UKUBAR KISHIYATA Page 41 to 50 (The End)

Tunawa tayi da Aina’u da kuma blank check da ta bata.
Sumbatu ta fara tana zagaye d’akin ita kad’ai kamar wata zararriya,ya za’ayi Aina’u ta k’washe mata kud’i tas kuma ta kashe waya me take nufi da hakan?
Kaman wacce ta tuna wani abu a zabure tayi wajan wani drower da take ajiye muhimman abubuwanta ciki harda documents na Al’ameen da ta k’washe a wajanshi.
Tana bud’e drowern shima wayam tagani ba ko d’aya duk ya k’wshe kayan shi sai ‘yan kud’ad’e a cikin.
Ta baya-baya ta fara tafiya tana girgiza kai harta kai jikin bango.
Zaman ‘yan bori tayi a wajan ta rasa wani irin tunani zatayi dan hawayen ma kafewa suka yi.
Lokaci d’aya komai na rayuwa ya tsaya mata Iowa ya juya mata baya ga wannan gyambon k’ara girma yake yana mata ciwon da ba zata ya misalta shi dana ciwon ajali.
Wayarta ta d’auka ta k’ara gwada number Aina’un hoping zai ko shia but still a kashe.
Number su Shamsiyya ta gwada suma a kashe dan haka sai ta k’ira na Mama bugu 2 ta d’auka tana…”Lateefa ‘yar k’walisa “.
Da ba sunan da take jin dad’in shi kaman shi amma yau wani bakin ciki taji ya rufe ta.
Daurewa tayi tace…” Mama su Fa’iza sun zo gida wajanki?”
“Yaushe rabona dasu,sun dad’e basu zo.basa gidan ne?”
“Nima rabo na dasu yafi sati 2 bansan ina suka je ba” Lateefa ta amsa mata.
Mama tace…” Kin san su da zuwa gidan k’awaye kila yanzu suna gidan wata k’awar su”.
Amsawa tayi da haka ne,suka yi sallama suka ajiye waya.
Yini tayi a d’aki ko parlourn ta bata leka ba har zuwa dare.
Karfe goma da rabi na dare tana kwance ta kasa bacci saboda azababben yunwa da yake k’wakularta tun tana daurewa har dauriyan nata ya kare taga ba zata iya jurewa ba.
Cikin tsand’a ta fito dan nemawa cikinta wani abu, Allah ya bata sa’a babu kowa a main parlour bata tsaya b’ata lokaci ba ta fad’a kitchen.
Warmers da akayi dinner dasu ta fara bubbud’ewa ko zata samu amma duk babu komai a ciki.
Wata daban tagani a can kusa da sink tana bud’e shi taga guntun tuwon shinkafa ce da akaci aka rage ga pepper soup na kifi da akaci sauran shima aka zuba akai.
Jiki na rawa ta jawo shi tare da zama dirshan akan tiles ta ciccire k’ayan ciki sannnan ta fara sambad’a loma hannu baka hannu k’warya.
Cikin abinda baifi kiftawar ido ba harta cinye abincin tas .
Bata tashi a wajan ba saida ta sid’e cooler tas kaman an wanke ta sannan ta hakura ta koma d’akinta ta kwanta da niyan gobe da sassafe zata tafi hospital taga doc ko zata samu maganin wannan bala’in da boka ya had’ata da shi.
Da washe gari da sassfe ta saka kai ta fice daga gidan dan zuwa hospital ba tare da kowa ya ganta ba.
Wani private hospital taje cikin sauki ta samu ganin doctor saboda warin jikinta duk inda taje bata hanya ake.
Tana yi mishi bayanin matsalarta amma ji yake kaman ya fita ya bar mata office d’in.
Daurewa yayi ya nuna mata gado da yake cikin office d’in yace ta hau ta k’wanta ya duba ciwon.
Hand gloves ya saka tare da rufe hancin shi da abin rufe hanci sannan yaje kanta ya tsaya a k’yamace ya mata nuni da ta d’aga rigarta ya gani.
Da gudu doctor ya fita a office d’in yana kwara amai kaman ranshi ya fita sakamakon ganin ciwon Lateefa da yayi.
Da ido tabi shi zuciyarta na suya lalle boka ya gama cutarta yasa ta zama dodo a cikin mutane.
A sanyaye ta tashi zaune tana gyara rigarta wasu securities 3 suka shigo suka tasa keyarta gaba har bakin motarta..
