UNCLE DATTI Page 41 to 50

Washe gari kamar yanda Usman yayi alkawari hakan ta kasance sai da ya biya ta gidan ya duba lafiyar shi kafin nan ya koma Office ya hau duba files d’in da ya tarar nurse ta kawo mishi baya ta aje saman table. Tun yana bud’ewa yana fahimtar me files d’in ke d’auke da shi tunanin maganganun da Fu’ad ya fad’a mishi daren jiya ya hau yawo a kan shi yana birkita mishi tunani………daga k’arshe ma kasa fahimtar komai yayi ba shiri ya rufe gaba d’ayan su ya maida inda ya d’auko su kana ya dunkula hannun shi yana tunani”.
“Gaskiyar Fu’ad ne bai rike abota da hannun biyu ba……..babu abokin da zai yarda ya jefa abokin shi cikin rami maimakon ya samo shi ya fidda shi cikin ramin sai ma ya hau hakar kasa yana watsawa domin ya ciki ramin da yake ciki………,
Duk irin uban sanyin ACn da ke ratsa shi bai hana zufa ya k’aryo mishi ba ya ciro hanky a aljihun wandon shi yana gogewa.
” Datti bai cancanci hakan daga gare shi ba……..bayyanar sirrin shine iya adalcin da zai mishi ko da kuwa baya so , kuma ko da kuwa zai zamo k’arshen abotan su da shi kenan.
Da wannan tunanin ya wuni a Office yana yi.
Haka Datti yaci gaba da zama cikin wannan halin a kullu yaumin baya samun barci fama yake da wannan ciwon sosai……., domin wani sa’in ma duk da irin zafin da gaban shi ke yi mishi sha’awar tana damun shi…….baida option haka zai danne pillow da iya kacin karfin shi yana neman biyan bukata……daga k’arshe ma ya fad’a a sume, baya sanin inda kanshi yaks har sai sanyin hunturu ya busu ya shige shi sosai kafin nan ya farfado ya ga yayi ma kanshi illa har, a hakan ma Allah ya taimake shi yana had’awa da azumi da shi ya sa yake samun saukin feelings ba ko yaushe yake ji ba.
Cikin lokaci ya zafge ya rame yayi baki kamar ba shi ba, Fu’ad hankalin shi ya mugun tashi domin shi kad’ai a gidan ya san irin abunda ke damun d’an uwan shi su Umma duk basu sani ba sai dai sunyi mamaki da suka ji kwana biyu wurin shi shiru, amma sai tunanin su ya basu wata k’ila gajiya yayi yayi zuciya ya koma gidan shi.
Aina ma bata wani damu ba tun da rashin ganin shi da bata yi ba………sai dai acikin kwanakin tana jin fad’uwar gaba mai tsanani…….time to time gaban ta sai ya fad’i.
Wata rana da daddare tana barci tayi wani mugun mafarkin da ya d’aga mata hankali wai Datti na ta amman jini yana nuno mata wata yarinya a can nesa da su bata iya ganin fuskar ta, kokarin rarrafawa yake ya kamo yarinyar a duk sanda ya kusa zuwa dafffff da ita sai ta b’ace, duk sanda ya so ya kamo ta baya iyawa gashi jini ta hanci jini ta baki duk ya b’ata mata jiki da shi………., bakin shi ta lura yana motsi kamar yana so yace mata wani abu………sai ta kai kunnen ta kusa da bakin shi tana kuka………kice rokar mini ita……, Na…….,sai ga gudan jini k’ato ya futo mishi ya fetsar idanuwan shi na rufewa a hankali……..ganin haka ta tashi ta runtuma a gude duk yanda ta so ta d’aga k’afa ta kamo ta amma sai ta k’asa, har ta gaji ta hau nishi da kyar tana d’aga k’afa sai ji tayi an Saki salati ta bayan ta da k’arfiiiiii a take awon muryar ya hau yawo a kwakwalar ta………a take tsoro da firgici suka kamata ta juyo da sauri dan ta gane muryar Datti ne………. firgigittttttttt fa farka a barcin ta hau salati tana dube-dube ita kad’ai…..wannan dare bata kuma komawa barcin ba gani take idan ta koma zata tarar ya mutu.
