WATA RANA Romantic hausa novels complete

Akai akai Asmy ta shiga tsaki ganin har ynxu sallau driver bai karaso ba ,Aunty zulfa da ta hasala tace wae ubanwa waye sa’anki dakike famar jawa mutane tsaki??”
Ta Dan turo baki tana kallon ,yayar tata Toni sabida Allah dake nake xakibi ki sakawa mutum ido takara sa mganar cike da rashin kunya.”
“Kwafa zulfa tayi xaki sani ne bari mukara sa gida dai- dai nan sallau ya karaso Gaba dan su suka shiga side din baya gaskiyya Mln sallau ka dde ,cewar Asmy yi hkuri Asma’u sae da naje nasha mai Aunty zulfa tace Dan Allah daena kula mahaukaciyar mukara sa gida.
” ke dai ce mahaukaciya wlhi bani ba.”
Ta fada cike da tsiwa zulfa takai mata mari tayi saurin dafe kuncinta mln sallau sae famar basu baki yake bakin Asma’u yaki ya mutu haka suka isa gida suna gama parking tari ga zulfa fitowa.”
Da gudu ta karasa cikin gida falo ta saki jakar karatun ta aza hnnu akae ta saki ihu dai-dai nan yah Anas ya fito shida Abbansu.”
“Wata uwar tsawa yah Anas yyi mata ke mahaukaciyar inace?” Kuka ta saka Abba ya karaso yna tambayr meya faru ?”
Dae -dae lokacin Aunty zulfa ta karaso cikin kuka ta fara mgana Abba ka daukar min driver ni na gaji da shiga mota daya dasu Aunty zulfa bbu abunda suka iya sae cin zalina.” Ta fada hawaye na xubar mata nan Abba ya juya kan Aunty zulfa ke Zulfa’u meya faru??”
Anan ta fadawa Abba komae ,nan ya juya kaina Asma’u bakida gaskiyya meyasa bakya yiwa yayunki biyayya?”..Abba in….saurin katseta yyi idan bakibar wannan halin naki ba baxamu shirya ba..anan yasa kai ya fita yah Anas yabisa a baya sae famar dokamin harara yake na murguda masa baki tareda saurin dauke kaina dakin mama na nufa ,yyinda Aunty zulfa tayi dakin su…
WATA RANA !
N@ Asmy b Aliyu..
©Haske Writer’s Association…
19
“Alh.Umar Aliyu omra haifaffen Dan garin kano ne A kano aka haifesa anan yyi karatu hka acikin kano ya girma ,mahaifinsa ya rasu tun kafin yaxo dunia sae mahaifiyarsa da ya tarar Da kuma yayarsa Asma’u Wanda daga ita sae shi…
Yana da shekara goma Allah yyiwa mahaifiyarsa Rasuwa ,lokacin baima San kansa ba yyinda rikonsa ya dawo hnnun kawun sa shida yayarsa Asma’u tana gama secondary skull aka aurar daita,ga wani chairman na local government.”
Barin Asma’u gidan Umar yaga rayuwa a gidan kawun nasa da tsangwama ,ga matan kawun nasa rasuwar kawun su Asma’u ta dauke Omar rikonsa ya dawo nta ,karatun sa da girman sa A hnnun yayar tasa yake kasancewar mijinta Dan siyasa ne yana sonta sosae ,haka yyi karatunsa a Jami’ar ahmadu bello dake xaria A fannin Economic computer”…
“A hka ya samu Aiki ” A pilgrim ,yana da matar aure daya Hajia hadiza shekara daya da aurensu ta haifi Anas ,yana cika shekara biyu aka haifi Aliyu Wanda suke kira Haidar ,shima shekarar sa biyu aka haifi Abdul hameed.”
Daga nan kuma shuru shekara hudu ,Shuru daga Aliyu kwatsam Mama ta samu ciki nan Alh.Omar ya dinga Addu’ar Allah ya basa macce yasa suna yayar sa Asma’u wadda bata taba haihuwa ba. (Blood cancer)”..
Shine Ajalinta mutuwar tashigi Alh.Omar duk tsawon wannan shakarun bata taba haihuwa ba.” Haka arzikin Alh.Omar ya bunkasa tun yana Aiki a karkashin pilgrim ,duk shekara sae yaje hajji ko omra anan ne ya samo sunan Alh.Omar omra.”
Matar sa na haihuwa aka samu shema’u haka dae Abba ya rada mata inda yace idan Allah yabasa wata xaisa mata Asma’u xokiga yarda yayunta ke nuna mata so shekara biyu akayiwa shema’u kanwa wato Zulfa’u anan yah Hameed ya samu abban su Abba har yau baka yiwa mai sunan umma takwara ba?”
Wato yana nufin Asma’u tun kafin rasuwarta dama Abdul hameed ne nata shine mai sunan mijinta ,Abba yyi murmushi karka damu Abdul hameed idan maman ku ta sake haihuwa sunanta Asma’u ko bayan raina.”
