UNCLE DATTI Page 51 to 60 (The End)

” Mission d’ina a lokacin shine sai kin haihuwa na kawo musu jikan su wata k’ila a lokacin Datti zai yarda da laifin har ya furta da bakin shi,
da naga yanda kika d’aga hankalin ki akan lallai sai kin koma gida na shirya plan da Kamal ya kawo ki………nayi mamaki a lokacin na zata zai hakura a lokacin sai na ga ya nuna tauri kai, shine na fito ta hanyar neman auren ki, na tabbata wannan itace kad’ai ya rage mana, ko muci shi da yak’i ko shi ya cimu da yaki.
“Hawaye taji ya zo mata ta sa hannu ta share kana ta jefo mishi wata tambaya” yaya aka yi ma san mun tafi asubi a ranar”.
“Gidan Aunty Aina naje na tambaye ta tace min baki da lafiya Datti ya kai ki asubiti, a lokacin sai naji ban yarda da shi ba zuciyana ya kasa hakuri na sa Kamal ya bi bayan ku kuma ya ki duk abunda ya faru ya fad’a min”.
Wasu sabbin hawaye ne suka fara rolling a saman fuskar ta ya tsuguna a gaban ta tare da ciro hanky yana goge mata” a da na tsane ki sosai na sha alwashin ganin bayan ki daga baya tausayin halin da kike ciki ya kama ni tun daga lokacin na fara jin son ki na kudurta a raina sai na samo ki daga halin da kike ciki”. Yanzu kin fahimci dalilina na zama Amintacce kin?” Ta gyad’a mishi kai tana kuka ya rungumo ta yana lallashin.
Lokaci na dad’a tafiya cikin Nana yanzu ya kai kimanin wata tara a lokacin ne ta ta fara nakuda ta haufo yaro namiji santalele lyakkyawa da shi.
Ranar sunan shi Fu’ad ne ya rad’a ta mishi suna”Sadeeq”.
Bacin Fu’ad da Nana babu mai yarda ya d’au yaron ko da sau d’aya har ya fara girma yayi wayo yana rarrafe…..idan ya rarrafo ya zo gun tsohuwa ta buge hannun shi sai ya sa kuka daga baya ya gane ya ma daina zuwa wurin ta, daga mamar shi sai shi.
Haka kawai Allah ya d’ora ma Datti son yaron idan Nana ta ajiye shi a parlour yana wasa ta tafi ta barshi sai ya turo Usman ya d’au ko mishi ya ya rungumo yaron tsammm cikin jikin shi yana kuka….laifin shi ne da yayi sanadiyar kawo shi duniya a kazamtacciyar rayuwa……., yana sane da ko wa baya son shi……ko da yake shi ma da yake uban shi bai bayyana ma duniya ba ya k’arb’e shi a matsayin shi na d’an shi ba balle wasu da ban……, tausayin kanshi da yaron yake ji………da dai bai so zuwan shi duniya ba ashe da rabon shi ma zai ajiye nashi ne yake mu’amala da Nana…….
So tari idan ya fito parlour yana wasa Datti na jin muryar tsohuwa tana sheganta mishi d’a da marar asali…….hakan na yi mishi zafi sosai a ranshi…..amma babu yanda ya iya.
Wata rana yana d’aki bayan Usman ya kawo mishi shi ya tafi, Datti na wasa da yaron har yayi barci a gefen kafad’an shi………Nana da taji shiru ta fito tana neman shi ta duba ko ina bata gan shi ba…….gashi babu wanda ya damu da ya san inda yaron ya tafi…….sai taji kuka ya zo mata mai tsananin k’arfin gaske” da ace d’an sunnah ne a yanda aka ji wurin shi shiru da hankalin kowa sai yafi tashi amma da yake ba ta hanyar aure aka same shi ba babu wanda ya damu duk da dai suma sun san ya b’atan.
Dabara ne ya fad’o mata ta duba d’akin Fu’ad ko zata gan shi…., haka ta haye sama tana sharar hawaye…….ga mamakin ta tana shiga ta ganshi yana sharar barcin shi hankalin shi kwance shima baban nashi barci yake yi……da masifa ta zo zata kwace d’an ta Datti ya bud’e ido ya sauk’e su fessss akan ta.
” Ina zaki kai min d’a?
