WATA RANA Romantic hausa novels complete

“Dan a zahirin gaskiyya Bata son wannan Mln Nura din ya cika daukar kansa wata tsiya amma idan taga yarda yake shiri dasu Aunty zulfa sae abun yabata mmki har ta gano yadae tsaneta kurum ne kamar yarda itama ta tsanesa.”
Suna isa bakin office dinsa ga sunan sa nan radau a jikin kofar (Nura Muhammad kurfi”)..
Samun kanta tayi da hararar kofa sannan ta tsaya cak !
Da mmki Rahama da sally suka tsaya suma suna kallonta me kuma ya faru??” Lokaci daya suka jefa mata tambayr idan naje ya wulakanta ni baxan taba yafe maku ba.”
Mun yarda sae da sukayi knocking aka basu ixinin shigowa sa’annan suka hada baki wajen yin sallama “wani haddadden kamshine ya bugi hancin su wani hadadden guy ne suka hango tsaye hka ya basu baya yna amsa wya cikin sanyayyan turancin sa da kuma muryar sa ,mai taba zuciya da ruhi dukan su bbu wadda bata shiga tunanin wannan wane irin haddadden guy ne haka Mln Nura ne ya katse masu tunanin su yana hakin ce akan kujera mai juyawa yana cilla bairon dake hnnunsa ,Ya masu kwarjini sosae Rahama CE tayi karfin halin fadin sir dama gurin ka mukaxo ..bayan sun gaishesa.
” murmushi yyiwa Rahama meke tafe daku Rahama??”..
Ya fada dauke da fara’a ” A fuskarsa dama kuma yna shiri da Rahama sosae ,ganin yarda yake fara’a Asmy ta hareresa “A ranta take fadin mugu kawae..dama Asma’u muka rako ta kawo assignment nata ,sabida ranar da akayi submit bata nan nan take yanayin Nura ya canja kuke da bakinta kenan ita bata da baki?”…
Dan haka Ku fita kubari tayi mgana jiki sanyaye suka fita yyinda aka bar Asmy tsaye hka taji tamkar ta bisu a zuciya dae-dae lokacin AJ ya kammala wyar da yakeyi juyowar nan da xaiyi idonsa cikin nata ” ya raxana da ganinta amma ita ko a jikinta karshe ma dauke kanta tayi …
“Tsawa Nura yyi mata malama idan bakida abun fada ki fitar min a office kinyi min tsaye akai ,har cikin ran AJ.yaji tsawar Dan haka ya tsaya cak !
Yna kallon abokin nasa da mmki ….
” wani irin bakin ciki taji ya mamaye ta hka ta samu ta lallashi xuciyar ta ta fara basa hkuri wani mugun kallo yake jifanta dashi na lura bakida tarbiya yarinyar nan ,Dan haka get out my office right now!
“Kije a koya maki tarbiya sa’annan ki dawo gareni a fusace ta daga dara -daran idonta tana kallonsa ya hango tsantsar bacin rae acikin su yaji ddi a ransa da yaga ran nata ya baci …
Rasa tayi mai xata fada masa ba laifin sa bane laifin su Rahama ne ta juya a hnkali xata bar office din AJ.ne yyi saurin shan gabanta bani Assignment din naki?”
Yyi matagana cikin wata irin murya mai cike da bacin rae.”
Kallon banxa tashiga jefa masa idan kana sonka da mutunci ka jayemin a hanya na wuce nafi karfin ya wulakanta ni wlhi kuma baisa ya wulakanta ni ba.” Dan haka bana so !
Kaji nace bana so!!
“Tayi mganar tana bude masa manyan idonta meyasa xaka kulata AJ. Ai girman kanta baxai bari tabaka ba ka barta kawae tsaki tayi tabi ta gefen sa ta bar office din a fusace.”
A fusace AJ.ya nufo gurin Nura anan ya fara balbalesa da bala,i haba Nura wannan wane irin wulakanci ne ka tsiro dashi ?”
A gabana friends din yarinyar nan suka baka hkuri ka korasu waje kace sae da kanta ta baka shine xaka wulakanta ka haka?”
Cikin fushi AJ. Ke mganar a wannan lokacin Wanda Nura yasha mmki …murmushi Nura yyi hello relaz…wat did yhu say??”
Look Nura ba lokacin wasa bane ynxu “dis ix d first & last tym da xaka kara wulakanta ta hka bana son kana mata tsawa ko fada .” bana son ganinta cikin bacin rae ”
Did yhu get DAT? This is d only problem only!
Baki wangalau Nura ya saki yana kallonsa ,me AJ. Ke nufi akan Asma’u haka Nura yaji ransa ya baci ..
“Am going to find d solution to my self I will find d solution.”
A fusace AJ. Yabar office din nasa kallon mmki Nura yabisa dashi..
WATA RANA !
N@ Asmy b Aliyu.
©Haske Writer’s Association….
