UNCLE DATTI Page 51 to 60 (The End)

Fu’ad na ganin sai tausayin shi ya kama yaron da yana da halin baiwa Nana d’anta da yayi.
Wani mahaukacin kuka taji ya zo mata tana so ta k’arb’i yaron har ranta tafi bukantan shi a kusa da shi…….me yasa su Ummi basa tausayin ta basa tausayin Sadeeq dan ya kasance ba d’an sunna ba?
“Umma taci ka fammmmm da shi sosai ” Ya san ba zai iya rik’e d’an ba ya haifa ?wa ya ajiye da zata yi rainon shi? Tsabar b’acin rai ji take kamar ta wank’a ma Datti mari…..bai ji kunyar abunda ya aikata ba shine yake cewa a rik’e mishi d’an shi”.
” Kaiiiii Abubakar ka fita a idona na rufeeeee, wai ba anyi maka iyaka da gidan nan ba?
“Ummi don Allah!!! don Allah ki taimaka kar kiyi min hakan…….ki sassauta min hukuncin nan ya min sauri da yawa ba zan iya d’auka ba”.
” Baba na san kaiii zaka fi Umma fahimtar halin da nake ciki……kaima namiji ne kamar ni…….baba ka san jarabawar da nake ciki na lalura ta……, ka fahimtar da ita cewa ba laifina bane, laifin k’addara na ne……..tasssss ya ji an d’auke shi da wani mahaukacin mari wanda ya gigitar da shi saura kad’an ya saki Sadeeq ya fad’i k’asa Nana na ganin haka tayi tsalle ta rik’e Sadeeq tana kuka wi-wi, shi kam da ya tsorata ya dad’a k’ara sautin kuka ya gama sadakarwa cewa zai fad’i ne.
“Rungumo shi ta yi tsammm jikin ta tana mai jin tausayin shi a ranta har take nadamar kin biye ma Datti da tayi lokacin da, shi kam Sadeeq sai ya manne a jikin ta ya hau ajiyar zuciya.
Scene d’in ya matuk’ar ba ma Aina tausayi sosai sai ta hau ba ma Umma hakuri…….please Umma ku tausaya wa yaron ba dan halin uban shi ba……” Saurin katse ta tayi cikin fushi” kee rufe min baki kin fini sanin abunda nake yi ne? Idan kika kara saka baki a maganar nan sai na hada da ke naci mutuncin ku……..marar kishin kanta kawaiiii.
“Ke Nana wuce ki shiga cikin gida”.
Zata tafi kenan baba babba yace” mik’a mishi d’an shi……..,kwalla ne ya zubo mata ta hau sharar su…….”babu yanda ta iya haka ta mik’a ma Datti Sadeeq, cikin wani irin hali Datti yace” kema kin goya bayan na tafi da shi kenan? Kin goya bayan a raba ki da d’an ki……., kin manta da ranar da cike da cikin shi kike cewa a bar miki d’an ki da hannun ki zaki raine shi…….zaki yi mishi gata ashe irin gatan da zaki yi miki kenan? Nana idan na k’i Sadeeq yana ciki ke kika so shi har ya zo duniya wani riba zaki ci in kika rabu da shi idan kika rabu da shi? Dama kin haifo shi ne dan ki mishi tab’on da zai nuna mishi baida gata? A yanda yake maganar muryar shi har tsarkewa yake yi, a take jikin shi ya d’auki rawa…………,
Yanda take jin maganar shi a ranta kamar diran kifiya…….., ba k’aramin ratsa mata kwakwalwa yake………bata da wani zabin da ya wuce ta bi umurnin iyayen su, haka tana ji tana gani ta mik’a mishi d’an cakkkkk ya rik’e hannun ta ya had’a da nashi suka matse Sadeeq gam a jikin shi” Son ka taya ni rokar mana mommy karta guje mu we really need her by our side…………, karta bar mu muyi maraicin ta………”, sai hawaye ya gabgaro ma yaron kamar ya fahimci abunda uban yake fad’a ya hau mik’a mata hannu yana so ta d’auke shi……….,matsanancin kuka ne ya kwace mata ta shafa tare da bashi peck tace” i’m sorry for letting you go, forgive your me son”, tana gama tayi d’aki gudu.
Wannan k’aron sai da zuciyoyin su ya k’arye saboda da tsananin tausayin yaran, Ummi ce dai sarkin kuka ta shige gida da sauri tana sharar kwalla.
Aina kam sanda Datti zai tafi da Sadeeq ta rushe da kuka tana rik’e k’afar baba babba tana pleading d’in shi kar a bari Datti ya tafi da d’an baba yace sai dai tayi hakuri dole ne ya d’auki hukunci komai tsananin zafin shi shi zai saka gaba idan ya ga wani mai hali irin nashi ya bashi shawarar.
