 hrs dan kika bar wannan precious time d’in ya wuce it means a lot,dafatan kin gane”tana gama fad’an haka tasa kai ta fice daga gidan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button