“Maganar sai ya bata haushi taja tsaki” au dama kana da d’a ne ban sani ba…….,
“Hannu ta kai zata d’auke Sadeeq yayi saurin rik’o hannun ta yana murzawa a hankali,” babyna i’m sorry na putting d’in ki through much pains kiyi hak’uri rabon yaron ne ya sa”.
Sai ga hawaye ya fara bin saman fuskar shi” Uncle kenan baka ji kunyar fad’a min maganar ba ina ce tun yana ciki ka sheganta min shi kuma kayi niyar kashe shi at the end kuma kana beginning d’ina bayan har yanzu kana claiming baka san komai ba…….kuka ne ya kwace mata ta hau sheshshek’awa…..Uncle me jikina yayi maka kake so? Me yasa ba zaka amsa laifin cewa Jikina kake so ba………., Uncle ka saka rayuwa ta cikin bakin ciki……. Yaure tsakanina da kai bashi yihuwa ko da ace ba jinin mu d’aya bane da aunty Aina…….., kamar yanda ka d’auki lalurar ka a matsayin k’addara ina so ka d’auki rabuwa da ni a matsayin k’addara, bana son ka Uncle i hate you!!!!!!
Yanda yaji maganar ta a ranshi kamar saukan mashi ya runtse ido da sauri zuciyan shi na mishi azabar rad’ad’i……k’almar rabuwa da baby shi ya fi komai d’aga mishi hankali a duniya…….gashi k’arfi da yaji so ake a raba shi da ita.
“Baby da nayi miki laifi amma na tuba ki yafe min…….Sadeeq jinina ne ina k’aunar shi fiye da yanda kike tunani……wallahi baby da kin san irin k’aunar da nake mishi baki isa ki furta hakan ba”.
Murmushin yake tayi wanda yafi kuka ciwo tace” da kana k’aunar shi tun kafin yazo duniya baka yi yunkurin hana shi zuwa ba…….., kana ganin irin tsanar da ake mishi a cikin gidan nan amma baka yi yunkurin komai ba……..,
“Shiru yayi yana tunani shi kan shi ya san abunda ta fad’a gaskiya ne shine wanda ya kamata ya share mishi hawaye tunda shi ya yi silar kawo shi duniya ta gurb’atacciyar hanya…….yana cikin tunanin ne har ta d’auki Sadeeq ta tafi da shi bai sani ba.
Ba ita ta zame ko ina da shi ba sai d’akin ta da yake b’angaren tsohuwa kusa da na Aina ta dire Sadeeq akan gado time d’in har ya tashi a barci yana kuka………, nono ta bashi ya k’i k’arb’a sai kuka yake yi da ta rasa abunyi sai itama ta rushe da kuka tana mishi wasa tana wak’a ko zai yi shiru…….taho taho d’an yaro nayi maka gata………,kowa baya sonka yace kai shege……,duka hantara da kyamar ka suke yi………tunda uban…..ka ya k’i ka……ba wani mai….maka gata.
Ta jima sosai tana wakar ta bata sani ba ashe Fu’ad ya shigo ya tsaya yana sauraren ta……haye mai uban d’umi yaji ya sauko mishi sai ya rungumo ta ta baya yana kuka kamar k’aramin yaro…….” Ni zan bashi kulawan da ya rasa a wajen mahaifin shi……ba zan bari ya wulakanta ba dai-dai da rana ba zan bari ya san cewa bani na haife shi ba……….d’an Datti nawa nima.
“Ya Fu’ad Uncle Datti mugune…..duk da dai na san cewa ba ta hanyar aure muka same shi ba amma na tabbata babu uban da zai kyamace d’an shi……., Sadeeq bai da wani gata a gidan na, kiyayyar shi tayi yawa a gurin kowa na gidan nan………
“Banda ni da ke Nana idan kowa ya k’i shi mu muna son shiiiiii.
Kuka suke yi sosai daga su har yaron kamar dama can yana ya san abunda suke fad’a .
Shirye-shiryen bukin Nana ya kankama a lokacin ne Datti ya d’aga hankalin shi ya fito musu b’aro-baro yace shi zai aure Nana…..mamaki sosai suka yi har suke zargin anya kanshi d’aya? Ya aure ya, ya aure k’anwa.
Ana gobe d’aurin auren hakalin shi idan yayi dubu ya tashi…..da dai ya ga tabbas da gaske ake za’a d’aura auren nan ya shiga rokon Nana akan karta amince a d’aura mata aure da Fu’ad shi zai aure ta……tace aure babu fashi da yana son ta ya zalunce ta.