22
“Kai tsaye wajen friends din nata ta nufa da wani irin mugun yanayi hangosu tayi jikin motar Emran A tsaye daga nesa ya harde hannayensa a kirji yana kallonta .”
Idonta ne suka kawo kwallah lokaci daya ji tayi tamkar ta juya sae kuma ta tsaya cak! Rahama ne da sally suka ida karaso gurinta hnkali tashe.
Ya kukayi dashi??”
Cewar Rahama ganin kwallah a idonta yasa suka xuba mata ido Kallon su tayi ta dauke kai kai tsaye gurin Em dinta ta nufa batare da ta masa mgana ba ta bude side din baya ta shige sally ce ta masa mgana da ido akan yaje yabata hkuri.
Daita da Rahama suka kalli juna anan suka shiga tunanin meye Mln Nura ya fada mata ta fito a hka?”
Dukan su bbu mai amsar tambayr nan idan baita ce ta fada masu ba Hango AJ.sukayi ya fito daga office din shima ransa a matukar bace ,sae ynxu ne suke masa kallon tsaf kasancewar basu ga fuskarsa ba tun farko Duk cikin su biyu din bbu wacce bata tsorata da kyawun sa ba.
“Musamman sally wadda ta tsaya karewa shigensa kallo yana cikin wani farin boyel dinki Riga da wando na captani ya aza hula baka haka talkamin kafafunsa rufaffune suma bakake sae agogon dake sakale a hnnunsa dagani kansa mai tsada ne “…..
Har yafice dga gurin sally bata daina kallonsa ba. Nan take taji tana yimasa wani irin so wandda idan bata samesa ba xata iya rasa Rayuwa ta.” To amma ta yaya ??” Da gani guy din nan xaiyi jin kai ji yarda ya’mmata ke binsa da ido ,Wanda ko tafiyan sa kurum abun burgewa ne.”
Wae meya faru ne habibaty?” Yyi mata tambayr cikin nuna damuwa daita ,bata kallesa ba balanta na ta amsa sa hawaye yaga suna fitowa a cikin idanunta nan take Emran ya rude .”
“Duk dunia ba abunda yafi tsana irin yaga saukar hawayen Asmynsa shin meya taba xuciyar ta haka ?” Bata da zabi ta aza kanta kan kirjinsa ta fashe da wani irin kuka mai sauti haka ya dinga jin saukar hawayenta “A hnkali ya dinga Shafa bayanta alamr lallashi tunani take me xatayiwa Mln nura Wanda baxai taba mantawa daita ba A tarihin rayuwar ta??”
Dagota yyi a jikinsa farin handkerchief,yasa yana goge hawayen idonta xuba masa ido tayi ganin duk yabi ya damu tana jin wani irin sonsa na huda duka ilahirin jikinta .samun kanta tayi da kwakwalo murmushi ganin yarda yake kallonta ko kadan bata son ganinsa A damuwa .”
“Fadamin meya saki kuka? Kawae dai ina son nayi kuka ne shine kawae ,ba fushi ka hauyi dani ba kwana biyu ta fada tana Nuna masa ya tsunta biyu ✌????murmushi dauke A fuskarta.
Karya kike Asmy fadamin meye matsalar?” Wannan karon cikin fushi yake mganar ,tafi kowa sanin halinsa idan yyi fushi bbu kyau fuskarsa ta tallabo da hannayen ta duka biyu.
“Believe me !! Bbu Abunda ya faru ta fada tana kallon cikin idonsa ajiayar heart ya sauke fuskarsa ya hade da tata ta gano me yake nufi sae tayi saurin dauke kanta agogon hnnunta ta duba saura minti goma sha biyar su shiga lecture ,gobe xanje Abuja.”
“A Dan tsorace ta kallesa dama yasan abunda tafi tsana kenan taji xaiyi tafia xanje na karbo Visa ta ya fito tareda daddy xamu tafi jin mganar Visa yyi balain daga hnkalin ta batace komae ba tafice daga motar kallonsa tayi Anjima idan xan tafi islamiyya xan kiraka mu hadu a bayan layin mu.” Tayi mganar cikin rawar murya bata jira mai xai fada ba tayi gaba abunta ..”
“A lecture hall din ta nufa kai tsaye acan ta tarar dasu Rahama mai makon ta karasa gurinsu sae tasamu gefe ta xauna basu da xabi suka nufo gurin ta anan suka shiga tambayr meya faru tsakanin ta da Mln nura bata boye masu komae ba ta fayyace masu abunda ke faruwa.” Sun sha mmki sae dae ita a nata bangaren ta manta da hakan yanxu tafiar Em dinta ce matsalar ta ,sunyi kusan lecture har biyu amma bbu abunda ta fahimta burinta kawae ta isa gida ,yauma su Aunty zulfa basa da lecture ga mmkinta Maman su taga taxo daukarta tana cikin uniform dinta na aikin Asibiti …