UNCLE DATTI 1-END

UNCLE DATTI Page 41 to 50

          ” Mik’ewa yayi yace” babu komai Aunty insha Allah sai na bi dukkan wata hanyar da zan bi na kwato mata y’ancin ta wannan alkawari ne”.

          “Kana ganin zaka iya?”

      Indai akan Nana ne zan iya yin komai ki kwantar da hankalin ki ba zai ci bulus ba he must pay for it”, yana gama fad’a ya sa kai ya fita”.

          A main parlour suka had’u da Umma Datti ya tusa ta a gaba yana mata sambatu har taji zuciyar ta ya fara cika da tausayin shi shine ta sa kai ta fita ta bar mishi d’akin”.

            “Yauwa Fu’ad dama kai nake nema”, yayi saurin karasowa ya zauna a kan kujera ya sadda kanshi kasa yana wasa da farcen yatsan kafar shi. 

          Zama tayi a gefen shi ta kafe shi da ido cikin tuhuma” maganganun da ka fad’a ranar sun rikita min tunani musamman da naji kana cewa bamu yi dana sani yanzu ba, sai zuwa gaba zamuyi, d’an uwan ka ma yak’i fad’a mana laifin da ya aikata har yayi sanadiyar guduwan Nana ta barmu, don Allah idan akwai wani abu da kuke b’oye mana ku fito fili ku fad’a mana”.

          Idanuwan shi ne suka kad’a zuwa launin ja ya d’ago kai yana kallon mahaifiyar shi da rinannun idanuwan shi wanda babu alaman fari a ciki”. 

               “Ummaaaa”, kiyi hakuri nima ba zan iya fad’a miki komai ba a halin yanzu, a baya babu irin shawarwarin da ban baku ba kuka yi banza dani, idan mai laifi bai amsa laifin da yayi ba ba zaku gamsu da abubuwan da zan fad’a muku ba cuz a baya ma ba d’aukawa kuka yi ba, and kuma banda shaidar da zan tabbatar muku da ita”.

          Dogon numfashi ta ja ta sauk’e a hankali” shikenan tashi ku tafi amma ka sani kai da d’an uwanka kun jefa zukatan mu cikin zullumi”.

         Mik’ewa yayi za shi d’aki dai-dai lokacin Datti ya fito daga d’akin Umma cuz ya gaji da zaman jiran ta hakan yasa ya fito ko zai ganta”.

           Fu’ad ya ga yanda ya zafge ya rame har ya fara kashin wuya idanuwan shi sun fito waje sosai, tsaki mai k’arfi ya ja yayi shigewan shi ko ufan bai ce mishi ba sai ma cewa yayi d’an ba k’ara ba yace abun nashi ba saiti ba ya samu yarinya yana ta danna mata ga irin ta nan, akwai  ranar kin dillacin”.

         Ko ta kanshi Datti bai bi ba domin bai da lokacin da zai tsaya yana kula Fu’ad bayan da nashi matsalar da tafi komai d’aga mishi hankali.

       Zai yi wajen Umma ta d’aga mishi hannu” ka kuskura ka k’araso nan sai ka had’u da fushi na, haka ya mak’ure a guri d’aya hawaye na rolling a saman fuskar shi d’aya bayan d’aya”.

          Da ta gaji da ganin shi a cikin wannan halin ta tashi ta bar shi a wajen,  haka yayi ta tsayuwa da ya gaji ya fita ya bar gidan tunda basa tausayin shi bayan ya fisu jin zafin rashin babyn shi mai d’auke mishi lalurar shi, ta tafi ta bar shi da tsananin kewan ta da na dumin jikin ta sannan kuma ga garuwar da yayi kullum cikin radadin rashin ganin ta. 

        Cikin dare Aina ta fito main parlour she was taste a lokacin and babu ruwan sha a fridge d’in tsohuwa gashi baza ta iya hakuri har zuwa safiya kafin ta sha ba kawai ta fito ta hamma ta nufi fridge d’in, har ta d’auka zata koma taji motsin mutum a bayan ta. Datti ne da tun shigowa ta yake kwance ciwon ciki ya addabe shi ya rik’e ciki yana murd’e murd’e shi kad’ai”.

          Tana had’a ido da shi ta tamke fuska kamar yana ganin ta tayi sauri zata bar wajen dai-dai lokacin cikin shi yayi wani irin murd’awa zufa ya fara sassako mishi cuz of tsabar azabar da cikin ke yi mishi, cikin sarkewar murya yace” help Aina i’m dying “.

