UNCLE DATTI 1-END

UNCLE DATTI Page 51 to 60 (The End)

      Wannan k’almar da Fu’ad ya fad’a sai ya zamanto weak point na Datti, ma’ana ya ajiye shege kenan shima ya rama maganar da ya cab’a mishi………., fuuuuu ya tashi kamar zai dake shi Fu’ad ya jacking d’in shi dukan su suna huci kamar zasu had’iye juna d’anye, Sadeeq kam har ya tsorata ya fara kuka ganin haka Nana ta shigo tsakanin su da gudu ta tsaya” ku kashe ni kawai ku huta nima na huta da rikicin duniyar da nake fuskan ta.

        “Me yasa a kullum nice tsilar zama matsala a tsakanin ku………to she bakin ta tayi a sakamakon gunjin kukan da taji ya zo bata, sai duk jikin su yayi sanyi suka saki juna suna kallon ta cikin wani irin yanayi.

        “Magana Fu’ad yayi cikin wata dishashshiyar murya” Nana tsananin kishin ki da nake yi shi ya sanya bana son wani namiji ya rab’e ki hatta d’an uwana……ban tab’a tsammanin a lokacin ina tsananin k’aunar ki ba sai daga baya naji zuciyana na bijiro min da son ki kamar zai fasa k’irjina……., idan zaki lura a da ina nuna miki tsana sosai wallahi tsabar son ki ne yake d’awainiya da ni kuma na fahimci cewa Datti ma na son ki, sai dai na kasa fassara ko wani irin so yake miki kasancewar Aunty Aina a matsayin matar shi……

        “Karya yake wallahi ni ke son ki da gaskiya tun kina tsumma har kika girma na raine ki da soyayya na a zuciyar ki…….bak’ar k’addara ne ya sa na cutar da ke cuz duk da cewar na san ke ce kad’ai maganina amma babu yanda banyi ba na cire sha’awar ki a raina amma na kasa.

       ” Na tabbata duk namijin da ya tsinci kan shi a halin da nake ciki sai ya aikata fiye da abunda na aikata…….

       Shiru suka yi suna kallon ta ko wannen su na hawaye……….., Mardiya ce tayi k’arfin halin janta suka shige d’aki tana jin kukan Sadeeq amma ta kasa kwacewa daga rikon da tayi mata balle ta kawo mishi d’auki…….., suna isowa Mardiya ta datsa ma kofar key ta dukusa da gwiwan ta ta rushe da kuka” kiyi ma Allah ko yi ma Annabi ki zaba wanda kike karki so a tsakanin su, kar ki bari gabar su na baya ya dawo sabuwa……kar kiyi sanadiyan dasa gaba mai tsanani a zuciyoyin su”.

        “Itama Nana kukan take sosai kamar ranta zai fita” wayyo Allah Mardiya ina zan jefa kaina na samu Sa’eedan radad’in da nake ji…….ban san wanda zan zab’a ba……..ban san wanda zan d’,auka na bar wani ba……..

        Ita kuka Muardiya kuka aka rasa mai lallashin d’an uwan shi, da kyat suka tsagaita kukan daga nan Mardiya tayi mata sallama ta koma b’angaren Umman ta. 

        Bayan fitan ta ne Fu’ad ya ritsa Nana a gaba yana cewa” me yasa bats fad’a ma su alhaji cewa shi take so shine zab’in ta? Anya kuwa ta na son shi? Ta mishi adalci da zata k’i bayyana ma mutane cewa shine zab’in ta? Shi hawayen ita hawayen har ya kare surutan shi ya fita ya koma d’aki yana jin pains a k’ahon zuciyan shi.

       Da daddare kusan kwana zaune mutanen gidan suka yi musamman mutane ukun nan.

        Washe gari kuwa iyayen nasu suka sake k’iran meeting bayan an gama hallara baba babba yace ya maganar su ta jiya ta kwana? Shin an samu wanda zai yi sacrifice ya janye ma d’an uwan shi?

        Duka su biyun suka yi shiru ganin haka sai iyayen nasu suka fahimci dai cewa kowa na kan bakan shi na auren ta.

        Kan kace me sai gasu sun had’a zufa tafffff hatta tsohuwa ma bini-bini take sharar hawaye tace” ja’irai kawai kun jefa mu cikin damuwa wallahi ko barci bama iyawa……..da ku mayuwa kuna kama mutum tuni zaku cinye shi., tana yi tana sharar kwalla.

      Alhaji ne yayi gyaran murya sai da ya natsa kafin nan ya dubi Nana da ta sadda kanta ta kasa d’agawa tana wasa da yatsun hannun ta, da zaka binciki kasan zuciyar ta damuwa ne yayi mata yawa shi ya sa ta yin hakan.

