UNCLE DATTI 1-END

UNCLE DATTI Page 41 to 50

Kaiiii jama’a naji dadin comments d’inku lallai Ammintacce ya farin jini lokaci guda ya zama celebrity kowa so yake ya san ko shi wanene ciki har dani…….. wasu suce Usman ne, Fu’ad ne, Datti ne duk dai haka ake ta fad’a amma ni dai nace……..uhmmm uuhmm da dai naso na bari sai kun karanta da kanku amma yanzu tunda naga abun ya zama na cece kuce ne nari da na fad’a muku, yauwa matso da kunnen ku kutsa kuji………..eehhhhmm tsowace ce ammintacceee……..lol.

*”eedatou”*

        

*????SHINNING STARS WRITERS ASSOCIATION* 

”’The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers.”’ 

https://m.facebook.com/110896360504039/photos/a.110896457170696/110898470503828/?type=3&source=45

???????????? *UNCLE DATTI*????????????. 

                 ”’JIKINA YAKE SO!”’

          

               *WRITER OF*

*1.MAGANIN MATA(DAMUWA)*

*2.WAYE MACUCI?*

*3.RAYUWAR SUMAYYA*

*4.UNCLE DATTI(JIKINA YAKE SO)!*

              

                            © 

                      *eedatou✍????*

”’Follow and ✅ote me on Wattpad”’: *eedatou*    

                     3️⃣7️⃣—3️⃣8️⃣

Juyowan da zaiyi tayi ido hud’u da shi…….ido waje ta zaro dan ganin wannan mutumin ne amma samm zuciyar ta ta kasa yarda da shi…………., sai ido take bin shi da shi ba tare da tace komai ba, kamar kullum murmushi ya sakar mata tare da k’awar da kanshi suka ci gaba da hira da Inna. 

         “Hawaye ne ya cicciko mata a idanuwan ta………menene kuddurin da yake da shi akan ta da zai tsare ta na, juyowa tayi da sauri zata bar wajen Inna tace” ina kuma zaki y’ata koma ki zauna “.

         Bata son da da ita ba shiri ta samo guri ta zauna ta k’asan ido take fuskar shi, tana so ta gano wani abu game da shi.

           Sai take ganin kamar da ban-banci tsakanin fuskar da take gani a duhu……….lallai Amintacce yana wahalar da zuciyan ta wajen gano ko shi d’in wanene and she can’t tress him. 

          Da wanan tunan har ya bar gidan ba tare da ta sani ba.

          Inna na zaune taji barci ya fara d’aukan ta tace wa Nana ta taso suje su kwanta, sai a sannan ne ta dawo daga rakiyar tunanin da take, jiki a sanyaye ta shige d’aki ta kwanta itama Inna tayi nata d’akin.

           B’angaren Inna tana shigowa d’akin taji wayan ta na ringing a samar drawer tayi sauri ta picking ta manna wayar a kunnen ta, suka gaisa da juna”.

         ” Yaya amanata Inna da fatan kina kular min da ita?  

       “Ehhhh gwargwadon iyawata ina yi sai dai fa yarinyar har yanzu bata hak’ura da batunta na komawa gida ba, baka ganin ya dace ace ta koma gida?

            ” Uhmmmmmm ya fad’a cikin muryar shi mai dad’in sauraro, har yanzu ba’a kai matakin da zata koma ba……..burin nawa bai gama cika ba amma saura k’iris”.

        D’oguwar ajiyar zuciya taja ta sauk’e a hankali…………to amma ya kamata ace ka bayyana mata kanka……ina tunanin ta fara zargin wani abu………..,ka san bana ta tashi hankalin ta saboda kar abun ya shafi juna biyun ta………..

            “Wani irin abu yaji ya daki zuciyan shi mai kama da mashi dan jin ta ambaci sunan ciki……….shikenan Inna zan duba na gani ki d’an bani lokaci kad’an kafin nan na gama cimma burina”.

         ” Uhmmm, shikenan tunda kace haka……Allah ya taimaka ya bada sa’a ina yi maka addu’ar cimma burin ka”.

         “Ameen, Ameen inna na gode, daga nan suka yi sallama ya kashe wayan.

         

            Tunani ya dumiya a ciki she ma kanshi bashi da piece of mind akan killace ta da yayi but bai da option than yayi hakan……….., waya ya d’auka ya dailing wata number ya manna a kunnen shi daga d’ayan b’angaren aka d’aga.”

         “Har yanzu baka kai gida bane naji kamar kana tuk’i ne?

       ” Yeah of course amma saura kirissss.

      “Owk….. Owk…..to yaya mission d’in?

