UKUBAR KISHIYATA 1-END

UKUBAR KISHIYATA Page 41 to 50 (The End)

Murmushi Ameera tayi tana girgiza kai a zuciyarta tana cewa ba abinda zan gani sai alkhairi saboda da Allah na dogara.

******************

Suna saka kai d’akin boka ya daka musu tsawa tare da dakatar dasu yace….” Ku tsaya daga nan kada Ku kuskura Ku shigo min cikin dan abinda kuka zo dashi ba mai yiwuwa bane saboda mutanen nan yanzu sunfi karfina gashi kinsa tsiburitu da manaru sunyi matukar fushi dani sakamakon k’ona musu ‘yar auta da sukayi.Ku fita nace kamin kusa in huce a kan Ku”.

Lateefa dama tun jiya ranta yake a jagule kuma boka ya k’ara mata da nashi saboda ta gama imanin tana zuwa wajan shi zata samu solution amma ya kore ta,nan da nan taji zuciyarta ya mugun b’aci bata San lokacin da itama ta daka mishi tsawa ba tace…

“Dallah dakata Mallam in ka kasane kawai kace mana ka kasa ba wai ka samu a gaba kana mana ihu kaman wasu ‘ya’yanka ba kuma wallahi…”

Bata samu daman k’arasa maganan ba sakamakon rufe mata baki da Aina’u tayi tana wuri-wuri da ido tace…” Lateefa bakida hankaline kike musu da boka,ko kin manta abinda na gaya mini a baya ne?”

“Ke dallah sake min baki ” tace tana ture hannun Aina’u a kan bakinta ta cigaba da magana…” Anyi mishi musun sai me?yayi duk abinda zaiyi in ya isa”.tace tana huci.

Aina’u zubewa tayi a kasa tana tuba a gaban boka .

Wata mahaukaciyar dariya ya kece dashi yana nuna Aina’u yace…” Ke tashi kiyi tafiyarki,ke kuma kije zaki ga abinda zanyi da wanda ba zanyi ba” ya karasa yana zarowa Lateefa manyan idanun shi kaman na ‘ya’yan boris.

Tsaki Lateefa taja ta fice abinta ko d’ar bata ji a zuciyar ta ba.

Suna shiga mota Aina’u tace…”gaskiya Lateefa kinyi kuskure ko ince kinyi ganganci but dont worry akwai wani shahararren boka da yafi wannan in kina so yanzu zan je wajan shi ya gama mana dasu dan shi ba abinda yake gagaran shi,shiyasa ake mishi lak’abi da boka gagara badau.amma yana da matsala 1 bata karban kudi kad’an kaman wannan bokan sai masu yawa”.

Ba tare da ta kalle ta ba Lateefa tace…” Har nawa yake karb’a?”

“Millions of naira ake bashi” Aina’u ta bata amsa.

Wani mugun kallo Lateefa ta watso mata tare da cewa…”wat millions of naira kika ce?amma daga ke har shi baku da hankali”.

“Da hankali na mana Besty ganin situation da kike ciki shi yasa nace muje wajan shi and am assuring u zai miki aikin da nan da wani lokaci kad’an ba mai yawa ba zaki maida abinda yafi wanda kika kashe,ko ya kika gani?” Aina’u tace haka tana kallon fuskan Lateefa.

Ajiyar zuciya Lateefa tayi tace…” Na yarda dake Ainau,bud’e hand bag na ki d’auko min check book inyi miki singing duka abinda ya bukata just ki cire ki bashi”.

Da haka suka iso inda zata sauke Aina’u ta sauke ta da sharad’in kada ta koma gidan har sai ta k’ira ta sanar da ita aiki yayi k’yau.

Direct hotel da take permanent room ta wuce akan a can zata zauna ta saurari k’iran Aina’u,dan baza ta iya jure ganin Ameera da ‘ya’yanta cikin walwala ba.

Salees ta k’ira a waya kan yazo suyi zaman su tare amma yace mata yana Dubai yaje saro musu kaya sai nan da sati maybe zai shigo.

Haka ta cigaba da zama a hotel ita kad’ai ba abinda take sai shan wine sai bacci.

A ranan da ta cika 3days ne da daddare har ta fara bacci ta fara jin motsi cikin baccin.

A d’an tsorace ta bud’e idonta.

Tsoron ta ne ya k’aru ganin d’akin duhu ya mamaye alhalin bata kashe wutane d’akin ba.

Kamin tayi yunkurin yin wani abu taga haske a tsakiyan d’akin kaman an kunna candle.