         B’angaren ki fa akwai wa da kika zab’a ko kuma har yanzu babu mafita?

       Sai ta girgiza mishi kai alamar a’a babu”.

        Numfashi ya ja mai nauyin gaske ya sauk’e a hankali sai yayi jimmm kad’an yana nazari can kuma yace” Tunda dukan an rasa wanda zai sadaukar ma d’an uwan shi, kema Nana kin ki zab’ar wanda kike so ina so ki bani zab’i kuma ina fata duk wanda na zabar miki zaki aminta da shi.

          Mugun bugu zuciyoyin su su ukun suka yi a tare ko wanne na tsoron kar d’an uwan shi za’a bawa a hana shi.

     Kai ta gyad’a mishi tare da sharo hawayen alamar ta amince.

       “Shikenan ku tashi ku tafi, Datti da Fu’ad ina so duk wanda ya rasa ya d’auki komai a matsayin k’addara Allah zai yi mishi zab’i da mafi alkhairi……., ba wai dan mun fi son wanda muka zabar mata bane ya sa muka yi hakan dukan ku matsayin ku guda ne baza mu so wani mu k’i wani ba, ko Datti da kwanaki muka yi maka hukunci dan mu natsar da kai muka yi ba wai dan mun ki ka ba dan haka duk sunan da kuka ji an ambata a wajen d’aurin auren d’ayan ku yayi hak’uri”. 

         Ba dan ransu ya so ba suka fita suna tunanin anya zasu d’auki k’addarar rashin ta kuwa?  

       Daren ranar ya kasance rana mafi muni a gare su gaba ki d’aya family d’in cuz ranar ta zamar musu cike da fargaba, tsananin rud’ani…., rikici mai tsananin gaske….. tsarkakiya……ranar da kowa zuciyar shi ke cike tsoron tunkarar wucewan ta. 

        Da ace Datti da Fu’ad na da ikon hana wucewan wannan dare da sun jima da yi saboda tsoron abunda za su bud’e ido su tarar da  shi.

          Washe gari da safe mutanne har sun fara hallara a cikin gidan ana shirye-shiryen d’aurin aure…….Fu’ad tun kafin gari ya gama wayewa ya shiga d’akin Nana ya ta ita a a kwance cikin bargo duk eyes d’in ta sunyi luhu-luhu sun dafe alamar taci kuka sosai d’in nan har zazzab’i ya fara kama ta.

          K’amshin turaren shi taji ta bud’e ido a hankali ta zabura ta mik’e da saurin” Ya Fu’ad na shiga uku za’a aura min miji ban san ko wanene aka zabar min ba…….., kaine mafita a lokacin da duhu ya bayyana a gare ni kaine kake yaye min…….., kaine Ammintacce na mai tsamo ni a cikin dukka wani bala’in da ya kunno min kaiiiiii,

           Kamar yanda ka zamar min Amintaccen nan na baya wanda ya cece ni, ya taimaka min da iyakacin iyawar shi…….don Allah ya Fu’ad ka zamar min Amintacce a yanzu ka fidda ni daga cikin matsalar da nake ciki………,ina tsananin fargabar wanda za’a bani a matsayin mijina. 

         Runtse idanuwa yayi ya bud’e a hankali har ranshi yake jin kukan nata na ratsa shi………muryar shi na cracking yace” kiyi hak’iri na zo muyi bankwana ne……., ki sani ba lallai ne na dawwama a matsayin Amintacce ki ba……….wannan k’aron abu ya juya salo yanzu bani da k’arfin da zan baki kariya…….kiyi hakuri da duk zab’in da kika ga an miki har abada ba zan daina son ki ba……….yana gama fad’a ya mik’e ya fita yana sharar kwalla, tana ji tana gani Fu’ad ya tafi, tafiyan da ta san ba lallai ne su had’u a matsayin masoya ba……. 

       Fu’ad na barin ta d’akin shi nufa ya d’auko car key d’in shi ya fito ya ya kashe wayan shi saboda kar ma a kira shi balle yaji abunda zai d’aga mishi hankali haka ya bar gidan cuz ba zai jure ganin an d’aura auren Nana da wani ba balle ace akaita gidan wani ba, gudu yake ta zafgawa a titin kamar zai tashi sama duk inda ya gifta a motan sai ya bad’a wa mutane k’ura…….., da haka har ya kawo wajen da yake so ya je ya nemi guri a gefen  titi ya parking ya fito ya zauna a saman motar shi, yayin da sanyin huturun da ke kad’awa a hankali ya ratsa jikin shi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Leave a Reply

Back to top button