UNCLE DATTI 1-END

UNCLE DATTI Page 41 to 50

Taji hawaye ya fara sauko mata ya mik’a mata hanky ta goge” kiyi hakuri har zuwa sanda da zan cimma burina, yana gama fad’a ya mik’a mata ledan kayan ya sa kai ya koma mota ya fita da sauri ya bar………tausayi yarinyar ta bashi sosai har sai da yaji zuciyar shi ta karaya ba zai iya jure ganin ta a hakan ba…….., zata iya rusa mishi plan idan yaci gaba da ganin ta a hakan”.

B’angaren Nana kuwa tana nan daskare a wajen da kyar ta iya jan kafa ta shiga cikin gida tana jan kayan da kyar tana nishi”.

Bata tarar da kowa a parlourn ba ta hakan ya sa ta saki ledan kayan a kasa ta haura sama tana kwalla wa Inna k’ira har ta iso d’akin tana cewa” Inna ta!!!! Inna ta!!!!! where are you?, tana isowa ta tarar da tana ninke kaya, Inna na ganin ta tace” har kun dawo diyata?

Kai ta gyad’a a wahalce ta fad’a saman kan gadon tare da sakin yar k’ara washhhhhh, Inna na ga Amintacce yau sai dai har zuwa yanzu zuciya ta bata amminta da shi ba”, nafi zargin cutar da ni yake son yi”.

“Nana kenan da yana da niyar cutar da ke da tun farko yayi, Inna ta fad’a a dai-dai lokacin da ta gama ninkewa ta d’au wani tana yi”.

” Ke dai Inna bakya son laifin mutumin nan”.

“Ba wai haka bane gaskiyar shi ne ta sa hakan, mutum ne shi da ya san k’imar d’an Adam”.

Mik’ewa tayi dan ta gaji da maganganun da Inna take fad’a akan shi” bari naje na duba ko an gama abinci yunwa nake ji”.

“To acici ke dai babu abunda kika iya banda ci……..

Fita tayi tana dariya Inna ta girgiza kai tana jin dad’in zama da ita sosai tana d’ebe mata kewan rashin d’a da bata da shi sometimes har fargaban rabuwa da ita take yi even though komai daren dad’ewa dole ne su rabu”. 

Da daddare Amintacce ya zo duk suna d’akin Inna suna hira a lokacin wutan layin su ya samu matsala babu haske a d’akin.

Sallama yayi musu da daddad’an muryar shi suka amsa su duka…….. Zama yayi a k’asa ya tankwashe k’afa yana suka hau hira da Inna, Nana kam gaban ta sai luguden bugu yake yi, lamarin mutumin nan na d’aure mata kai mai yasa tafi jin muryar shi tafi dad’i da fitowa yanzu compare to d’azu………, haka dai take ta tunamin nan har suka gama hira da Inna yayi mata sallama yace ma Nana ta fito ta same shi a waje karta b’ata mishi lokacin sauri yake yi, sai kuma ya mik’e ya fita.

Bayan fitan shi Nana ta gyara kwanciyar ta akan bed d’in Inna ta batsar da shi…….da Innar ta ga bata da niyar tashi ta daka mata bugu a gadon baya ta ce kinci gidan ku ba da ke yake magana ba?

“Cuno baki tayi ta mik’e tana kunkuni ciki-ciki”, Allah Inna na tsane wannan mutumin bana k’aunar ganin shi”.

” Munafurcin banza ina ce d’azu tsabar kin k’osa da son ganin shi kika saka ni a gaba kina tambayar yaushe zai zo?

Fitowan ta kenan daga d’akin taga NEPA sun kawo wuta, tana fitowa kofar gidan ta hange motar shi daga nesa kad’an ta tako a hankali tana tafiyar hawainiya ta zo ta bud’e motar ta shiga.

” Difffffff numfashin shi ya d’auke, cikin motar babu haske ya kai hannu ya lalumi nata ya had’a cikin nashi yana wasa da su………, tayi saurin janye hannun ta cikin matuk’ar fad’uwar gaba da ya zamar mata kamar al’ada a duk sanda ta ganshi ko taji muryar shi”.

Sautin murmushin shi taji ya doki dodon kunnenta yana cewa” wannan bugun zuciyar na menene amanata?

Sai taji kunya ya rufe ta ashe shima yana jin heart beat d’inta.

Ba tare da ta amsa mishi ba tayi shiru tana murza hannun ta”.

Shiru shima yayi yana mai jin wani abu a ranshi” ba dan burin da yake da shi a kanta ba da he will let her go”.

“Haushi na kike ji ko Nana kina ganin kamar banyi miki adalci bane da na tsare ki a nan ko?

” Har yanzu bata tana mishi ba ji tayi ta cika da tsananin jin haushin shi, ai tambayar rainin wayo yake yi mata”.