            Juyowa tayi da baya zata tafi ta ga ya rarrafo ya rik’e k’asan rigar ta da wani irin dishashshiyar murya nana jan numfashi da kyar yace” please ki taimaka min mutuwa zanyi”, ciki na ciwo wife, karki tafi ki barni cikin wannan halin”.

       Jikin ta ne yayi mugun sanyi a sanyaye ta d’ago ta dube shi sai taji zuciyar ta ta karaya sosai, he really needs her help, and dole ne ta taimaka mishi even though he killed her sister but she can’t afford to loose him”, shima wani b’angare ne na jikin ta”.

        Tsuguna tayi ta d’ago shi da kyar tana fidda numfashi duk ta jigata ta taimaka mishi suka bar parlourn,  D’akin Fu’ad ta shige da shi suka tarar har ya fara barci ta taimaka ma Datti ya kwanta a gefen Fu’ad d’in, kafin nan ta tapping d’in shi da hannu”. Fu’ad!!!!!! Fu’ad!!!!!!, ya bud’e ido a hankali yana kallon ta tare da mik’ewa ya zauna yana mitsik’e ido”.

       Ga mamakin shi sai ganin Aina ya a gaban shi, in a surprised mood yace” lafiya Aunty kika taso ni cikin wannan dare? 

         “Ina fa lafiya Fu’ad, hannun shi ta kama ta manna a saman wuyan Datti yaji zafi rad’a ba shiri yayi saurin janye hannun shi ya koma zai kwanta, bai ma san da Datti a d’akin ba sai yanzu”.

           Muryar Aunty Aina yaji cikin rud’ewa da magiya tace” don Fu’ad mu taimaka mishi kar shima mu rasa shi kamar yanda muka rasa Nana”.

         “Had’e rai yayi sosai ya sha murrr, duk da irin duhun da ke mamaye da d’akin bai hanata gane hakan ba yace” Allah aunty ba zan taimaka ma wannan azzalumin ba, mugu marar imani mai halin akuyan ci”.

         Duk da irin jin jikin da yake yi bai hana shi jin zafin kalaman k’anin nashi ba, rutse ido yayi sai ga hawaye ya biyo baya…… Me yasa Fu’ad yake neman bashi ciwon kai ne bayan ya tabbata da shine da irin kaddarar shi da sai yayi abunda yafi hakan……, amma duk da ya san komai me yasa ba zai d’auki k’addara ba? Me yasa ba zai yarda cewa ba shine ya d’ora ma kanshi son jikin baby ba?

            “Haba wannan wani irin rashin imani ne Fu’ad, dan uwan ka ne fa kake gaya mishi haka? Yau ko makiyin ka ka tarar a cikin wannan halin baza ka fad’a hakan ba, ba’a gaba da ciwo ko ka manta ne?

              Dogon numfashi ya ja ya sauk’e a hankali jikin shi yayi sanyi sosai” shikenan aunty bari na k’ira family doctor ya duba shi, har ya mik’e zai tafi Datti ya rik’o hannun shi da sauri cikin karfin hali ya b’alle bottle na aljihun wannan shi ya fiddo wayan shi ya mik’a mishi, yana cizon lab’a cikin pain yace” Usma…n zaka kira please”, ba tare da musu ba ya hau dailing number d’in shi four times wayar ta yi ringing daga d’aya b’angaren Usman yace” helo friend.

           “Fu’ad ne bro Usman shi yace nayi k’iran ka akwai wata yar matsala ne”.

      “Owk owk gani nan zuwa, ko sallama basu yi da juna ba suka katse k’iran a tare.

         Jim kad’an sai gashi ya iso ya tarar da gidan a rufe ya fiddo waya ya kira mumbar Datti yace ma Fu’ad d’in gashi yan ya iso yana waje ya tarar da gidan a kulle.

          ” Alright gani nan tahowa yana gama fad’a ya bar wajen cikin sauri.

          Har gate ya fita ya ma maigadi magana ya bud’ewa Usman gate ya shigo da motar shi ciki, yana gama parking suka shige d’akin da Dattin yake yana bin Fu’ad a baya. 

          Zama yayi a gefen Datti ya d’an matso gaban shi ya ga sai uban zufa ne ke ta k’aryo mishi kamar wanda yake fama da rad’ad’in dafin maciji.

           Jikin shi ya tab’a yaji kamar garwashin wuta ba shiri ya d’auki kayan aikin shi ya hau mishi gwaje-gwaje, bayan ya gano matsalar ne yace ma su Aina su basu waje zasu gana, Fu’ad da ke latsa wayan shi ya d’ire ta a saman drawar bed d’in a tare suka fita su da Aina barsu su biyun suka koma parlour suka zauna”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Leave a Reply

Back to top button