Shuru shuru hadixa bata kara samun cikiba shekara shidda har sun fidda rae sae ga cikin Asma’u nan suka Shiga murna Allah yasa Maman su tasamar masu kanwa macce ,cikinta na shiga wata Tara tayi doguwar na kuda wadda bbu Wanda yasa ka ran hadiza xata rayu ,bata taba shan wahalar haihuwa ba irin wannan kwana biyu tana na kuda.
“A yinin na ukku ne ta haifi katotuwar ya’rta mai kama da ubanta sak! Dan duk cikin ya’yansa Asma’u ke diban kama dashi sauran kuma duk mahaifiyar suce kasan cewarta bafullatanar Adamawa ce..
An sha shagali sosae A bikin Asma’u hka yayunta na nuna mata so hka ta taso cikin gata da kulawa a kowane fanni…
Da yake Hajia hadiza ma’akaciya ce hka kuma kwarrrar likitar mata anan asibitin Mln aminu kano ,ita da kanta tayi addu’a Allah ya tsayar mata da haihuwa hka Asma’u ta xama auta.
Barin ta biyu ,bayan yaye Asma’u haka ya’yan su Anas da Aliyu a tare suka shiga mkaranta tun daga primary har secondary da yake kusan Kansu daya ,Anas a fannin pilot ya karanta yyinda Aliyu ya karanci fannin soja ,sai ya hameed Wanda yake sha’awar likita ,sae Aunty shema wadda ta karanci law Shekara daya dagama makarantar ta a jami’ar Ahmadu bello dake Zaria ,sae Aunty zulfa dake shekrara karshe Anan b.u.k . kano sae ni Auta Asma’u wandda A tashi na nayi fitina,rigima da Neman tsokana ba kadan ba ,haka nasamu gata ta kowane fanni sae dae duk da wannan gatan nawa baisa iyayenmu suka kasa bani tarbiya ba ,Dan bana mantawa a gidan mu ko kana jami’a baka daina xuwa islamiya ko sauka Littafai Dari Dari kuwa xakayi sai idan kayi aure ne ko kasamu Aiki….
Ina da shekara goma A dunia Abba ya kara Aure da wata malamar makaranta Zainab ,xaman su da mama Abun Sha’awa tamkar mamace ta haifi Aunty amarya dama haka muke kiranta haihuwar farko ta samu y’ah macce akayiwa mama takwara hadiza ana kiranta Afra sae kuma kaninta mai sunan Abba ana kiransa sageer
.
Da ganan itama haihuwar shuru ,bangama secondary skull ba.Abban mu yyi ritaya ya koma kasuwan ci inda ya buda manya-manya shaguna a nan kasuwar kware ,bbu abunda baya xubawa a shagon tun daga kan kayan cosmetic ,wanda shago daban ne ya ware sae kuma na atamfa da Le’ss da sauran kayan mata bbu laipi arxikin Abba sae bunkasa yake yyi fice sosae haka ya wadata iyalinsa sosae duk da ritayar da yyi A ma’aikatar pilgrim baisa duk shekara ya kwashe iyalinsa suje omra ko aikin hajji hatta da sageer dake karamin mu dashi ake xuwa.
Harda su yah Anas da ya Haidar dake da aure harda ya’yah bibbiyu ,duk shekara sae sunje harda iyalansu …acikin yayuna kakaf nafi shiri da yah hameed shine kadae ke sona su kuma gabadan su cin zalina suke musamman yah Anas da yabi ya tsaneni kasan cewar ,nikaina nasan bana jin mgana haka inada daukar mgana sosae ina girma kamanni na sak na mahaifina hka gabadae nice baka a gidan mu…gaskiyya duka yayuna sun fini kyau ,idan na bata ma yah Aliyu rae a wata rana yana kirana da Kalmar da sai nayi kuka na yini ina zazzabi wato ya’r baka kuma mummuna natsani Kalmar A rayuwata Abba yyi fada har ya gaji da haka aka Samar min Admission anan jami’ar Bayero inda na dage akan lallai irin karatun Abba xanyi wandda duk gidan mu bbu wandda yyi kalan sa ,wato (Economic computer))… Kusan tare muka shiga skull da Rahama ,tun muna yara tare muka taso gida daya ne tsakanin gidan mu da nasu.. ”
Isalamiyar mu daya haka iyayen mu amminan junane ,Yayan Rahama daya ne yah Al’ameen wandda Dan sanda ne kusan sa’a suke da yah Aliyu Dan abokinsa ne ,sai Rahama sa’annan Aysha muna shiri sosae da yah Al’ameen har ya’n gidan mu ke ganin sona yakeyi ,acewar su duk da shima kyakkayawa ne ajin farko na kanyi daria nace aini police basa burgeni kudae jinin mu yaxo dayane.