Haka suka koma gida tana waiwayen Datti” duk da dai ta san cewa yaci amanar ta, ya ci amanar zumunci amma yana tsananin bata tausayi………, some times ma idan ta zauna tana tunani sai ta ga kamar ba laifin shi bane……., ace a bama kura ajiyar nama kura kuran nan ya tabbata yana tsanin bukatar naman me zai hana ya ci………, ko ace majinya ci ne ciwon ajali ya kama shi sai akace ga maganin da zaiyi amfani da shi dan ya warke……duk talaucin shi sai anyi yanda akayi aka samo maganin dan ya warke.
Da wannan take k’afa hujja take ganin ya kamata a sassauta mishi hukunci yayi mishi sauri da yawa…., sai ma take jin kamar idan aka aura ma Fu’ad Nana hakan bai dace ba………., cikin daren ta lek’a d’akin Alhaji cikin sa’a ta same su tare da tsohuwa tana sharar hawaye tace” don Allah Alhaji ku sassautawa Datti hukuncin da kuka d’auka…….., ba dan shi ba ko dan lalurar da ke damun shi………
Idan har Nana ta kasance magani a gare shi me zai hana a bashi auren ta ni na hak’uri da shi ko da na kasance tare da shi ba amfanin da zai yi min kuma ba zai daina bibiyar Nana ba………., ina so ku duba magana ta da fuskan fahimta ba wai goyon bayan shi nake yi ba hasalima tausayin shi nake ya had’u da jarrabawa kala-kala.
“Shiru Alhaji yayi yana sauraran ta bai ce komai ba tsohuwa ta fusata sosai tace” kaji ja’irar banza, kina tausayawa yaron da ke bai tausaya miki ba……..Nana kanwar ki ce uwa d’aya uba d’aya shi kuma mijin ki ne me yasa da ya tashi aikata tsiyar shi bai tuna da hakan ba.
“Share hawayen ta ta yi tana mai jin zafi a zuciyan ta” tana son Datti so na hak’ik’a shi yasa zata sadaukar da rayuwar ko dan ceton nashi rayuwar………., ba dan lalura ba ta san halin Datti ba zai aikata hakan ba………hasalima k’addarar lalurar da shi ne ya jawo hakan.
Matsanancin kuka ta rushe da shi cike da tausayin kan ta………., ashe akwai ranar da har zuciyan ta zata ji tana so ta mallaka ma wata mace bayan ita?
Sai kuka take da iyakacin k’arfin tsabar kuka har jikin ta bari yake yi, Alhaji dai yana jin sai dai ya rasa ta hanyar da zai b’ullo wa lamarin……idan yace zai yarda da k’uddurin Aina me zaice ma Fu’ad bayan irin taimakon da ya dinga yi mata ya samo ta daga tarkon Datti bayan da dukan su suka yi watsi da maganganun ta? Idan kuma aka d’aura auren Fu’ad da Nana ta yaya za a magance matsalar shi bayan an raba shi da maganin matsalar……gashi abu yazo da tsananin rud’ewa dukan su suna tsananin bukatan ta wa za’a ceto ?
Sai uban gumi yake had’awa shi kad’ai ya rasa samo mafitan ta yanda zai b’ullo ma lamarin.
“Ki tashi ki tafi zan nemi iyayen naku duk hukun cin da suka dauka akai idan marar dad’ine ina so kiyi hak’uri da shi, Fu’ad da Datti duk d’aya ne a wajen su baza so d’aya ba su bar d’aya, duk matsayin su guda ne.
Shikenan Alhaji na gode, fita ta yi daga d’akin ba ita ta zame ko ina ba sai d’akin y’ar uwar ta ta tarar da ita ta had’ai kai da gwiwa tana aikin kuka ba……, ba komai ne ya saka ta kukan ba illa rabata da aka yi da d’an ta.
Zama tayi a gefen gadon ta jawo ta jikin ta suka rushe ta mahaikacin kuka babu mai rarrashin d’an uwan shi, cikin dishashshiyar muryar da bata fitowa Nana tace” me yasa ba’a min adalci ba aka raba ni da d’ana wanda tun yana ciki ni kad’ai na sha fama da shi har na haife shi ya zo duniya, opon duk wahalhalun da na sha babu wanda ya kawo min d’auki sai daga baya za’a raba ni da shi…….., idan su Umma gudun abun kunya suke yi ni da nayi abun kunyar ina son abuna zan k’arb’a d’ana na gudu da shi ta inda babu mai jin d’uriyar mu balle a same mu”.