Washe gari wuni tayi jugumm duk an rasa gane kanta banda sunan Datti babu abunda take fad’a…………., ita gida zata koma ta nemo mijinta tana son shi bata so ya mutu ya barta, shine fa hankalin su duk ya tashi Alhaji da kanshi ya d’au key na mota ya nufi gidan Datti ya tarar k’ofa a garkame mai gadi ya sanar mishi cewa rabon shi da ya ga maigidan da matar gidan har ya manta, ba dan zaman mutunci da suka mishi ba da ya dad’e da barin gidan ya gaji da bauta babu salary.
Da Alhaji ya dawo ya fad’a musu abunda ya faru sai hankalin su ya fi na farko tashi, sunyi sakaci da wauta da har suka yi tunanin yana gida bayan sunfi kowa sannin halin da yake ciki…….kar shima guduwan yayi.
Ummi kam rushewa tayi da kuka dama k’irisss take jira” duk laifin mu ne da muka yi watsi da halin da yaron yake ciki gashi nan shima ya gudu kamar yanda y’ar uwar shi ta gudu”.
Mardiya kam banda kuka babu abunda take yi ita tafi ganin laifin Umman su fiye da na kowa…..tana sane da hurar da Umma ke yi mishi……..gashi nan ta jawo brother d’inta was no where to be found.
Baba Babba cikin dakiyar zuciya yace” ba kuka ya kamata kiyi ba Ummin Nana………, idan da laifin mu a sakacin b’atan shi shima ai da nashi laifin…….., munfi kowa dacewa ya fad’a mana damuwan shi mu da muke a matsayin iyayen shi amma baiyi hakan ba…….me yasa ba za mu fusata ba”.
“Baba karami zaiyi magana Alhaji yayi saurin dakatar dashi” ya isa hakan yanzu mafita muke nema ta yanda zamu b’ollo wa lamarin, yanzu yaya kuke ganin za’a yi?
Gugum suka yi bai tare da samun mafita ba kowa na bin kowa da kallo.
Suna nan carko-carko a parlourn har wajen k’arfe bakwai na dare ko wannen su sai uban zufa yake had’awa, Usman ne ya shigo gidan a dai-dai wannan lokacin yana ganin su ya sha jinin jikin “shi…….bab….a sannun ku”, ya fad’a cikin inda-inda.
Around takwas da rabi sai ga Usman ya shigo gidan dan ya duba shi sai ganin su yayi ko wannen su hankali a tashe, ba shiri ya ja jinin jikin shi cike da fargaba.
Kallon kurilla suka yi mishi suna mamakin zuwan shi a wannan daren ko dai shima ya samu labarin cewa Datti ya gudu ne……..?
Tsohuwa dai k’irjin ta sai bugu yake fattttt fatttt tana so ta tambaye shi amma tsoron ta kar ace shima Usman d’in bai san inda Dattin yake ba.
” Don Allah ya Usman kar kace kaima baka san inda yake ba………., bana son ka furta min cewa d’an uwana ya b’ace ba’a san inda yake ba…….., duk a cikin kuka tayi maganar.
“Shiru yayi kamar yana tunani……, ya so ya b’oye musu amma condition d’in da Datti yake ciki ya sa ba zai iya b’oye musu ba cuz he is in a critical condition, Datti bai gudu ba yana nan cikin gidan nan fama yake da rashin lafiya shi yasa baku ganshi ba, ku biyo ni na inda yake, yana fad’a ya haura saman D’akin Fu’ad da sauri suna bin shi a baya.
A kwance suka tarar da shi a kan bed fuskar shi ya kod’e fatar jikin shi ya koma kamar na mai ciwon Aids, yana had’a ido da su sai ga hawaye babu bakin magana.
Aina ta rushe da gunjin kuka ta rungume shi cikin rashin sa’a garin fad’awa jikin shi ta bata sani ba ace hannun ta ya kai wajen peppered bananar shi ya kwalla k’ara da k’arfi tare da nuno wajen yana yarfe hannu, yaji azaba sosai kamar ranshi zai fita.
Saurin ture ta daga jikin shi Usman yayi……….kunya ce ta sa shi tayi k’asa da kai sai yanzu yaji rashin dacewan abunda yayi………,
Muryar Alhaji yaji yana cewa” me ya same shi a wajen ne yake ihuuuuu haka?
Da murya irin na marar gaskiya yace” Allah baba ku gafarce, na b’oye ban fad’a muku ba cewa Datti na fama da ciwon al’aura kuma ciwon ne ya kwantar da shi ya hana shi fitowa”.