UNCLE DATTI 1-END

UNCLE DATTI Page 41 to 50

         Cikin kwanakin ta d’aga hankalin ta sosai kullum cikin d’aki take bata saukowa sai idan yunwa ya addabe ta kafin nan ta nemo abinci taci ta koma. Inna ta damu sosai da wannan sauyi na ta sammm bata jin dad’in hakan domin Nanar bata tab’a bari su had’u ko da kuwa sun had’u bata bata mata maganar har ta gama abunda ya kawo ta ta koma d’aki.

            A lokacin tsananin kewan gida na kama ta idan ta tuna sai tayi ta shafar cikin ta tana kuka shine kad’ai abunda yake saka ta jin sauki a halin yanzu.

          Shima kanshi Amintacce bai ji dad’in hukumcin da Nana ta d’auka ba………,hakan ya sa ya gane cewa duk rubutun da yake bata bata karantawa………, da ace tana karantawa da ba zata d’aga hankalin ta ba……..da zata fahimci asalin kuddurin shi na yi hakan……cuz yayi rubutun ne ta yanda zata gane ko waye shi da kuma kuddurin da da dalilin kin bayyana mata fuskar shi da yayi……..

          Wata rana da ya shigo gidan da rana ya haye sama daga bakin k’ofa ya tsaya yana mata magana da tattausar muryar shi wanda kusan kullum kamar ana k’ara mishi zaki yace” ko da sau d’aya kin yi tunanin bud’e takardun nan da na baki kin karanta? 

         “Ko wace takarda da dalilin rubuto ta me yasa baki bud’e kin ji hojjojin da na rubuto ciki ba…….,

         ” Sheshekar kukan ta ya jiyo ba shiri ya runtse ido, da ta san me yake ji a ranshi da ta hak’ura da kukan nata”.

       Mik’ewa tayi daga kwancen da take ta tako har bakin k’ofa ta tsaya……..baka da wani hujjar da zaka ajiye ni a nan, idan har zaka iya rubuto min takarda kamar yanda ka fad’a na tabbata babu abunda zai hana ka bayyana min kanka”.

         Bana bukatar karanta komai ka rik’e hujjarka kuma ka ci gaba da b’oye kanka, sai ta durgusa a k’asa tare da jingina bayan ta a jikin murfin k’ofa ta saki wani irin malalacin kuka mai tsuma rai.

        Wani irin kuka yaji ya kwato mishi ya hau rerawa ya hau bugun k’ofan, muryar shi na breaking yace” kar kiyi saurin yanke hukunci akan akan abunda baki sani ba……….takardar nan shine sirrin duk wani abunda kike so ki sani game da ni………..

             “Dakata malam ba zan bud’e ba nace…..ka barni na tafi gida na gaji da wahalar da ni da kake yi. Suna cikin hakan ne yaji an dago shi ta baya……….Inna ce ta fito daga d’aki zata lek’a ko Nana ta fito parlour sai taji muryar Amintacce na kuka………, shine ta hauro taji menene ya faru………

          Jikin ta ya mutu sosai da ta ga shi a hakan abune mai matukar wahala ka ga namiji yana kuka wi-wi da hawayen shi sai gaji Amintacce yana yi.

          “Muryar shi taji tana cewa” Inna kin gani kuka take yi kice mata ta daina bana so? 

           Takardar da na rubuto mata ma tace baza ta karanta ba yaya tace so na saka raina?

         “Ni na fita jin zafin killace ta dani amma dole ce ta sa babu yanda na iya…………

             ” Shiru Inna tayi sunyi matuk’ar bata tausayi sosai daga shi har ita Nanar……….

         “Ban ga laifin ta ba dan tak’i bud’ewa kamata ka janye maganar burin da kake son cikawa ka fito mata ido da ido ta san komai game da kaiiiii.

           “Hawaye mai uban d’umi ya matsa” Shikenan  Inna yanzun nan zata san ko ni waye kuma a yau d’in nan zan zata koma ga iyayen ta ko da kuwa burina bai gama cika ba amma Alhamdulillah ko a haka ma ya wadatar……….bud’e ki ganni a yau zan bayyana miki kaina.

