UNCLE DATTI 1-END

UNCLE DATTI Page 41 to 50

          “Whattttt ka san me kake fad’a kuwa? 

       ” Ba tare da ya furta komai ba yayi yunkurin zame bed shit d’in tsohuwa da su Umma suka yi saurin kawar da Ido su baba Karami suna gani sai da suka kad’u, salati suka saki gabaki d’aya dai-dai lokacin Usman ya rufe su Mardiya suka juyo da kan su, sai gani suka yi iyayen maza suna had’a gudu sun rasa ta cewa. 

          Shigowan Fu’ad kenan ya tarar da abunda ke faruwa, da ya d’au ka ba wani abune mai girma ba sai da ya shigo ya gani da idanuwan shi hankin shi sai ya tashi………, sai yayi nadamar kin fad’a ma iyayen su da yayi, ko da yake ba laifin shi bane hasalima bai tab’a gani ba sai yau, da d’inma maganar su yaji shine ya san cewa Datti baida lafiya amma bai san cewa ciwon yayi tsanani har haka ba.

        Fad’a baba Karami yake yi cikin fushi ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ta ciki” yanzu a naku wautan kuna sane da halin da yake ciki shine baku fad’a mana ba? musamman kai Fu’ad ku kwana tare ku tashi tare da mutum yana jin jiki kamar haka baka fad’a a d’auki mataki ba?

         ” Mugun kallo ya watsa ma Usman a ranshi cewa yake zaka yi baya ni ne, a fili kuwa yace” wallahi baba ban san rashin lafiyar nashi ya kai har hakan ba, ga babban maci amana nan da ya b’oye muku, kuma ya san komai yake binnewa, duk suka bi bayan Usman da kallo.

         “Kallon Datti yayi da gefen ido ya ga yana girgiza mishi kai yana ruwan hawaye ma’ana yana warning d’in shi no matter what happen karya sake ya fad’a kawai sai yace” Kaiiiiii  Fu’ad  kaji tsoron Allah me na sani da har zan b’oye musu?

         “Da safen nan ina wajen aiki ya bugo min waya ya sanar dani halin da yake ciki shine nayi mishi treatment lokacin sauri nake yi cuz ina da aiki shi yasa ban fad’a muku ba……., ko shigowa na da niyar fad’a muku nashigo da naji kuna tambayana shine na kawo ku inda yake”. 

         Mamakin irin k’arfin hali na Usman yayi sai ran Fu’ad ya b’aci zuciya ne ya kawo Fu’ad iya wuya yace” Wallahi k’arya kake munafuki, ya san komai boye muku yake son yi!!!!!!!!!!!!

           “Baba sirrine rufaffiya wanda ku baku sani ba……….

         ” Usman Adalcin da zaka yi ma Datti kenan ka fad’a musu………na san shi ya gargad’e ka da hakan shi yasa baka son fad’a……..,idan har Datti ya mutu ka sani kana da laifi mai tsokaa kaima Allah ba zai barka ba………, 

          Sai jikin Usman yayi sanyi sosai ya juyo yana kallon Datti kayi hak’uri abokina dole na fad’a musu su san komai, daga nan ya kwashe komai ya fad’a musu, da irin shawarar da ya ba ma Datti na aikata barnar da yayi duk ya fad’a musu.  

            “Sunyi mamaki sosai har ransu basu gamsu da abunda Usman d’in ya fad’a ba, k’ila sun shirya hakan ne dan wani nufi na su amma bari suji daga bakin Datti.

             ” Datti da gaske ne abunda Usman ya fad’a a kanka?

         ” Hantar cikin shi ya kad’a, Usman baiyi mishi adalci ba da ya fad’a musu…….., amma ko da zai mutu ba zai tab’a amsa laifin da bakin shi ba, tunda basu da wani hujja da zasu bayar wanda zai tabbatar da hakan.

           “Abba ban san komai ba sharri suke min……., 

         To kunji yace bai aikata komai ba kuma muma mun yarda da hakan 

         Shiru Usman yayi dama ya san dole za’a rina ba kowa ne zai yarda da abunda ya fad’a ba haka kuma dole sai ansha daga da Datti wajen fad’ar gaskiya.

