UNCLE DATTI Page 51 to 60 (The End)

Yana maganar tazo mishi kamar dirar mashi…., a basata yaji maganar bai tsammaci zai samu amsa daga gare shi ba”.
” Murmushin takaici ya sake” Fu’ad kenan babu abunda ka sani game da rayuwar duniya kwakwalwar ka tayi kad’an ta fahimtar da kai hatsarin da ke tattare da auren Nana.
“Idan ka aure ta gangar jikin ta kadai zaka aura zuciyar ta na tare da ni……..,ina so ka rubuta ka ajiye sai ana son ka kafin a mallaka maka zuciya da gangar jikin ka…….ko a hakan na barka ya kamata ka fahimci inda magana na ya dosa…….ga misali nan ka gani a gaban ka ba tilasta ta nayi ba ta kawo min kanta…..muka dirji juna”, uhhmm ina taya ka bak’in cikin auren fanko, shuk’ar wani wanda ya raya ta da ruwan jikin shi shi yake ban ruwa mata”.
Kunnuwan ta tayi saurin toshewa da tafukan hannun ta zuciyan ta na bugawa da k’arfi.
Idan ta fahimce shi yana nufin kawo mishi kanta kenan tayi? Lallai yayi mata gadarzaren da warware shi zai yi wuya, da na sani iya da na sani tayi shi fiye da a k’irga na zuwan ta gidan.
“Fu’ad na nan daskare a guri d’aya ya kasa ko da kyaklyawan motsi, bakin shi yayi mishi nauyi ya kuma rasa k’almar da zai yi amfani da shi don ya rama abunda aka fad’a mishi kasa cewa komai yayi da sauri ya fita daga parlourn zuciyan shi nayi mishi tafarfasa, Nana ta bi bayan shi da sauri Datti ya shafa suman kanshi yana murmushin mugun ta yayin da a heart d’in shi yake cewa” kiyi hakuri baby duk son na mallake ki ne ya jawo haka, ya biyo ta wani hanya ne ya nad’a min tarko kuma tarkon ta kama da ni, nima dole na biyo mishi ta wata hanyar ni da shi zan ga wani jarumin ne zai yi nasarar auren ki”.
B’angaren Fu’ad kuwa a waje ya tarar da Aina ta rik’e k’ugu tana jiran shi cuz ta kasa jure tsayuwa……., fuuuu ya zo zai wuce ta tayi saurin shan gaban shi tace” baka ganni bane kake k’orarin wuce ni?
Yayi yayi ya rik’e kukan a ranshi amma ya kasa sai ya fashe da mahaukacin kuka kamar k’aramin yaro” auren Nana zai yi ya aure ganganar jikin ta kamar yanda Datti ya fad’a? ko kuma hak’ura zai yi da ita da ita ya fasa auren ta?
Idan yace zai fasa auren ta kenan Datti yaci bulus a kan shi? Idan kuma yace zai aure ta bai san wani irin zama zai yi da ita ba bayan ya kamata red handed da shi sun gama aikata zina”.
Da ya d’auka cewa tilasta ta yake yi kafin ya samu biyan bukatan shi shi yasa tausayin ta ya shige shi har ya fara son ta yake jin zai iya zaman aure da ita, sai yanzu ya fahimci cewa itama jin dad’in abun take yi munafurtar shi take yi kamar bata so ashe itama jikin shi take so! tunda har ta iya kawo kanta gare shi.
Shiru gurin ya d’auka banda sautin kukan shi babu abunda ke tashi a wajen, sai kan Aina ya mugun d’aurewa tace” fad’a min mana baka samu Nanar bane?
Kai ya girgiza mata hawaye na ta zarya a saman fuskar shi” aunty aina nayi mugun gamo…idanuwa na sun gane min abunda har abada ba zan so na sake gani ba………tambayar shi ta kuma yi tana cewa”me idanuwan naka suka gane mak…….cakkk maganar ta mak’ale a mak’ogoron ta ta kasa kasa fitowa……..ba komai ne ya saka ta hakan ba illa ganin Nana da tayi ta mak’ure a guri d’aya tana kuka ga suturar jikin ta a yage”
“Whatttt”, ta fad’a a mugun mamakin ce ta tsorata matuka da ganin ta, sai yanzu ta fahimci inda maganar Fu’ad ya dosa wato kama Nana yayi kenan suna aikata zina.