Doguwar ajiyan zuciya ya sauk’e ya fiddo da takarda guda d’aya mai d’auke da rubu a ninke ya rik’o hannun ta yana murzawa a hankali…… wani irin force of attraction ya kama su lokaci guda, a tare suka lumshe ido” uhmmmmm”, suka fad’a.

Amintacce kuwa was carried out by tattausan fatar jikin Nana, yarinyar she gather soft skin d’in da ko gani kayi mata zata d’auke maka hankali balle ace had’uwar fata da fatar da zaka yi da ita”.

Kan kace me idanuwan shi suka kankance, shi mai sha’awar mace ne hakan yasa ya d’an ji marar shi ta murd’a yayi saurin sakin ta yana maida numfashi………., ganin idan suka ci gaba da ita a hakan zai jawo ma kanshi matsala yayi saurin sallamar ta ta koma gida.

D’akin ta ta nufa direct ta fad’a saman gado jikin ta duk a mace yake……taji wani irin shauk’i ya kama ta……… takardar da ya bata bata bud’e ba ta had’a da wanda ya bata a baya ta maida ta ajiye……..daren daren ranar duk runtsawar da zata yi zuciyar ta na karanto mata fuskar Amintacce, kunnuwan ta kuma ya karade mata da amon muryar shi. 

B’angen Fu’ad da Datti kuwa zasu kwana da Datti a guri d’aya su tashi tare babu mai ce ma wani ci kanka……….shi dai Datti yana so sun sulhunta amma ba fuska.

Zaune yake a parlourn da ke d’akin su idanuwan shi na kan TV yana sauraran news ko zai ji wani labari game da b’atan baby d’in shi. Fu’ad ne ya shigo ta kofin a hannun shi wanda ban san ko me nene a ciki ba yana sipping………,, 

Wuce Datti yayi ya koma inna room ya zauna abunshi tare da d’auko eye piece ya connecting da waya ya manna a kunnen shi, yana kurbe abun cikin kofin yana lumshe ido”.

Daga parlour Datti ya kashe TV d’in ya nufi inda Fu’ad yake ya zauna a gefen shi yana magana amma ko kula shi baiyi ba”.

Da ya gaji ya fizge wayan a hannnun shi ranshi a b’ace yace” ba da kai nake magana ba kayi banza dani”.

Sai a sannan ne ya d’ago ya jefa mishi mugun kallo”.

“Duk da ranshi ya b’aci da irin rainin wayon da yake yi mishi sai ya dake ya sassauta murya.”

“Please Fu’ad mu ajiye gaba a gefe duk abunda ya faru kuskure ne ba yin kaina bane, idan kana min haka Umma da baba babba na min haka ina kuke son na sa kaina?

“Jini na ne kai idan wani ya juya min baya bai kamata kai ma ka juya min ba”

“Kallon shekeke Fu’ad ya watsa mishi, lallai Datti baida kunya da har zai iya tunkarar shi yace zaiyi sulhu da shi bayan irin abunda yayi ma masoyiyar shi, yet baya so ya amsa laifin shi a gaban parents d’in su”.

” Murmushin yake wanda yafi kuka ciwo yayi” bana yin sulhu da kai har sai zuwa ranar da zaka amsa laifin ka ya mik’e zai fita har ya kai bakin k’ofa ya juyo yana kallon Datti” idan kuma baka amsa laifin ka ba i assured you sai na tilasta maka ka amsa da bakin ka”.

“Hmmmm ina jiye maka wannan ranar da haske zai mamaye du, gaskiya ya ringaje k’arya, ranar da zaka cika da tarin kunyar abunda ka aikata………, yayi saurin barin d’akin ya nufi d’akin Alhaji.

Yana kwance akan carpet ya d’ora kanshi a saman pillow yans reading news paper, tsohuwa na gefen shi itama a k’asa ta zauna, gefen ta kuwa yankakkiyar fruits ne tana yi ma mijin nata hira tana d’auka tana taunawa a hankali, sallamar shi ne ya saka su d’agowa da sauri suka dube tare da amsa mishi”.

Samo wuri yayi ya zauna ya had’a kai da gwiwa yana rusar kuka.

Hankalin su ya gashi sosai suka hau tambayar shi cikin had’in baki.

“Ya Sallam, Fu’ad me ya faru kake kuka?

“Alhaji an salwantar min da rayuwar Nana ta gashi ta gudu an gaza samun ta, wayyo kun raba ni da farin cikin na har abada zuciya ta zata dawwama cikin kunci………Inna ma da a sanda take fad’a muku cewa” *JIKIN TA YAKE SO!* kun saurare shi……., ina ma da tun farko baku yarda da yaudarar da yake muku ba……….ina ma da baku bada amanar ta a hannun shi ba……….. kasa cigaba da maganar yayi a sakamakon wani irin kukan da ya kwato mishi………Tsohuwa ma ta hau kuka cikin tsananin tausayin shi da kuma jikar ta da ta bata aka yi cigiyar ta aka rasa”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Leave a Reply

Back to top button