UNCLE DATTI 1-END

UNCLE DATTI Page 51 to 60 (The End)

         “Yanzu Nana ba lallai ne ta zamu nashi ba? ” Idan ya rasa ta ya zai yi da rayuwan shi bayan ya d’auki son duniya ya d’ora mata?

       “Shi dai ya cire rai da samun Nana domin ya tabbata ba lallai ne a bashi ba.

        B’angaren Datti ma tun safe ya d’auki Sadeeq suka bar gidan ya kashe wayan shi, Usman yayi mishi fad’a sosai da hakan ya tursasa shi lallai lallai sai sun tafi amma sai ya k’afe yace babu inda zai je, haka Usman ya halacci gurin d’aurin aure yana ma abokin nashi fatan samun nasara. 

          Gudun kar Usman d’in yaje ya jiyo mishi mugun abu yayi zumburrr mik’e ya d’au d’an shi suka bar gidan ba tare da kowa ya san inda suke ba……ya saka Sadeeq a gaba yana kuka wi-wi da hawayen shi yana surutai kala-kala” mamanar ka zata yi mana nisan da har abada baza mu cimma ta ba……., shi kenan mun yi loosing d’in ta”.

          “Nana ta zame min magani amma kaddara ta k’i had’a mu ban san ko sai na koma ga mahaliccina ba kafin nan mu had’u a matsayin ma’aurata da ita. Haka yaci gaba da kukan shi yaron na kallon shi kamar zai taya uban kuka. 

        Mutanen gida sai faman k’iran layin su ake yi dukkkk a kashe, tun ana saka ran ganin su abu yaci tura har mutane suka gaji da zaman jira wani aminin Alhaji ya lek’a  me ake jira ba’a fito ba an shanya mutane a waje, a sannan ne suka fiffiito aka fara gudanar da daurin aure. 

        Kamal da Usman sun yi cirko cirko ko wannen shi na so abokin shi ne jarumin da zai mallake Nana sai aikin harara suke sakar ma junan kamar idanuwan su zai tsiyayo, kowannen su sai shan k’amshi yake a matsayin shi na abokin ango suna cika suna batsewa kamar y’ay’an sarakuna. 

        Ana cikin haka Alhaji ya tarar da su yake tambayar su ko sun san inda abokan nasu suke, Usman yace Datti na gidan shi yayi yayi da shi ya fito su tafi amma ya k’i yayin da shi kuma Kamal yace tun d’azu yake k’iran layin Fu’ad baya shiga.

          Alhajin yace yace suje da baba babba su tusa k’eyan shi ya zo gurin d’aurin auren nan, baza su iya da sakarcin su ace ana sure a gidan su dukan su sunk’i hakarta? 

        Babu b’ata lokaci suka tafi ga mamakin su basu tarar da shi a gidan ba haka suka dawo suka fad’a ma Alhaji.

         Cikin narasa aka d’aura har aka gama mutane suka fara neman ango domin su taya shi murna ba ango, sai su Alhaji ne suke ta bada hannu ana musabaha har jama’a suka watsewa.

        Gida suka shige su Umma suka hau tambayar da wa aka d’aura baba Karami ya fad’a musu……..,fatan Allah ya sanya alkhairi suka musu, Alhaji yace kar ayi saurin fad’a musu maganar auren tunda har yanzu babu ango, bayan hakan ba su san wani hali zata k’arb’a zab’in na su ba.”

         Hakan kuwa aka yi har aka gama budurin buki dare nayi aka d’auki amarya aka kaita gidan ta da ke unguwar Federal lowcost, tamfatsetsen gida ne wanda Alhaji ya gida a sirrance shine aka kai amarya ciki aka yi mata jera rasssss gidan yayi kayatu sosai, daga nan aka barta daga ita sai Mardiya.

        Tun Mardiya na ra ran ganin ango har ta gaji ta mata sallama zata tafi Nana take tambayar ta da wa aka d’aura auren tace itama bata sani ba su baba basu fad’a mata ba.

       Shiru tayi har Mardiya ta tafi ta barta kana ta koma tayi lamo a ranta tana fargabar had’a ido da wanda zata gani a matsayin mijin ta wanda zata yi rayuwar aure da shi, to ko ma waye ta d’auki zaman ta da shi a matsayin k’addara cuz iyayen ta baza su tab’a zabar mata abunda zai cutar da ita, kuka taji ya zo mata ba ta hau sheshshek’awa………. 

      

*eedatou*

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14

Leave a Reply

Back to top button