         Suna cikin hakan ne wani irin wawan ciwon ciki ya turnik’e Datti…….numfashin shi ya hau d’aukewa sama-sama, sai nishin azaba yake yi………..,suka d’ago shi zasu da niyar su kaishi asubiti yace musu a’a ba zai tafi ba……..su barshi a gida kawai rayuwar shi ne ya zo k’arshe, ciwon ajali baya jin magani.

           Mata suka rushe da kuka wi-wi da hawaye.

          ” Fu’ad dai hawaye kawai yake yi……..ko mutuwa ce zata d’auki d’an uwan shi yafi son ya bayyana musu komai zai fi mishi kwanciyan hankali ko da ya mutu ne……………, sai dai Dattin yana da taurin kai yak’i bada had’in kai, gefe ya matsa shi kad’a yana feeling pains kamar an tsoka mashi a kasan zuciyan shi, dole ne ya tursasa d’an uwan shi ya fad’a laifin da ya aikata,

              Dole ya bi duk hanyar za zai bi ya cimma burin shi na tursasa mishi fad’an gaskiya ba zai barshi ya mutu a matsayin mai laifi ba……..ta wace hanya zai bi yayi hakan……………

           

          B’angaren Nana yau tun safe bata fito ba tana d’aki sai wajen k’arfe tara na dara taji uban yunwa ya kamata ta fito tana neman abinci.

        Har ta d’eba zata koma taji k’afarta ya zungure wani abu………bata sani ba ashe da mutum a parlourn dama yau through babu wuta shi yasa bata gan shi ba.

         Tsoro taji zata koma da baya yayi saurin riko hannun ta tun d’azu ya zo yana jiran zuwan ta, Amintacce ne ya bugo mishi waya yace duk halin yaya ya san yanda zaiyi ya kawo mishi amanar shi, gashi damar da yake da shi kenan idan har ya bari ta tafi ba lallai ne ya samu wannan daman ba.

         Ihuuuu zata kwala yace” shttttttt nine fa, sai tayi shiru cuz ta gane ashe mutumin nan ne dai.

           A masifan ce ta cuno baki kamar yana ganin ta” malam sake ni na koma ko?

          “Naji zan barki amma da kin bani lokaci kad’an……..

         ” Baza ka tab’a samun lokacina ba….har abada ka daina yaudara ta da fake fuskar ka”, ta fizge hannun ta zata shiga.

            “Naji na yarda daga yau amma yau d’aya ki bani lokacin ki idan yaso har abada karki sake bani, rashin bani had’in kai a wannan lokacin zai iya haifar da matsala babba.

           Ganin yanda ya marairaice mata ya sa tace shikenan na yarda.

         ” Alfarma nake nema ki bini mu tafi wani waje ni kuma nayi miki alkawarin a cikin daren nan zan sada ki da mahaifan ki……….., karki yi zargin cutar da ke nake son nayi nayi miki alkawarin cewa babu abunda zai same ki.

       Ba dan ta yarda ba ta bishi sai dai dan yayi mata alkawarin cewa ba zai cutar da ita ba.

          Mota suka shiga ya ja suka bar gidan………, garin babu haske shi yasa bata gane unguwar da suka shiga ba sai ganin ta tayi a wani gida suna isowa yace ta fito.

         Cikin gidan ya nufa da ita…….kasancewar akwai solar a gidan shi ya bata daman ganin ko ina sai take jin kamar ta san gidan amma decorations d’in ya banbanta da wanda take tunanin gidan ne.

        Har matakalan bene suka taka suna isowa dai-dai bakin wani k’ofa yayi dailing number ya saka wayar a kunnen shi” hello mun iso muna bakin k’ofa……….ka fito please.

      Muryar da taji a wayan ne ya tsinkar mata da gaba ta juyo ta aika mishi da kallon shine ko?

         Kai ya gyad’a mata ba alamar eehhh ba tare da yace komai ba.

         K’arar bud’e k’ofa suka ji Nana ta zuba ido ta ga wanda zai fito, she shocked sosai da fuskar da ta gani a gaban ta,………tunanin  fuskar ne ya fad’o mata a rai, sai yanzu take kanin fuskar tayi matching da wanda take gani a gaban ta……………Mene dalilin wani buri ne yake da shi akan ta da rufe ta a guri d’aya?

              Lallai akwai lauje cikin nad’i bata tsammaci ganin wannan fuskar a matsayin ammintacce ba………….

*eedatou*

       

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Leave a Reply

Back to top button