UNCLE DATTI Page 51 to 60 (The End)

Da abu ya dame shi ya same su Alhaji yana kuka yace” zan fad’a wallahi baby d’in nan nawa…….don Allah ku karku raba ni da ita…….., daga nan ya kwashe komai ya fad’a musu har da hotel d’in da yake kaita suna hutawa duk ya fad’a musu”
“Sosai suka firgita da jin abunda ya fad’a” da gaske ne kai ka yi wa Nana ciki”.
“Eehhh ehhh wallahi nine don Allah ku yafe min”.
Inalillahi wa ina ilaihiraji’un sai yanzu suke jin k’amshin gaskiya akan abubuwan da Nana take fad’a a baya……garin yaya suka yi sakaci har hakan ya faru? tambayan da kenan suke fad’a a zuciyoyin su.
Alhaji da ya cika da tarin al’ajabi da b’akin ciki yace” kai da muke tsammanin ba lafiyayye bane yaushe ka samu lafiya ka aikata wannan b’arnar.
“Lalura ce nima ba da son raina bane na d’aura ma kaina sha’awar ta…….
Aina taji wani irin mahaukacin kuka ya zo mata ashe dama Datti cin amanar ta yake bata sani ba? Ina alkhawarin da ya d’aukar mata a baya na cewa ba zai cutar da ita ba? Me yasa ita da take mace ta rik’e mishi kanta shi kuma bai rik’e mata kan shi ba yayi taraiya da k’anwar ta”.
Kallon Nana ta yi wacce tun d’azu take rusar kuka tace” Kaico na da na yarda da yaudarar d’a namiji fiye da rayuwar k’anwata……..duk irin abubuwan da Nanar take fad’a ta toshe kunnuwan ta k’arshe ma tace k’azafi take mishi ashe yaudarar ta yake da kalama ta.
Ita dai bata ga amfanin zaman aure da shi ba bai amfane ta da komai ba……tana nan tana rik’e mishi kanta amma shi jikin wata yake so ba nata ba……….
Tsohuwa dai baki ya mutu sai suma take yi tana farfad’owa, duk irin tsanar da take nunawa Sadeeq ashe da uban shegen a gidan, kaiiiii Datti baiyi halin bugun girma ba….. ba a banza abar shi ya dame shi da ciwo ba, a d’au yarinya a bashi k’arshen sakamakon da zai nuna musu kenan.
Mari baba Babba ya wank’a mishi ya had’a mishi naushi da k’afa kan kace me sai ga jini ya b’alle mishi a baki………
Ka ban kunya wallahi ban tab’a tsammanin haka daga gare ka ba……..sirrin da kake boyewa kenan da baka nuna ba ka sa muna zaluntar yar uwar ka”.
“Umma dai kunya had’e da bak’in ciki duk ya ishe ta ace d’an da ta haifa da cikin yayi tarayya da k’anwar matar shi uwa d’aya uba d’aya? Tausayin Nana da Sadeeq ya mugun kama ta musamman Sadeeq da bai san komai ba suka d’auki k’aran tsana suka d’aura mishi.
Hawaye taji ya soma zubo mata ta matso cike da tarin takaici tace” ba mu da muka baka amanar yarinya ka cutar ba kanka ka cutar…….., tana gama fad’a ta d’auki Sadeeq ta mik’a mishi d’auki d’an ka tafi da shi daga yau mun cire ka acikin family d’innan bama son sake ganin ka.
“Sai a sannan ne hakan shi ya mugun tashi , don Allah Umma kiyi hakuri ta rainar min shi idan yafi haka wayo sai a dawo min da shi”.
” Uban ka nace, ba za ka d’auke shi ba ko har sai ka hasalini nayi maka baki…….da muka baka amanar ta mun had’a da shi ne ina ce kai ka samo shi daga baya……..don haka ka tafi ka bamu wuri.
“Yaron kamar ya san za’a raba shi da uwar shi ya saki kuka yana mik’a mata hannu ta d’auki shi sai tausayin shi ya kama Nana taje da gudu tana kuka zata k’arb’e shi baba babba ya rik’e ta da sauri……barshi ya tafi da tsiyan shi raino kam kin gama yi mishi sai ya d’aura daga inda kika tsaya.
Tana ji tana gani haka Datti ya tafi da Sadeeq uba kuka d’a kuka uwa kuka…….da dai sauran masu saurin kuka suma suna taya su.