Inalillahi wa’inna ilaihiraji’un me zata yi banda hawaye.
” Ashe ba za ki nutsu ki san mutumcin kanki ba, sai ki bari namiji na gara ki yanda ya ke so……..,wace irin rayuwar akuyanci ne kika zabar ma kanki?
“Ga wanda ya taimaka miki zai aure ki kin zo kina bibiyan wanda ya b’ata miki rayuwa?
Nana na kallon ta tana mamakin yanda itama Ainar tayi mata mummunar fahimta, ta bud’e baki zata yi magana Aunty Aina tayi saurin d’aga mata hannu ta hanyar dakatar da ita………….tace yi min shiru kar ki fara tunanin maganganun ki za su yi tasiri a zuciya na……., tsakanin ki da Datti na rasa gane wa ke son jikin wani”.
Kuka ne mai tsananin k’arfin gaske ya kwace ma Nana tace” don Allah Aunty ki fahimce ni ban aikata abunda kuke zato ba wallahi Sadeeq naje gani shine fa……..
“Kar ki raina wa mutane wayo wannnan rigar da aka yaga ta Sadeeq din ya yago?
Ajiyar zuciya ta sauk’e cikin kuka tana jin zafi a ranta bata da kalmar da zata yi amfani da shi ta wanke kanta.
” Aunty ba zan iya ci gaba da tsayuwan nan ba zuciya ta zata iya faso k’irjina ta fito………, yana fad’a ya sa kai ya bar wajen Aina da Nana suka bi bayan shi da sauri.
A mota suka tarar da shi Aina ta zagaya ta d’ayan gefen ta shiga, ganin haka Nana ta kai hannu ta bud’e gidan baya zata shiga, Aina tace ai sai dai ki tafi da k’afar ki ko kuma ki koma wajen wanda kika zo gurin shi ya samar miki abun hawa amma mu kam baza ki bi mu”.
“Fu’ad d’aga mota mu tafi kar haushi ya sa na kai mata bugu dan a yanda nake jina din nan zan iya b’arar mata da hak’ora.
Bayan sun iso gida Aina tayi wuffff ta shige gida ko ta barsu yayin da Nana da Fu’ad ke cikin mota ta k’i saukowa shi kuma yana jiran ta fito.
Gajiya yayi da jiran ta ya juyo yana masifa” ba za ki fita ki bar min mota ba ko sai nace miki ki fita”.
Marairace murya tayi tana sharar kwalla” don Allah ya Fu’ad kayi hakuri ka saurare ni kaji mai zan fad’a Allah ba abunda ka d’auka bane….., kaima ka san ba zan yarda na kuma tafka kuskuren da nayi a baya ba”.
Iska ya fuzar tare da bugun steering d’in motar kafin ya juyo ya tsare ta da firgitattun idanuwan shi suka kad’a zuwa launin ja” me zaki fad’a na gamsu da shi bayan abunda idanuwana suka gane min?
Upon all the fightings and sacrifices did you end up betraying me, nayi trusting d’in ki amma kin yi breaking truest d’ina ta yaya kike so na k’ara yarda da ke? Idan muka yi aure wani irin tarbiya zaki ba ma yara na?
I’m trying to make you a woman that every man will be proud to have you but ki failing d’ina Nana,
Kin tozarta ni a gaban Datti kinanta da me yace? Cewa fa yayi ke sauran shi ne, kin san yanda k’almar nan take da zafi? Yanda kika zan zafin fitan rai haka nake jin ta a raina”.
“Kukan ta ne ya dad’a tsananta, she don’t have a single wads to prove her self. Tsabar kukan da take yi sai da taji azabebben ciwon kai ya kama ta.
Hanky ya mik’a mata yace ta karb’a ta share hawayen ta kuma ta tabbatar ta daina kuka kafin ta shiga gida, idan su Ummi suka tambaye ta tace tare suke da shi.
Kai ta gyad’a mishi ta kana ta k’arb’a ta share tana gamawa ta fita daga motan ta shige gida.
Yana nan a zauna a cikin mota he cried bitterly kamar ran shi ake zarewa a lokacin shima, tsabar kuka har majina yake had’awa da kyar ya iya fitowa yayi ma motar key ya nufi d’akin shi ya danna lock ya kwanta a take jikin shi ya d’auki zafi rad’au.
B’angaren Nana kuwa cikin sa’a har ta shigo room d’in ta bata had’u da kowa a hanya ba.