         Tana jin su kuka yaci k’arfin ta she cried bitterly, da dishashshiyar muryar ta tace” bana son ganin fake fuskar ka da a kullum kake yaudara na dashi cewa fuskar Amintacce ne bayan ba hakan bane…………,

          “I hate to see your face……..na gaji da yaudara da zulumin da kake barina da shi a duk lokacin da nayi arba da fuskar ka…………., kuka ta kuma sakewa har tana shid’ewa.

          “Billahil Azeen nine Amintacce ba da fuskar da kika saba ganina zaki ganni ba……..i bet you yau na shirya bayyana miki furkar da ya dad’e yana b’oye miki…….bud’e ki gani nana nine………..,

         “Enough please!!! tayi sarin katse shi cikin kuka,  na gaji da jin yaudarar ka please let me be………duk ka bi ka hana zuciya ta sakattttt ko da yaushe cikin fargaba take, i don’t want to see you…….i hate you most.

          Maganar ta ta k’arshe yayi mishi zafi da yawa……..ba tare da ya furta komai ba ya sa kai ya fita daga gidan Inna har waje ta bishi tana kwala mishi k’ira amma ko tsayawa bai yi ba. 

         Mota ya shiga da uban gudu ya ke jan ta kamar zai tashi sama sai da yayi tafiya mai nisa kafin ya parking ba tare da ya fito ba ya fiddo dawa ya dailing wani number………daga d’aya b’angaren aka d’aga tare da sallama”, maimakon yaji an amsa mishi sai ma jin sautin sheshshek’ar kukan shi, da mugun mamaki yace” Subahanalillah! Me ya same ka kake kuka? Waittttt tell me please, duk a rikice yake maganar”.

         “Ina son mission d’in nan ya k’are daga yau…….daga yau, yarinyar tana bani matsala sosai ban jin zamu d’ore a hakan”. 

       Doguwar ajiyar zuciya ya saki yana sauraran shi har sai da ya gama kafin nan yace” tun farko sai da na warning d’inka akan wannan plan d’in, ni ban ga dalilin da yasa baka so ka yi ido hud’u da ita ba………..yanzu yaya kake ganin za’a ending mission d’in?

          “I really don’t know, har yanzu burina bai gama cika ba…….., ka san for how long na d’auka nake neman hanyar da zan cika burina?

      Ya gyad’a kai kamar dama yana ganin shi.

       ” You won’t know ni kad’ai na san irin adadin lokacin da na d’auna ana zaman jira. 

          “Ka ending wannan plan d’inka please ni kaina wallahi k’arfin hali kawai nake yi a duk sanda na je mata a matsayin kaine, sometimes tausayin ta har kusan saka ni kuka yake yi, tana narkar min da zuciya musamman da cikin ta ya fara tsufa d’in nan”.

          Da haka suka yi sallama ya koma gida ya kwanta da tunanin kala-kala a ranshi….that night he cried bitterly har sai da hawaye suka k’afe mishi a ido”. 

         Bayan kwana biyu abubuwa sun dad’e cunkushewa wa Amintacce duk sanda ya so ya so ya shawo kan matsalar abu ya ci tura, a duk sanda ya shigo digan sai ya haura d’akin Nana ta bud’e amma ta k’i bud’ewa hakan zai koma cikin k’unan rai. Inna ma tayi nata iyakan k’ok’arin amma duk da haka still Nana tana nan akan bakan ta…….., yanzu kam ma idan zata sauk’o sai ta tabbatar babu kowa a parlourn kafin ta fito tana gama abunda zata yi ta koma ciki………, haka zata zauna ta saka cikin a gaba tana kuka she knows that babu k’ofan guduwa daga gidan cuz akwai tsaro na musamman da aka yi ma duka k’ofofin gidan.

        Yau ma kamar kullum tana d’aki tana kwance taji haka kawai tana so ta watsa ruwa rabuwan ta da wanka har ta manta, mik’ewa tayi ta sauko ta nufi ban d’aki ta had’a ruwan wanka ta tayi tana gamawa ta fito ta d’au rigar ta zata saka taji yak’i shiga……..kusan kala goma ta duba duk sun ki shigan ta kawai sai ta sa kuka……….ta hau dube-dube ko zata yi sa’a ta samo wanda zai yi mata dai-dai bata samu ba haka ta hak’ura ta maida wanda ta cire sai hawaye take yi cuz kayan sosai yake tashi da tsami.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Leave a Reply

Back to top button