Datti na fita Fu’ad yayi saurin bin bayan shi ya sha gaban shi” yaya ka ga takun”,
Nayi amfani da kwakwalwata na cusa maka k’iyayyar Nana a zuciyan ka………, a halin yanzu tafi kowa tsanar ka……., ka san me? Na raba ka da ita ne dan na cimma burina kuma” kana ji kana gani sai na aure Nana na cusa maka bakin ciki wanda zaka dawwama a cikin ta.
” Wawan shak’a ya kai mishi da hannun shi d’aya yana huci kamar mayunwacin zaki……. Idan har ban aure ta ba kaima baka isa ka aure ta ba……., bangaje hannun shi Fu’ad yayi ya shige ciki ya barshi.
Haka ya ja yaron shi ya bar gidan daga bakin k’ofa ya tsaya yana k’are ma gidan kallo zuciyan shi nayi mishi zafi…….
*eedatou*
*????SHINNING STARS WRITERS ASSOCIATION*
”’The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers.”’
https://m.facebook.com/110896360504039/photos/a.110896457170696/110898470503828/?type=3&source=45
???????????? *UNCLE DATTI*????????????.
”’JIKINA YAKE SO!”’
©
*eedatou✍????*
“`Follow and ✅ote me on Wattpad“`: *eedatou*
~Attention pls akwai mistake a page na baya, idan akace gobe ne auren Fu’ad da Nana har aka kore Datti a gidan, ga abunda zan saka a wajen” lokaci na tafiya gashi yanzu bukin Nana na dad’e matsowa”, ban sani ba na saka wancan laifinane da ban editing ba ku min uzuri ku gyara, ngd.~
4️⃣1️⃣—4️⃣2️⃣
Mota ya shiga da Sadeeq a hannun shi ya had’e kan shi da steering motar yana rusar kuka har da majina……..su Umma basu mishi adalci ba da suka raba shi da Nana sannan suka raba Sadeeq da mahaifiyar shi……….., kallon Sadeeq yayi a lokacin har ya gaji da kuka yana sake ajiyar zuciya……….rafa suman kan shi yayi sai yaji sabon hawaye ya sauko mishi” kayi hak’uri son nayi sanadiyar kawo ka duniya ciki kazamin rayuwa……….., da ace ta hanyar aure aka same ka da baza raba ka da uwar ka ba…….hawaye msi d’umi yaji ya sauko mishi sai ya k’asa tsare su……….da kyar ya iya d’aga ya jan mota ya bar gidan……….
Ba shi ya tsaya a ko ina ba sai a gaban wani makeken shago na ga ya parking ya fito da Sadeeq a saman kafad’an shi ya shige ciki……..,
Shopping yayi ma yaron sosai na kayan abincin yara da rigunan sawa da wando, kayan wasa da dai sauran su daga nan ya nufi gidan shi.
Tun a hanya Sadeeq ya fara barci har suka iso bai tashi ba ya samu ya kwantar da shi ya koma gefen shi ya kwanta tare da jawo shi jikin shi sai ga hawaye ya fara kwaranya a fuskan shi.
Cikin dare yaron ya farka yana ta sandara kuka sosai kamar ranshi zai fita……., Datti ya tashi a firgice ya d’au ledar da ya shigo da shi ya had’a mishi costant yana bashi a baki maimakon ya karb’a sai ya hau kawar da kaiiiiii shi dai mamar shi yake bukatan gani a lokacin.
Hawaye na bin fuskan Datti yana d’aga k’afa da kyar dick d’in shi na mishi zafi amma ba sosai ba yaje ya d’auko zani a d’akin Aina ya goya shi yana yawo da shi a parlour duk Sadeeq sai dad’a k’ara kuka yake kamar zuga shi ake…..hankalin Datti idan yayi dubu ya mugun tashi……” Shi kam ji yake ya ma fi yaron bukatar bukarta hakuri kawai ya fishi. Rasa inda zai yi da shi ya kunce zanin da sauri cikin daren ya zare car key d’in shi ya nufi gidan su Alhaji ya hau buga musu k’ofa su bud’e, duk suka firfiito cuz daga d’akunan su suna jin kukan yaron karancewar dare ne”.
Zubewa yayi a gaban Nana ya mik’o mata yaron hawaye nata kwaranya a idanuwan shi” don Allah ki k’arbi d’an ki kar ki bari a raba ki da shi……..ba don hali na ba ki rik’e Sadeeq kina jin irin kukan da yake yi ki tausaya mishi……..help me, help me please i beg you”.