Boka ta gani yana mata dariya d’akin yana amsawa,hannayenta tasa ta toshe kunnuwanta da shi sakamakon Dodon kunnen ta da taji suna barazanan fashewa.

Ganin shi tayi akan gadon da take tsirara da wata k’warya a hannun shi ga warin da yake fitowa daga cikin kwarayan shima yana yana barazanan sata amai.

Hannu yasa ya ciro abin ya d’aura mata a kan cikinta tare da karanto wasu kalamai da shi kad’ai ya san ma’anar su.

Tun da Ya fara Lateefa ta kasa motsa koda yatsanta balle tayi yunkurin guduwa.

Saida ya shafe minti 2 yana yi sannan abinda ya d’aura mata a kan cikin ya b’ace bat.

Abin yana b’acewa boka ma ya b’ace kuma wutan d’akin ya dawo, kuma sai a lokacin taji zata iya motsi.

????????????????????????

*UKUBAR KISHIYATA*

????????????????????????

(Its all about love and betrayal)

Story by *~UMMEE YUSUF~*

(Maman Yusuf)

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*

*_~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~_*

*part forty seven*

A razane ta tashi zaune tana dube-dube ko zata ga wani Abu amma bata ga kowa ba.

Barin gadon tayi ta koma kan kujera ta takure cike da matukar tsoro.

Kamin wayewar gari duk kamannin ta sun canza,baya ga haka ga cikinta inda boka ya d’aura mata abu ya zama gyambo yana fitar da wani irin ruwa mai warin gaske da ita kanta tana cutuwa da wsrin balle kuma ta kaiga mutum ya zauna kusa da ita.

Gari yana wayewa ta k’ira Aina’u amma wayarta a kashe.

Wuni tayi tana trying but amsa d’aya take samu shine is switch off.

Ganin yamma ta karato yasa tsoro ya karu a zuciyarta tana ganin in ta sake k’wana a d’akin nan maybe abinda zai same ta sai yafi na jiya worst.

Had’a ‘yan kayanta tayi ta fito da niyan komawa gidanta.

Tana fitowa reception,duk mutanen da suke wajan suka fara toshe hanci suna mata kallon kyama wasu har guduwa suke daga wajan.

Sauri-sauri gudu-ggudu ta fice daga reception d’in ta fad’a motan ta.

Direct gida ta nufa,ta shigo bugum- buzugum kaman wata mahaukaciya.

Ameera ta gani k’wance a kan cinyar Al’ameen ta d’aura Fadeel kan cikinta,Al’ameen yana rik’e da Fadeela yana sai ta sauk’e Fadeel ta d’auki Fadeela da take kuka ita kuma tana bata so.

Tsayawa tayi a bakin k’ofan parlour tana kallon yanda suka kaure da kokuwan wasa suna ta dariya.

Lokaci d’aya suka ji wani irin wari mai kama da mushen jaki ya cika musu parlour.

Lokaci d’aya suka toshe hanci tare da dubu-dube ko zasu ga me yake musu wari haka.

Lateefa suka gani tsaye a bakin k’ofa fuska duk hawaye ga kamannin ta da yanayin ta duk sun canza.

Ganin duk sun zuba mata ido yasa tayi hanyan part d’inta ba tare da tace musu komai ba,suma ba Wanda ya iya ce mata komai illa rakata da ido suka harta shige.

Tafi 5 mins da wucewa sannan suka samu daman sake hancin su.

Ameera turaren wuta ta saka a parlour harda room fresher sannan warin yayi dama-dama.

Tsaki Al’ameen yaja yana cewa …” Gaskiyan Hajiya da tace zata dawo da kanta ni ko shekara zata yi a gidan nasu ba zan tab’a binta ,ji yanda ta dawowa mutane kaman wata mahaukaciy”.saboda Al’ameen duk a tunanun shi yaji tayi dan ya mare ta akan ta zagi Ameera.

Ameera ta rasa bakin magana jin abinda Al’ameen yace,saboda tabbas tasan ba yaji tayi ba bisa la’akari da magananun da ta fad’a mata kafin ta fita.

Allah ya musu tsari daga sharrinta tace a zuciyarta

dan Al’ameen baisan komai game da zaman da suka yi a baya ba.

Lateefa taci kuka a d’aki kaman ranta zai fita ta rasa tudun dafawa ga number Aina’u tayi ta gwadawa harta gaji.

Alert da tagani ya shigo mata waya shiyasa ta tsayar da kukanta ba shiri ganin an k’washe mata kud’in da suke account d’inta dama 12.5 Millon ne a ciki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button