Shiga tayi ta tayar da motarta ta fita a asibitin ga hawaye sai tsere suke a idonta.
Tunani take a zuciyarta na ta tafi wani asibitin ne kota ta fita abroad?
Zuciyarta yafi amincewa da ta fita abroad d’in dan haka ta juya kan Motan ta tayi hanyan gida.
Tana tafe tana zancen zuci,tana gwara da tayi dabara ta bawa Salees kud’inta yana juya mata su gashi yanzu sai ta karb’i abinta taje ayi mata maganin fitinan da boka ya had’ata dashi.
Tsaki taja ganin yanda hold up yayi yawa yawanci ‘yan zuwa aiki da makaranta sunfi yawa.
Juyawar da zatayi kaman daga sama taga Aina’u cikin wata luxurious car sabo dal sai sheki take.
Murza idonta tayi Dan tabbatar da gaskiya idonta yake nuna mata ko dai Aina’un da ta sani ne?
Sauke glass na window motarta tayi tana k’wala mata amma bata jiba saboda ita glasses nata a rufe suke.
Har tana shirin bud’e kofar mota ta fita taga taja motarta tayi gaba.
Da sauri ta fad’a nata tabi bayanta.
Tana bin bayanta taga Aina’u ta tsaya a wata lafiyyar gida madaidaici mai d’an karan k’yau.
Tun kamin tayi horn mai gadi ya bud’e mata gate ta shiga ciki.
Tana shiga ya mayar da gate ya rufe.
Da gudu Lateefa ta fito a nata mota ko kashewa bata tsaya yi ba tabi bayan Aina’u ta shiga ta karamin k’ofa tana kwala mata kira.
Juyowa kawai tayi tana kallonta fuska a had’e kaman an aiko mata da sakon mutuwa,ba tare da ta amsa ba har ta karaso kusa da ita tana haki da fara’a akan fuskarta.
Hanci Aina’u ta toshe tana komawa baya tana mata kallon wulakanci da kyama tace…” Lafiya kike kwala min kira haka?”
Hawaye ta fara tana…”Aina’u kin ga abinda boka ya min kin ga yanda ya maida ni na zama abin kyama a cikin mutane kowa ya ganni sai ya toshe hanci,kema kulum ina ta trying number ki bata shiga. Nayi ta jiran kiranki kaman yanda kikayi alkawari shiru sai daima alert d’in kwashe min kud’in account da kikayi gaba d’aya”.
Tunda ta fara magana take binta da kallon wulakanci harta karasa kana tace…” Maganan boka ke kika jawowa kanki dama na gargad’e ki tun farko ba’a mishi musu kikayi harda cacan baki,maganar kud’i kuma nice na kwashe su kuma banje wajan wani boka ba face rabona dana kwada dan bazan tashi a tutar babu ba,saboda haka fita ki bar min gida tun kafin ranking ya b’aci ko insa yanzu ayi min waje dake”.
Da gudu Lateefa tayi kanta tana…” Wallahi baki isa ba ni zaki yiwa haka?na rantse da Allah sai kin fito min da kud’i na”.
Hankad’ata Aina’u tayi sai gata ta zube a kasa kaman kayan wanki.
“Isa isa!!” Aina’u ke kwalawa masu gadinta k’ira tun karfinta.
Da gudu suka zo gabanta suka zube.
Cike da masifa tace…”Ku fitar min da matan nan a gidana kuma wallahi in kuka k’ara barin irin wa’yan nan suna shiga min gida a bakin aikin Ku”tana gama fad’an haka tayi cikin gida abinta.
Ciccib’ar Lateefa da take ta faman zage-zage da tsine-tsine harda fizge-fizge amma hakan baisa sun sarara mata ba saida suka fito da ita da karfin tsiya suka jefar tare da maida gate suka rufe.
Ta dad’e zaune a bakin gate d’in gidan tana cigaba da masifa har tana bubbuga gate ba wanda ya kulata saima jama’a da suka fara taruwa suna mata kallon sabuwar mahaukaciya.
Gajiya tayi da masifar ga zafin rana da ya ishe ta yasa taja tsuman jikinta ta shiga motarta ta bar anguwan.
????????????????????????
*UKUBAR KISHIYATA*
????????????????????????
(Its all about love and betrayal)
Story by *~UMMEE YUSUF~*
(Maman Yusuf)
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*
*_~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~_*
*part forty eight*
Kuka take kaman ranta ya fita wai yau ita Aina’u zata yiwa haka?duk abinda tayi mata a baya bata gani ba?