        “Dariya yayi a dai-dai lokacin da ya k’arya steering motar ya shawo kwana,” gaskiya mutumina kwakwalwar ka na jaaaaa ban yi zaton yarinyar nan zata yi saurin gano wani abu ba sai yanzu………., ya bashi labarin yanda ta tarar da shi a parlour “.

           ” Ajiyar zuciya mai nauyi ya sauk’e tare da gyara kwanciyar shi a kujerar da ke babban parlourn gidan su yace” dama na san dole za’a rina shi yasa tun farko na shirya hakan”.

           Basu wani dad’e da wayan ba suka yi sallama da juna………, daren ranar da tunanin yarinyar ya kwana ga uban zafi da ranshi ke yi mishi…….., abubuwa da yawa sun saka shi a gaba sun hana zuciyan shi sakat.

          B’angaren Inna kuwa bayan ta gama waya da mutumin taji an bud’e k’ofa an shigo…….., Nana ce ta tsaya daga bakin k’ofa ta jingina bayan ta da jikin k’ofan hawaye na bin bayan fuskar ta d’aya bayan d’aya, da alama taji duk abunda suke fad’a cuz a hansfree wayar take. 

       Jikin ta ne yayi mugun sanyi ta taso da sauri tayi wurin ta zata lallashe ta Nana ta ja jikin ta da sauri cikin kuka tace” Irin zamar da zamuyi da ke kenan? Ashe dama kina sane da komai kike b’oye min………da na d’auka ke mai tausayina ne amma yanzu na gano cewa da had’in bakin ki ake so a cimma buri a kaina……..kuka ne ya ci k’arfin ta tayi shiru tana sheshshekar kuka…….laifin ta ne da ta yarda da da ita tun farkon zuwan ta gidan har take bata girma ta d’auke ta a matsayin dangin ta duk da dai ta san cewa bata tab’a ganin ta ba sai a gidan amma haka ta ammince da ita.

         Zuciyar Inna ya karaya sosai da jin kalaman yarinyar” Ba cutar da ke zamu yi ba ki yarda da dukkanin abubuwan da nake fad’a miki……….,

            Cike da takaicin maganar Nana ta juyo ta dube ta” ta yaya zan k’ara yarda da ke bayan da had’in bakin ki aka b’oye min ainihin fuskar Ammintacce da kuma hujjar zamana a gidan nan tare da ku?

          “Na sani ni mai laifi ne a gare ki amma ki daura ki dubi magana ta da fuskar fahimta………

       Ba zan tab’a fahimtar ku ba har a bada………, barin d’akin tayi ta koma nata da sauri ta fad’a saman bed ta shiga rusar kuka kamar ranta zai fita…………, abu ta tuno da sauri ta mik’e da sauri ta d’ago rigar ta tana shafa cikin ta………..da gaske ne baby ne a ciki d’ina?

        Is it true that baby d’in nan na Uncle d’ina bai zube be? 

        ” me yasa Inna bata fad’a mata cewa cikin ta bai zube ba bayan ta sani………….

           Kuka ne mai tsananin k’arfin gaske ya kwace mata na tunawa da rayuwar da suka yi da Datti” ya treating d’inta kamar k’are, ya maida ta kamar jujin shi, ya maida ta tamk’ar rigiya a duk sanda yake bukatar ruwa ya zira gugan shi ciki ya d’iba…………, at the end da ya d’irka mata ciki sai ya manta da irin rayuwar da suka yi a baya, at yayi yunkurin zubar mata da cikin…………, hawaye mai uban d’umi ta ya sake bin kyakkyawar fuskar ta tana shafa cikin tace” baby d’ina dady d’inka baya son mu? Ya maida mu useless, he tried to murder us.

          Idan na haifo ka ka fito duniya kar ka d’auki irin halin mahaifin ka………,kar ka kasance cikin jintsin maza marasa sha’awan mata like daddy d’inka………..bana son halin mahaifin ka ya shafe ka…………..bana so ka taso da halin akuyanci irin na mahaifin ka…………cuz idan ka taso da hakan zaka zamo mutum mugu mai son kanshi……….zaka yi cuta irin na mahaifin ka……….., promise me cewa idan ka fito duniya ka zamo mutum kamar kowa baza ka aikata abunda mahaifin ka ya aikata ba………….,abun da ke cikin ne ya fara motsawa kamar yana jin ta………murmushin mai d’auke da hawaye ya subuce mata ta ta sauk’e rigar ta koma ta kwanta……….tana mai ci gaba da kukan ta…….ta ko ina bata da sauki ga matsalar da Datti ya jefa ta a ciki ga kuma Ammintacce da saboda bakar kudurin shi ya ki barin ta ta tafi gida. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Leave a Reply

Back to top button